page 79

3.6K 266 52
                                    


🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨













💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*_NA_*
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *_QUEEN BK_* 👸🏼














🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan   zaman  lafiya  da amana    insha    Allah🤜🏻🤛🏻))











_Itz_queenbk @ insta gram_











Page 79













Wani uban tsaki Ladi ta saki tana faɗin "wallahi Shafah naki mai sauƙi ne muje kiga abunda ya faru da ni" ta faɗa tana jan hannun Auntyn Yara zuwa ɗakinta da hannu take nuna mata fasassar tukunyar sihirinta tana ƙara fashewa da wani kuka mai tsuma zuciya tana faɗin "shikenan ni nasan tawa ta ƙare tunda har tukunyar nan ta fashe kin dai san abunda boka yace ko?".





Auntyn yara kuwa tana ganin fasassar tukunyar ta fasa ihu tana zamewa ƙasa tana faɗin "Ladi mun shiga uku garin ya akai tunkunyar nan ta fashe ne? taya hakan ya faru bayan kinsan da ita kaɗai kika dogara?".





"Ni ta ya zan san ya akai ta fashe kawai yau na dawo daga gidan Alhaji Labaran wannan mai takarar governer kin san kwana biyu ina gidanshi shi yasa ma ban ɗauki wayarki ba dan baya san ina ɗaukar wayar kowa in ina tare da shi, to dawowata kenan na tarar da ita a fashe ban san ya akai hakan ya faru ba".


"Ai wallahi ta zama bata ganmu ba tashi tashi mu tafi yau ko boka bai so ba dole muje wajensa".


"Ai dole ma muje wajenshi Shafaa dan ya gaggauta yin wani abu akan wannan lamuran" key ɗin motarta ta warta ko ta kan gyale ma bata bi ba ta sheƙa da gudu waje, ita ma Auntyn yara a gaggauce tabi sawunta dan ita tama manta da wani Abbah da kuma maganar da suka aje.






Inda Ladi tai packing motarta suka nufa suna shiga Ladi ta jasu a guje suka hau hanya ba wanda ke magana a motar sai tunane tunane da zuciyarsu ta gaza daina saƙa masu, Ladi kam figar motar kawai take dan ta ƙagara su isa Allah dai ne ya kaisu lafiya wajen ƙarfe uku na rana suka isa nan sukai packing gefen titi suka shiga dajin dutsen safe sai dai tun kamin su isa karagar boka suke jin wani gurnani da ƙarfin gaske da gudu suka ƙarasa wajen, wata irin mahaukaciyar wuta ce ke tashi a wajen a yayinda suke iya juyo ihun boka da gurnaninsa da alama yana ciki wutar ta tashi, ihu suka rinƙa saki cikin rashin sanin abunyi ga hayaƙi yana neman ya turnuƙe su, sai da wutar nan ta gama cinye boka tas sannan ta fara bin dajin su kuma ganin haka suka sa ƙafa suka fara gudu da ƙyar suka isa inda suka aje motarsu suka ɗau hanya Auntyn yara na cewa,

"Amman wallahi munyi babban rashi yanzu ina zamu iya samun boka mai aiki kallar Darɓusa?".


"Kar ki damu nasan wani boka nan ƙauyen gaba sai mu gangara" Ladi ta faɗa tana ƙara figar motar.

Can suna tafiya Ladi ta burma ihu tana faɗin "kam wallahi shafa dishi dishi nake gani ga wata ƙara da nake ji a kunnuwa na ƙafafuwana kuma da hannaye na sunyi sanyi kamar ba lakkha a cikinsu".

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now