page 55

4.7K 291 61
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨






💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼









🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana insha Allah🤜🤛 )





















Page5⃣5⃣





A kwana a tashi ba wuya wajen Allah yanzu wata ɗaya kenan da auren Abdallah da Asmah, kullum ƙara shaƙuwa suke da son juna, Ammie da Abbah kam ba ƙaramin ji suke da ɗan da sirikar tasu ba, su Auntyn yara kuwa an warke garas, yanzu yadda take jinta da dawo da lafiyarta zata cigaba da muguntarta dan da ciwo ya sata saduda.





🦚 🦚 🦚
Asmah ce ta tashi daga bacci tana salati gaɓa ɗaya jikinta ya jiƙe sharkaf da zufa sai data maida lumfashi sosai sannan ta dawo hayyacinta zare jikinta tayi daga Abdallah ta miƙe tana ta tunanin me yasa wannan ƴen kwanakin take yawan mafarkin Ummanta, toilet ta faɗa ta ɗauro alwalla tazo ta shiga sallah tana kai kukanta a wajen ubangiji, ta daɗe tana addu'a ta roƙi Allah akan ya taimaka mata a kasuwancin da ta fara sannan ta roƙar ma Abdallah sauƙi ta roƙi Allah akan yasa ta gana da Ummanta in tana raye, sannan ta roƙi Allah akan ya katange ta da sharrin Auntyn yara da duk wani mai son cutar dasu, kiran sallah taji an fara can Abdallah ya fara motsawa dan yanzu zama da Asmah ya saba kwata kwata bai bari sallah ta wuce shi kuma har ta asuba ya saba tashi wata rana ma shi ke tada Asmar barin ma ranar da ya tara mata gajiya da yawa, yanzu ana samun sauƙin shi sosai dan har ƙur'ani yana zama Asmah ta koya mai, dan dama tuni Asmah ta daina bashi maganin da Auntyn yara ke bata, ko da har yanzu bata daina kawo mata ba tare da mata kashedi akan ta tabbatar tana bashi ita ko Asmah bata nuna mata komai a gabanta zata nuna tana ba Abdallah sosai kuma tai ta mata godiya akan taimakon shi da take, amman Auntyn yara na fita Asmah zata tiltilar da su a sink tana faɗin "haba Auntyn yara Ma'un da kika sani ba ita bace Asmar yanzu ba, Asmah wayayya ce me ja da ita kuma sai ya shirya dan ita da Allah kawai ta dogara" ta faɗa tana dariya tana ƙara gode ma Allah akan asirin Auntyn yara da ta sani.




A hankali ya fara tattaɓa gadon kusa dashi bai jiyo Asmah ba da sauri ya tashi yana buɗe ido yana mursuƙa su can ya hango Asmah dake zaune saman abun sallah wadda idonta ke kanshi tun fara motsawar shi take kallonshi, murmushi yayi yace "beauty ashe wayau kika mun ko?".

Itama murmushin ta saki tace "wane wayau na maka?".

"Gayanan kin tashi kina ta sallah ni baki tada ni ba saboda baki so na samu lada ko".

"Haba babyna ya zaka ce haka wallahi na fi kowa son ka samu lada, kayi haƙuri babyna kaji zanna ta daka yanzu insha Allah".

"Beauty kin dai mun addu'a ko?".

"Sosai baby addu'ar ka tafi dukkan addu'oin da nayi yawa".

"Kenan kin fi sona ko".

"Sosai baby nafi sanka, ina sonka fiye da kaina".

"Uhmm ai ni ban ma son kaina nafi sonki fiye da komai hadda wayata fa".

Dariya tai ganin yace yafi sonta akan wayar shi tasan yadda yake ba wayar shi mahimmanci sosai ko bai faɗa bama tasan yadda yake sonta kawai dai bai iya expressing kanshi ne, karkaɗa kai tayi tace "wayyo babyna ina sonka sosai har abada".


ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now