page 19

3.8K 245 2
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨







💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*NA*
BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼





🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 🖊
((Gidan   zaman   lafiya da   amana   insha   Allah🤜🤛    ))




Wannan page naki ne *MARYAM MUHAMMAD HASSAN (( MEEMAH ))* a gaskiya muna jin d'ad'in yadda ki ke wayar da kan masu zagin marubuta a novel d'innan naki me taken *MARUBUCIYA CE* gaba dai gaba dai my meemah ki cigaba da fayace masu k'udurin mu, duk wacce kema marubuta mummunar fahimta dan Allah ta nemi novel d'innan ta karanta harda ma masoyan mu duk ku karanta dan kusan duk abunda muke dan ku muke badan komai ba sai dan mu nishad'antar, ilimantar, koyar, tunatar da fad'ankantar daku akan abunda Allah ya bamu sani, Allah kasa mu dace ameen, masoyana a duk inda kuke a fad'in duniyar nan ina mik'o sak'on gaisuwata gare ku, kuma inajin dad'in yadda kuke nuna kulawa da yabawa gareni, ubangiji Allah ya had'a fuskokin mu a gidan aljanna, one love fans❤😍💋.





Page1⃣9⃣





Tun kafin asuba ta tashi ta fara shirye2 don an cemata da wuri zata rink'a ma yaya Abdallah aiki kuma batason ta sab'a lokaci, bayan tagama wanka ta shirya cikin wata doguwar riga na farin cotton material me touchings d'in coffe collor tayi kyau sosai, sai lokacin miemie ta tashi don shirin makaranta don ita indai tai sallar asuba sai ta koma bacci ta kejin dad'i, ma'u ta fita  dan ta gaida ammie a kitchen ta taras da ita har ta gama had'a ma Abbah abincin break fast tana jerawa a tray, donshi Abbah baya cin abincin y'an aiki duk wacce keda girki cikin su ita zata mai girkinsa, har k'asa ta duk'a ta gaishe ta, cikin faran2 suka gaisa sannan tayi mata sallama ta nufin part d'in ya Abdallah.

yau ma kamar jiya ba kowa a falon ta isa ta gyara falon da diny area da kitchen d'in tas, tayi sallama bakin k'ofar d'akin ba amsa, kai tsaye tayi ciki don azatonta ba kowa, toilet d'in tayi don gyarawa bayan ta fito turus tayi don gannin mutum saman gado, tana shirin fita taga ya tashi zaune sai da yayi mik'a sannan ya mik'e manyan idanunshi tar a kanta kasancewar suna fuskanta juna ne, k'ura mata idanunshi yayi k'yar ko k'yaftawa ba yayi, itama ma'u ta d'an shagala da kallon kyawun surarshi shine dai wanda tagani a hoto sai dai a fili yafi kyau, gabanta taji yana ta faduwa sosai sai da ta dai2ta natsuwarta sannan tace "ina kwana ya Abdallah" me kon amsa sai ya k'ara binta da idanu, yanxu kallon ya fara isarta dan duk inda ta motsa sai ya bita da idanu abun har ya fara bata tsoro, cikin k'aguwa da kallon da yake matan tace

"ya Abdallah zan gyara d'aki in ba damuwa kaje  falo yanxu zan gama in anso ma kalacinka"

nan ma shiru na mujiya kawai ya bita da su, yanxu kam abun ya tsorata ta sosai dan haka tace

"yasin kuruwata kurrr nama na d'aci mai d'a yaci d'anshi marar d'a yaci k'ok'on zuciyar shi, kacika nacin kallo wlh"

wata kasallalliyar dariya Abdullah ya saki sannan ya yaye bargon da ke jikin shi ya tura shi k'asa, fulo da bedsheet d'in da ke kan gadon ma duk k'asa ya wurgo su itako ma'u sai kallon mamaki take binshi dashi bata k'ara tsinkewa ba sai sadda taga ya shiga toilet ya d'auko brush da buta ya dawo ya zauna kan kujeran madubi ya fara abunshi cike da mamaki tace

"ah ah ya Abdalah ya da haka anan xaka wanke bakin?"

ko kulata beba ya cigaba da sabgar gaban shi, a ranta take cewa " wannan wane irin hali ne?, ai ko hauka sai haka!" data gaji da kallon wañann ikon Allah sai ta k'arasa bakin gadon ta shiga gyarawa, bayan tagama ta shiga toilet d'in dan Ida gyarawa tana cikin wankewa sai dai ganin mutum tai kanta tsaye a razane ta d'ago, a karo na farko da ya fara mata magana, gatsine yayi tare da nuna mata k'ofa da hannu yana fad'in "ki fitaaaaaa" da k'arfi, ma'u kam tsabar firgici fad'uwa k'asa tai dirsham, itakam bata gane mashi ba, juyawa yayi ya cire farar jallabiyar dake jikin shi ya rage daga shi sai boxsers d'in dake jikin shi da alama wanka zaiyi ma'u na ganin haka ta fito a guje bata tsaya ko ina ba sai a bakin k'ofar falon tana maida lumfashi, a fili tace " wannan wane irin abu ne ko dai ba hankali ne?" take wata zuciyar tace mata " to inba hankalin ai da ammie ta fad'a maki ko? an dai cemun baida lafiya to me hakan ke nufi mahaukace ne ko ko? duk ita kad'ai ke tambayoyinta ta rasa me amsa mata, ta d'auki aniyar in miemie ta dawo zata tambaye ta, meye ciwon ya Abdallah.

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now