Page 2

5.6K 350 2
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨


💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*NA*
BILKSU ALIYU KANKIA
*((QUEEN BK)).*

🚩ZAMAN AMANA WRITTER'S ASSOCIATION (( Gidan  zaman  lafiya   da  amana  insha  Allah  ))

page 02⃣

Nan gwgo ta tafi ta barta yashe a k'asa, taje tayi sallah don yau y'an sallahn nata sun motso,
taci
tuwan dawan ta ta k'oshi, ta dawo amman har lokacin ma'u bata tashi ba,
ta matso kusa da ita tana haskata da tocilar hannunta
don duhu yayi tab'e baki tai tace

"yau ma iskancin da kika saba yi mun xakiyi ko? to maxa kisa hinma"

Ta dauki kwaryar furarta ta kai uwar d'aka, sannan ta dawo ta dauki butar data fasa tace

" koman darin d'ad'ewa sai kin biya ta, shegiya sae kace me jikin k'arfe"

ta wuce ta kaita kitchen tana fadin ayi makamashin wuta da ita,
ta  canxa ma k'ullin kokon ta ruwa tagama y'an kintse2 ta har zata shige
ciki ta kwanta, sae kuma ta dawo ta d'eb'o ruwa ta sheka
ma ma'u, firgigit ta tashi tana lumfarfashi tana jujjuya idanu, gwgo taja wani
tsaki mae madda tare da fadin

"motsatsiya kawai dallah tashi ki b'acen da ga gani"

ba musu ma'u ta lallab'a tana turo baki ta tafi dan tasha wahala d'axu bata son a kuma,
Tayi alwala da rarrafe ta k'arasa dakinta, a daddafe
tayi magruba sannan ta d'ora da isha'i sannan ta kuma
rarrafawa kan y'ar lotsatsiyar katifar ta, jin kanta
tayi kamar an d'ora mata bulo jiri kawai take ji, dan daki gaba d'aya juya mata yake, ga kuma bayanta da k'irjinta sun rik'e
mata sosai suke mata ciwo,
abu goma da ashirin sun tarar mata,
ta d'ad'e a kwance amman
b'arawo bacci yak'i saceta,
k'ulululu kawai ka keji, cikin
tane keta kiran ciroma,
da
axaba tae axaba sae dae ta kwanta ruf da ciki nan ma ta d'ad'e amman ta kasa bacci,
can ta fara azhkar a xuciyar ta ckin ikon Allah
bacci yayi awon gaba da ita

Sae dae me can wajen k'arfe biyun dare ta farka,
sosai cikinta ke juya mata, sae juyi take ta tashi tae magudada da gudu sakamakon yunk'urin aman da ta fara,
tana isa kuwa sae amai shhaaaaaa kamar an bud'e
fanfo amman zallah ruwa
ne yellow tunda ba abun da ta ci, ta korar da aman da ruwa sannan ta kuskure bakinta
ji tae kamar ana rarake mata cikin,
dan haka ta b'amb'ami ruwa sosai
gamawar ta keda wuya ta maido shi tasss,
Jikinta har b'ari yake, jiki ba kwari ta nufi kicin dinsu wanda wani d'an k'aramin d'aki ne suka mayar
madafa, tuwon da gwggo ta
rage wanda ta rufe da fai fai
tacinye amman bata koshi
ba saboda dan k'adanne, ta
bude tukunyar nan ma dan kadan
ne shima tacinye ahi tass,
Sannan ta d'an zubzubda miya a k'asa
ta yada tunkunyar da kwanon ta bar k'ofar a bud'e,
taje tasha ruwan randa mae
sanyi tayi mik'a, a haka tabi lafiyar katifar ta nan ko
ba dad'ewa bacci mai d'ad'i ya sure ta hadda minshari, niko nace lafiya uwar jiki babu me fushi dake.

Washegari ma'u  bacci yayi d'ad'i bata tashi ba kamar yadda ta saba tashi ba wato kafin asuba,
Yau har gwggo tariga ta tashi
abunka da in jiki ya saba, don gaskiya baffa baya wasa ta fannin addini ko kadan uwa uba sallah,
dan in bada dan shi  ba ma'u baxatana zuwa islamiyya ba
in dan gwggo ce, don Allah yasa ya tsaya mata sosai
da baxa ta samu har ta haddace ba.
dan haka yana tilasta ma gwggo ko ba ta so sae tayi sallannan, duk da wani sa'in
tana b'otsarewa sae ya had'a da addu'a,
to da haka har ta d'an saba,
in yana nan toxa tayi amman wata sa'in in be nan,
sae tace wae bari ta hole

((WAIYA ZUBHILLAH KO INA HOLEWA A RASHIN YIN SALLAH, ALLAH KA GANAR DAMU AMEEN))

Itama ma'u haka ta taso cikin kulawar tarbiyyar baffahn ta, don haka bata wasa da addinin ta ko kad'an, don ko kiwo taje lokacin sallah be wuceta ba tare da tayi ta ba.

Gwggo tafito har tae alwalla amman bataji motsin ma'u ba akasin kullum, tayi murmushin mugunta
ta nufi randa ta debo ruwa mae sanyi, yau xatayi muguntar da ta saba mata
duk randa ta riga ta tashi da wuri ba,
saboda haka ne ma ma'u to koya tashi tun kafin asuba.

Tana isa ta shek'a mata ruwa kamar wata shuka,
Firgigit ta farka daga Mafarkin da take wanda dama ta saba irin shi,
Na wani mahaukacin mutum da yake binta kullum
a mafarkin, yae ta kiran sunan ta yana cemata wae ita matarshi ce, ita kuma tana kuka tana ce masa k'aryane ita matar jauro ce bashi ba,
shima yai ta kuka,
a haka dai mafarkin nata yake tsaya wa kullum,
To yau tana cikin mafarkin ne taji saukar ruwan sanyi a jikinta wanda har ta manta yaushe
rabon da a tadata dashi taja wani dogon lumfashi
tareda salati, ta tashi tana
kakkama rigarta saboda sanyin ruwan, sae da ta canxa riga sannan ta fita
tayo alwalla ta dawo tae sallah.


*QUEEN BK*

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now