P19

62 7 0
                                    

💕 *BINTEE*💕
        *( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
*Serlmerh-md*

🅿️ *...19*

                 Haka Zaitoon ta cigaba da rayuwa cikin wannan gidan cikin kuncin zuciya bakin ciki da damuwa, ko bakin kofa bata sake gigin takawa ba, gaba 'daya komai ma na duniyan ya fice mata aka, abinci ne dai ba'a fasa kawo musu ba kamar yadda aka saba ko wani yini sau uku, tun ma bata iya cin abincin har tazo ta fara sakin ranta tana dan ta6awa sbd karfin jikinta, shima zazza6in tuni yy nashi waje, tun ranar bata sake ganin Dr Rasheed ba, bata sake jiyo ko tashin muryar sa ba haka kuma bata san me ke faruwa a gidan ba tun bayan waccan ranar.

Kwanan ta biyar a haka duk ta sake ramewa tayi duhu sai idanuwan ta da suka kara fitowa, Mufee kanta sai da yanayin ta ya canza sbd rashin natsuwa da Zaitun din ke ciki dole ya shafe ta.

Da wani dare bayan ta idar da sallahr isha'i sun gama cin abinci taga an turo kofan, ta tsorata sosai sbd bb wanda ya ta6a shigo mata a irin wannan lkcn dan haka tai zuru zuru.
Wani daban ta gani ba wanda ya saba zuwa ba sbd bambancin tsawo da ta fahimci akwai tsakanin sa da wancan din.

Gaban ta ya iso ya tsaya daga muryar sa ta fahimci fuskar babu alamun rahama balle wasa tattare da shi" Ku tattara ku biyo ni".
Haka kawai yace da ita yaja baya kadan, bazata iya mai musu ba dan hk a hankali cikin sanyin jiki rauni da tunani ta sauko, yanzu a yanda ma take jin jikin ta ko magana ta kirki ba iya wa zata yi yadda za'a fahimce ta ba balle ta iya tanka shi, ta riga ta barwa Allah komai nata yanzu sai yadda kawai ya yi da ita a cewar ta...yanda kawai taji muryar mutumin da ko idanun sa bata iya gani sakamakon bakin gilashin daya rufe masa idanun banda tsoron su ma ba abinda ya karu mata, dama tsoron kowa na gidan ya riga ya mamaye ta tun kwanaki biyar baya.

Bayan sa tabi a hnkl rungume da Mufeeda da kayan su, dan ji take tamkar kafafun ta zasu karye saboda rashin karfin jiki.

Har gaban mota yaje ya tsaya ya bu'de mata baya, shiga tayi tana zazzare idanuwa tamkar mage amma bazata iya tambayar sa inda zasu ba, ita fatan ta kawai su bar ta, Allah yasa kar su rabata da Mufee koma me zasu yi mata suyi amma su barta ta rayu da yarinyar ta, in da Allah zai bata ikon rokon su da zatayi kawai tace su barta tayi tafiyar ta amma bazata iya ba, tun kashedin da Dr Rasheed yai mata sai take jin harshen ta yy mata nauyi.

Bata kara sanin komai ba tun shigar ta motar sai bude idanu tayi ta ganta a wani katafaren 'dakin da yaso firgitata, ga kuma Mufee na bacci gefen ta.
Kasa motsawa Zaitun tayi sbd tsoro, Allah gani gareka ta furta cikin zuciyar ta..wasu kwalla masu zafi na gangaro mata.
Bata tashi daga kwancen ba har zuwa lkcn da kunnuwan ta suka jiyo mata kiran  assalatu.

Bata yi kasa a gwiwa ba ta tashi ta nufi bayi.
Ta da'de kan Carpet 'din da tai sallahn tana hawaye tana rokon Allah ya sassauta mata ya kuma yafe mata laifukan ta manya da kananu, ta mika masa lamuran ta yy mata jagora ya raya mata yarinyar ta ya kuma kawo musu mafita.

Gefen Mufee ta koma ta kwanta tana sake rufa mata Hijab din jikin ta, tunani take yadda rayuwa ke ta gargara ta..zuwa yanzun duk ta saduda tsoron Allah da shakkan mutanen dunia ya gama cika ta.

Da safe misalin karfe bakwai taji an turo kofar gami da sallama, Dr Rasheed ne bayan sa kuma wata mace ce doguwa 'yar kyakkyawa sai dai fuskar ta tamau babu ko alamun fara'a.

Wani faduwan gaba Zaitoon taji me tsanani da ganin Rasheed, duk da yk bata yi mmkn ganin nasa ba amma sosai ta tsorata, rabon da ta gansa tun ranar da ya kafa mata warning sai yau kuma, sosai jikin ta ya fara rawa amma tashin farko bazaka fahimci hkn ba sai in ka dubi cikin idanhn ta, hk kuwa ta bude idanu ta zuba akan su zuciyar ta cike fal da tsoro da fargaban me kuma ya kawo su gareta...fahimtar hakn yasa shi sakin 6oyayyar murmushi idanun sa fess akanta.

"...Kuntun ubancan!..lalle ma  Rasheed, yana nufin wannan ce matar? 'yar yarinyar nan, rainin hankali"
" Erh lallai! salon ta zauna da ita bayan ta waye tazo ta aure mata miji...bazata sa6u ba sam wlh.."
Zancen zucin Hameedah kenan wanda tayi sa ne tana daga inda take tsaye bayan Rasheed itama tana duban Zaitun da wani mugun kallo.
Da rawar murya ta gaida su, babu wanda ya amsa gaisuwar daga cikin su sai ma " Ya jikin naki..?"
Da taji Dr Rasheed ya fa'di.
Rarraba idanu ta fara da tunanin wani jikin kuma? bata san dalilin tambayar ba dan hk kawai ta amsa masa" Alham..dulillah..da sauki..".
Gaba 'daya ya gama rikitar da ita, " dama bani da lpy ne..?"
Ta tambayi kanta tana me yin tsam da tunanin ta gami da hasaso inda ke mata ciwo cikin jikin ta..bata ji komai ba.

Waigawa yayi ga Hameeda yana 'yar murmushi yace" Hameeda meet Zaitoon...my Patient.."
" Na ganta.."
Ta amsa a sanyaye tana kya6e baki da kawar da kanta.

" Zaitoon wannan matata ce sunan ta Hameeda..nan kuma gida na ne..zaki zauna tare da mu zuwa lkcn da zaki dan kara samin sauki sai aga yadda hali zai yi ko..?"
Ya fa'da cike da kulawa, sai dai hkn duk ba shi Zaitoon ke son ji ko samu daga gareshi ba, ba wannan kalmar take son ji ba, sam ta kasa fahimtar inda maganganun nasa ma suka dosa, yana nufin zama zata cigaba da yi dasu, tayi musu me? amma bata da bakin tankawa koma me yace mata dole ta amsa shi dan bata ta6a mance haduwar ta ta karshe da shi.
Shi kansa ma yasan hkn shiyasa bai wani damu da sake jaddada mata wani kashedin ko tilasta ta amsa maganar sa ba.
" Amma wai sai anan gidan dole zata yi jinyan ne Abban Naina? why not can asbiti inda kowa ke zuwa kuma yafi dacewa.....".
" Anan nayi ra'ayi Hameeda pls, bana san dogon magana".
Dole taja baki tayi shiru badan hnkln ta ya kwanta akan zaman ta da Zaitoon din ba sai dan gudun 6acin ransa.

Tare suka sake ficewa a dakin suka bar Zaitun cikin zullumi da toshewar tunani.
Duk ta rasa meke shirin faruwa da ita ne.
In tunanin ta ya bata daidai kenan an canza musu muhalli zuwa gidan sa inda iyalan sa suke kuma an kawo ta ne da sunan marar lafiya..kenan bashi da niyyar barin ta tafi ne ko me hkn ke nufi..Yah Subhanallahi, wannan wani irin tarko ne? kenan ta bar bakin kare ne ta fa'da bakin kura.

A hanya Hameeda ke sake tambayar sa amma ba da'dewa zatayi anan din ba ko?
Yace" Ni kaina ban sani ba, ma mmk su dade 'din.
Turus tayi cike da takaici batayi kasa a gwaiwa ba ta sake jefa masa wata tambayar.. zata na fitowa tayata aiki yace sam ita ba me aiki bace majinyaciya ce.
Wannan karon sosai ya hassala ta duk wani zafin da ke zuciyar sai da ya bayyana kan fuskar ta ta kasa danne shi.
" Amma Abban Naina sai nk ganin kamar ka zake da yawa akan yarinyar nan...taya za'ai ka kawo min gantsamemiyar yarinya irin wannan hk kawai kuma kace in Zauna da ita ba muharramar ka ba ba tawa ba ba komai ba..."
" Thought gidan nawa ne..?"
Ya tare ta da tsawa yana waigowa gareta muryar sa da alamun fushi, ji yy ya gaji da maganar gaba 'daya, tun daren jiya yk kokarin fahimtar da ita amma ta kasa fahimtar sa.
Hameeda saroro tayi tana duban sa cike da mamakin sa.
" Anya Abban Naina cikin hnkalin ka kk kuwa...?"
Ta tambaya cikin wani sanyi da raunin tsoron yadda ya buga mata tsawa sbd waccan yarinyar.
" What ever..abinda na sani kawai shine ke da duk wani abinda ke cikin gidan nan mai rai ko sa6anin hkn mallaki na ne, kuma karkashin iko na, dan hk ba lalle sai nayi tarayya da wani wajen zartas da hukunci cikin gidan nan ba...Zaitun zata zauna tare da mu daga yanzu har zuwa lkcn da nayi ra'ayi nd that's final...."!

Salmerh😘

BINTEEE ( 'Yata ce)Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora