P1

499 15 0
                                    

💕 *BINTEE* 💕
      ( 'Yata ce)

*By*
*Salmerh MD*

🅿️....1

.........Duban farko idan kai mata zaka fahimci cewa matashiya ce mai karancin shekaru kasa da ashirin, sanye take da zanin atampan wanda daurin ya tsaya mata saman siraran kafafuwan ta sai hijab din ta na roba mai zanen blue da fari wanda shima dududu bai wuce tsayin hannun ta ba.

Tafiya take cike da sassarfa rungume da 'kullin kaya cikin wani ko'da'd'den zanin da ba se ka sha wahala wajen fahimtar cewa zanin ya jima yana shan ruwa ruwa ba musamman saboda kodewar da yayi.

Duk da cewa tana cikin yanayin tafiya ne na sauri amma hakan bazai hana ka fahimtar nutsuwar da Allah yayi mata ba. Akai akai zaka ga ta kai bayan hannun ta daya tana share 'kwallar da ke zuba daga idanun ta babu 'kakkautawa.

Tayi tafiya me dan nisa sosai domin daga inda take tsayen sam ko kusa ko alama bazaka iya hango alamun gari ko makamancin hakan ba.

Abu daya dake sata waigawa shine idan taji dirin tahowar mota daga bayan ta takan waiga wani sa'in har tsayuwa take yi ta tsurawa motar idanu har sai ta wuce inda take ga dukkan alamu kage take wajen ganin ta samu abin hawan amma hakan be yiyu ba.

Zuwa wannan lokacin tuni hawayen nata sun tsagaita  sai dai har yanzun fuskar ta daure take babu wani alamun fara'a tattare da ita.

Bayan kamar shudewan rabin sa'a tana tafiyar batare da ta samu abin hawan ba, wata doguwar farar Bus ce ta taho wanda mutanen cikin ta basu haura mutane biyar ba. Ban yi mamakin tsayuwar da tayi ba bayan jin tahowar motar saboda na jima da fahimtar motar da zai tsaya ta hau tun dazun take dako.

Cak kuwa ta tsaya tabi motar da idanu, bansan dalilin da yasa har yanzun takasa budan baki tayi magana ko nuna alamu da hannun ta wajen tsaida abin hawan ba duk da cewa alamu sun bayyana asalin matsuwar ta da son ganin ta samu abin hawan amma hakan bai sa ta iya furtawa ko nuna alamun hakan ga matukan motocin dake faman zuwa suna wuce ta ba...sai dai bana raba dayan biyu cewa ta kasance bakuwa ce a wannan harkar shiyasa.

Kadan Bus din ta gitta ta cikin sa'a kuwa sai tsaya daga gabanta kadan take drivern Bus din ya sauko.
Cikin ranta ta saki hamdala gami da ajiyan zuciya afili.

"Uwargida ina zaki..?"
Drivern ya fada yana me bude mata bayan motar.

"..Inda kuka nufa.."
Tace dashi tana me kokarin taka motar ta haye.
Bai sake magana ba kawai ya ja marfin ya rufe ya koma mazaunin sa tare da jan mota suka yi gaba.

Karo na farko kenan a rayuwar ta da ta ta6a sanya kafa ta bar mahaifar ta, a iya sanin ta tunda mahaifiyar ta ta haife ta bata ta6a zuwa ko'ina ba...ta girma ta budi ido tayi wayo duk cikin garin su...sai gashi ayau kaddara ta rabata da mahaifar ta da kowa da ya kasance ahalin ta ne.

Duk da cewa kwanakin nan din wajajen nasu bai fiya lafiya ba amma sam bata ji hakan ya dame ta ba musamman da ta ga cikin motar akwai wasu mata guda uku da maza biyu...ta riga ta tsaida zuciyar ta akan kudurin ta na barin garin dan haka aranta take ji koma ina ne suka nufa a shirye take itama.

Rintse idanu tayi gami da dafe kanta. Yayin da dayan hannun nata kuma ta kai bayan ta ta dafe abinda ke goye abayan ta dashi bata sake daga kanta ba har sai da kunnuwan ta suka fara jiyo mata tashin hayaniyar mutane...amma baza ta ce ga tsawon lokacin da suka dauka suna wannan tafiyar ba.

Sai a lokacin ne ta dago kanta ga mamakin ta sai tayi arba da mutane, titina da kuma gine gine ba irin wanda ta saba gani a garin su ba..." _Duniya sabuwa_ ".

Ta furta cikin ranta tana mai gyara rikon da ta yiwa kunshin kayanta tare da daidaita zamanta da kyau dan kar ta takurawa abinda take goye da shi...duk dama tun farkon shigar ta zuwa zaman da tayi a motar ankare take ko da wasa hankalin ta bai bar kan abinda ke goye a bayan tan ba.

BINTEEE ( 'Yata ce)Where stories live. Discover now