P57

86 13 6
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh_md_

🅿️ *...57*

               ........Sau da dama Ammi kam mamakin ta ma take yi, domin ta jima da fahimtar cewa ba ita ce ta haifi Moopy ba, domin ba ita ta shayar da yarinyar ba madara taba ta, amma ta gaza samun cikakken prove da zai tabbatar mata da hakan domin Zaitoon ta toshe dukkan wata kafa da zaka samu direct game da ko'kontan ka, 6angaren kula da yarinyar new ko kuwa 6angaren dangantaka, ko cikin labarin da Zaitun ta bata ta nuna mata ne cewar dalilin yarinyar ne ta bar gidan su kawai dama garin baki 'daya, amma bata sanar da ita tushe da asalin wace ita ba.

Hakan yasa har yau ta kasa samun gaskiyar lamarin da zata riga game da Zaitoon.

Yarinyar na da hankali uwa uba nutsuwa, kamilalliya ce a zahirin gaske, sannan kuma tsawon zaman su bata ta6a ganin wata alama da zai tabbatar mata da cewa bata da kamun kai ba har yau 'din.

Sau da dama takan yi kwa'dayin kasancewar ta mata ga 'daya daga cikin 'ya'yan ta musamman ma Sultan da tasan cewa bazai ta6a yi mata gardama ba koda ta za6a masa Zaitun matsayin mata sai dai tasan hakan ba me yiyuwa bane domin Rayyan ma kansa ba ze ta6a amincewa da batun ba...baya ga hakan ahar yanzun bata san takamammai asalin Zaitun ba shiyasa ta kasa bawa kanta 'kwarin gwiwar aiwatar da shirin ba...'karshe ma kawai sai tayi watsi da batun gaba 'daya.

Wata biyu ya rage Moopy ta cike shekara biyu wanda yayi dai- dai da cikar shekarun rasuwar Nadia itama shekaru biyu, ya kasance watan Ramadan ne da bata jin zata ta6a iya mancewa da shi, sosai Ammi ke jimantawa da rashin ta sai dai bata da yadda zata iya ba kuma wani gata da ya rage mata a yanzu illa addu'a da basa gajiya da yi mata shi.

Yayin da Amrah kenan itama haihuwa yau ko gobe harma Ammi ta nemi Rayyan ya dawo da ita 6angaren ta Rayyan yace toh amma har yau bata ga suna da niyyar hakan ba, saboda cikin Amara nema kuma ya sa Ammi soke duk wata tafiya tata ta 'dauki hutu har sai bayan haihuwar Amra kafin nan ta cigaba, domin bata ji matu'kar tana numfashi zata daina wannan harka ta taimakawa da 'karfin ta dukiya dama zuciyar ta gaba 'daya.

Ta koyi darussa masu dama cikin wannan harkar ta kuma koyi sanin darajar 'dan Adam, tasan bambancin tsakanin akwai da babu, wasu idan labaran su ya iso su kafin su bincika har sukan iya 'karyatawa ma sbd tsanani dake cikin labarin amma lokuta da dama idan suka bincika sai su tarar da erh ashe gaskia ne, koma da kuskuren toh shine mafi 'karanci.

Hakika idan Allah yayi maka ni'ima kamata yyi ka gode masa, duk wani abin da Ubangiji ya baka ka raina idan ka shiga rayuwar wasu zaka tarar ne cewa 'kalilan daga cikin taka ni'imar daka raina idan aka basu sosai zasu karramashi har ma suji tamkar suma basu da wata damuwa.
Allah yayi mana ni'imomi masu dama, Allah ya halicce mu musulmai ya bamu Rai ya bamu lafiya, ya bamu arziki, ya bamu ji da gani, yayi mana kyautar imani ya kuma wadata mu da ni'imomin sa da mu kanmu ba zamu 'kayyade yawan su ba...ba tare kuma da ya nemi komai daga gare mu ba so baya ga mu bauta masa me zamu yi in ba godia agare shi ba.

A mafi yawan lokuta ta kan gode wa mahalicci da ni'imomin da ya yi mata har ma takan nutsar da 'ya'yan ta game da hakan, takan hane su raina halittar Allah ko ya take musamman 'dan Adam,  ta hane su kaskantar da duk wanda suke tunanin su suna sama da shi..hakika Allah ke bawa bayin sa komai a kuma duk lokacin da ya ga dama, su da ya basu ba son su da yake ne fin na kowa ba ba kuma iyawar su ce ta sanya hakan ba, ba kaunar su yafi yi fiye da sauran ba face dan kawai ya jarabce su.

Ammi ta hane su da almubazarranci da kuma 'dagawa, kyakkyawar mu'amala ta koya musu da zasu aiwatar a ko'ina suka tsinci kawunan su kuma tsakanin su da kowa.

Ko Zaitoon Ammi ta 'dauko tane sbd tausayi da kuma ganin kamar tana da maganin matsalolin yarinyar, baya ga hakama tayi duba izuwa ga 'karancin shekarun ta bai kamata ce kamar ta tana gallafiri saman titi ba, tana da muhallin da tasan zata iya ajiye mutane fin 'dari batare da kowa ya takura 'dan uwan sa ba, sannan tana da abinda tasan ba yayan ta ba hatta da jikokin ta mawuyacu ne suyi rayuwar 'kunci da talauci ba in dai ba wani ikon Allah ba,  toh miye yasa zata barta tana yawon bara akan titi bayan tana da damar tallafa mata.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now