The end and thanks.

4.1K 213 48
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨















💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*_NA_*
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *_QUEEN BK_* 👸🏼













🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah🤜🏻🤛🏻))















_Itz_queenbk @ insta gram_







The End





Am so so sorry dearies i can't explain why this last page is coming late it was out of my control i could'nt help it wallah i was so so occupied, am realy sowwie😣😥.



Jin wannan maganganu sun razana Asmah sosai to waye wannan tambayar da zuciyarta keta maimaitawa kenan, a hankali cikin ƙarfin hali ta shiga buɗe idanunta ta sauke su akan mamallakiyar muryar riƙe da binɗiga yana sosa ƙeya tare da watsa ma mutumin dake kusa dashi banzan kallo, cikin mamaki ta wage ido tana faɗin .......

"Ya ...Aliyu?" akan laɓɓanta maganar ta tsaya dan sam basu ji ta ba, lumshe idonta tayi ta ƙara buɗe su kan Aliyu sai da ta tabbata shine ta wage baki iya sauran ƙarfin da ya rage mata a jiki tana ƙwala sunan shi "Aleeeeeeyu!" muryarta a shaƙe da ƙyar suka jiyota, juyowa sukai gareta yana sakin wani murmushin "yaushe gamo" ya tako gareta bindigar hannun shi yasa yana janye mata gashin da ya rufe mata fuska yana faɗin "Hy baby it's been long how were you fairing".

Wata uwar harara ta banka mashi dan tuni tagama tuna komai a ƙwaƙwalwara da furucin da ya furta mata na ƙarshe kamin rabuwarsu da kuma labarin da Zarah ta bata akanshi wato shine ya kamo ta yazo yana azabtar da ita a cikin wannan kangon gidan ya rabata da masoyinta da ƴaƴanta da mahaifiyarta amman bazata taɓa yafe mai ba ace azo a ɗaure mutum ko salla ya gaisa da ubangijin shi baya da hurumin yi, ganin tana binshi da wani kallon tsana ya saki wata dariyar mugunta cikin son ƙara ƙular da ita yace "yana ga kamar baki yi missing ɗina ba baby" ya faɗa yana daɗɗaga wuya idon shi sam ba alamun tausayi a cikinsa.

Wani ƙarfi Asmah taji ya dirar mata ta taro miyau a bakinta ba tare da ya ankara ba ta watsa mai a fuska tana faɗin "wallahi na tsaneka a rayuwata kuma bazan taɓa yafe maka abunda ka aikata mun ba har duniya ta naɗe kum.........." kasa idawa tayi saboda wata walƙiya da ta gani a idonta tare da jin kunnenta yana mata wani gumm kamar an ɗura mata ruwa a cikin sanadin marin da Aleeyu ya gabza mata a fuska yana faɗin "shiiiiit" yana fito da handkachief a aljihunshi tare da goge miyan da ta watsa mai yana ta sakin tsaki.

Ita ko Asmah tuni idanunta sun rufe ruf bata ƙara sanin me ake ciki ba, Royce ne cike da tausayi da tashin hankali kar dai ya kashe ƴar mutane dan kisa a wajen oganshi ba wani abu bane me wahala a ruɗe yace "oga kar dai ka kasheta?".

Yana lashe baki ya juya gareshi yace "not yet am not gonna kill her now sai in har buƙata ta bata biya ba and at that point i have no option rather than to kill her kuma ma meye damuwarka inna kasheta?"

"Wannan karan i will not fail i will surely protect this pure soul from your devil heart" ...  ya faɗa a ranshi a fili sai ya sadda kanshi ƙasa alamun yayi given up.


ZAN SOKA A HAKAWo Geschichten leben. Entdecke jetzt