P85

104 13 0
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...85*

                         .......Kwanaki na ta tafiya lokaci na shu'dewa, amma an dauki tsawon lkc ba'a saka ranar auren mu da Babagana ba, Baffah Liman cewa yayi ko ma shekaru nawa ne za'a 'dauka suna nan bazai ta6a bawa bawa Babagana aure batare da ya ri'ki kwakwarar sana'ar yi ba, sbd har alkcn Allah bai nufe shi da dacen sana'a ba, yayin da Baffa Liman ke ganin kamar da gayya yake yaki.mayar da hankali ya samu sana'a tunda ga sa'o'in sa nan duk suna da abinyi sai shi.

Ni kuwa zuwa lokacin sosai na 'kagu inga anyi auren duk dama ban furta hakan ga kowa ba hatta Dije bata sani ba, amma ina da dalilai na da ni ka'dai na barwa kaina sanin su...ba wai dan ina 'kaunar sa ba ba kuma wai dan sbd bu'katar kaina ba..amma sosai na 'kagara inga na bar gaban Iyami ko dan in samu 'yancin kaina da kaina.

Gashi yanzu Babagana ya fara zuwa zance, Iyami sai ta tayi min habaici wai sai dai muta bin bango ni da shi kullum amma bata ga ranar auren ba, ni fa bansan me hakan ke nufi ba a zahiri amma har ga Allah maganganun nata na matu'kar 'kona zucia ta.

Shi kansa Bbgana idan yazo ro'ka na yake akan in taimake sa in sanar da Baffah cewa ko babu sana'ar ma zamu iya zama tunda yana nema kullum kuma baya rasa na rufin asirin da yasan zai iya rike mu da shi.

Yace shi bai san meyasa Baffa ya zafafa da yawa ba, ba dan.shine ya haife shi.ba da ya sai yace Ni 'din.ce Baffah baya son bashi, amma mahaifi yake agare shi da ya tabbatar bazai cutar da shi ba.

Ni kaina nasan hakan, na kuma san gata Baffah ke son masa ba komai ba, a yadda yake a yanzu idan aka cigaba a haka har aka yi kasadan bashi aka kuma fara ciyar masa da ita to kuwa zuciyar sa mutuwa zata yi bazai ta6a yun'kurin neman na kansan da gaske ba, amma ya kasa ganewa.

Ni dai idan ya fa'di cewa in samu Baffan kallon sa kawai nake yi da mamakin sa, taya yake yake tunanin zan iya hakan, wace iriyar rashin kunya kenan zan ce na aikata?

Wani sa'in idanu nake 'kwalalowa sai in girgiza masa kaina.
Wani sa'in kuwa ce masa nake ni gaskiya bazan iya ba, sai yace wai in fadawa Yaa Bukar to...sanin da nayi cewa shi ka'dai zan iya samu da maganar ne ya sani amince masa a tunani na zan iya shi 'din sai dai koka'dan da ya dawo naji bama zan ta6a iyawa ba, shine ma ke min mitar hukuncin da Baffah ya yanke kan batun auren namu dan shi a fa'dar sa wai duk shirin sa ya kankama Baffa kadai ke son mayar da shi baya, sam a ganin sa bai kyauta ba, shi aure ai haske ne, yace ko muma lokacin da mukayi auren ai babu wani abin arziki, kusan kullum ma agida muke cin abinci musamnan idan damina ta  tsaya dan a lokacin ko'ina babu sau'ki, to da ikon Allah ba gashi tun ba aje ko'ina komai ya daidaita ba har muma zamu iya aurar da wasu..."
Yayi maganar yana kallona ni dai ban iya na kalle shi ba illa murmushi cikin raina nake ayyana da alamu dai Yah Bukar bu'di ya samu.

Bana yawan shiga gidan sa amma a bakin Ummaru nake yawan jin zancen.." Sun ci abu kaza da kaza nakan ji da'di har raina da jin cewa rayuwar 'dan uwa na ta fara sauyawa, ko muma agida ba laifi abincin mu ya 'dan sauya salo ba kamar baya ba gaskiya, hatta Yaaganan mu ma idan taji labarin yazo ta kanzo yayi mata ihsani ta koma gidan ta cikin jin da'di..Iyami kam ai ba'a cewa komai, ni kuwa duk lokacin da ya bani ku'di idan na ajiye bana sake ganin su koda kuwa na canza wurin ajiye ne, to ma ina ne lungu da zan wani iya ajiye ku'di a 'dakin, daga gadon kwangwalar da ke 'dakin da 'yar tabar ma akai shike nan sai jakar kayan sawa na...daga haka 'dakin babu komai to a ina zan ajiye da baza'a gani ba.

Sittira wannan idan sabuwa ce ya siyomin da kasafai ake bar min nema nake na rasa ta, shiyasa kullum nake nan.cikin tsummokarai, idan ya lura da haka ya tambaye ni inda kayana suke kuwa sai ince masa suna nan kawai.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now