page 1⃣4⃣

3.8K 249 0
                                    

[14/11 3:38 pm] 👸🏼Queen bk👸🏼: 🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨





💎💎💎💎💎💎💎💎 *ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*NA*
*_BILKISU ALIYU KANKIA_
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼







🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S*
(( ~Gidan zaman lafiya da amana insha Allah~ 🤜🤛))





Wanan page din naki ne *Halissa Adamou (( lissah))* tanx for d 1 love ina yinki irin sosai d'innan❤



Page1⃣4⃣






Duk da kasancewar diraban
motar ya hango ma'u sadda
ta hayo kan titin da gadu, kuma
yana ta mata horn, kuma yayi
k'ok'arin cin birki, ganin yai ta tsaya
cak ba ma ta motsi, amman
birkin bai ci ba sakamakon gudun da motar keyi,
a fannin ma'u kuwa batasan
ta hau titi ba sai da fitilar motar
ta hasko ta, ta kuma ji k'arar
horn d'in motar wanda ya k'ara
haddasa mata firgice dan
haka ta tsaya cak ta ma rasa
me zatai, kawai hannun ta
tasa ta rufe fuskar ta.

A haka tana tsaye har motar ta k'araso ta banke ta
kamar a mafarki take ganin abun,
sai dai Allah yasa motar bata
bi takanta sakamakon birkin da
taci, tunda motar tai sama
da ma'u ta zube k'asa batasan
inda kanta yake ba.


A hankali ta fara bud'e idanuwan ta,
jin kanta ya mata wani irin
nauyi da k'yar ta iya bad'e su tar,
da cieling ta fara cin karo dan
tana kwance rigingin ne, a
hankali ta juya kanta taga
mutane kwankwance bisa
kallar gadon da ta tsinci kanta a kai,
sai masu fararen kaya da ke
ta kai komo gurin mutanen,
ta rasa tantace a inda take
a duniyar take ko ta mutu
ne ma ohon mata, wata mata
taga ta nuho ta da fara'ar ta,
ma'u da ido ta bita ji tayi tana
fad'in alhamdullilah tare da
kiran doctor bayan yazo ya
duba ma'u yaga ledar ruwan
da aka samata ya k'are dan
a gwaje gwajen da sukai sun
gano tana d'auke da ulser
wacce har takai cronical stage
shine suka d'aura ta akan magani
kuma suka d'aura mata drip,
bayan doctor yagama y'an
dube duben sa ya tafi, matar
ta matsa kusa da ma'u tare
da cewa "sannu da jiki baiwar Allah"
ma'u da k'yar ta iya bud'e baki
tace " ina nake"
matar tace " ki kwantar da hankalin ki, tsautsai ne
ya ratsa ki ka hau titi mukuma
muka banke ki a rashin sani,
sai a lokacin abun da ya faru
tas ya dawo ma ma'u a ranta
ta gode ma Allah raba ta da
yayi da wannan dan iskan
mutumin, matar ta cigaba
tace " an gode ma Allah ba
internal injuries, amman kin
samu karaya a k'afa dadai
y'an k'uk'ujewa a k'afa da hannu
da cinya, sai lokacin ma'u ta
kai duban ta ga k'afarta ta haggu,
da tun tashin ta taji tana mata
nauyi da azababben rad'ad'e,
ganin ta tayi nannad'e cikin
farin bandage, nan ta du ba
sauran jikin ta duk patch ne
na plaster da bandage Allah
yasa abun be shafi fuskar
taba, matar
ta katse mata tunani da fad'in
" yanzu duk ba wannan ba
tunda dai Allah yasa kin tashi
lafiya ba buguwar kai, sai ki
fad'a mana numbar wayar iyayenki
ko addreshin gidan ku dan mu kira mu fad'a masu
dan yanzu duk inda suke nasan
hankalin su yana kanki kuma
ba kwance yake ba, dan tun jiya
da dare baki farfad'o ba sai
yau da safe, duk da nayi mamakin
me ya fito dake cikin dare
kina gudu kuma har da kaya,
take idon ma'u suka kawo
ruwa jin an ambaci iyayenta,
sai da matar ta mai2 ta mata
tamabayar,
sannan ma'u cikin kuka take
fad'a mata bata da iyaye, matar
ta jajanta mata sannan ta kuma cewa a ina kike zaune to,
nan ma'u ta fad'a mata ba batada kowa garin nan
hasali ma ita bak'uwa ce,
dan a jiyan ma tazo garin
kuma
batasan kowa ba, tace to daga ina
kika zo, ma'u tace daga rugar nagge
tare da k'unshe kuka da yazo mata,
matar ta fuskanci halin da take
duk yadda akai akwai abun
a ya faru shiyasa ta bar inda
take zaune, amman sai ta k'udurin
baza ta kuma tambayar ta
ba akan hakan har sai an sallame su
taga ta samu natsuwa dan
ta fiskanci yarinyar bata son
maganar, sai ta canja maganar da fad'in
" ya sunanki"
tace " suna na ma'u."
ta amsa da " masha Allah asm'u."

A haka aunty nafy ta cigaba da kula da ma'u duk bills d'in asibitin ta biya,
tana bata magugunanta a kan
kari, hata peak milk d'in da doctor
yace ana bata saboda ulcer ta,
duk tana bata
sannan tana matuk'ar jan ta
jiki dan har labari take zaunawa
ta bata, ma'u ko sarkin jin labarai tai ta dariya da haka
shak'uwa mai k'arfi tashiga tsakanin su.

Cikin ikon Allah an kwacewa ma'u d'auri kuma an sallamesu, cikin k'oshin
lafiya, duk da ma'u k'yangyasa
k'afar tata take, bayan sun isa gidan aunty nafi,
Gida ne d'an madaidai ci dai2 zaman mutum biyu dan
d'a kuna biyu ne d'aya nata
d'ayan kuma yaranta biyu maza ke
shaering d'insa in sun zo hutu
dan duk suna makaranta d'aya
uni d'ayan kuma secoundry duk kuma boarding
suke kasancewar ba a garin suke makarantar ba.
aunty nafy taja ma'u a jiki sosai
ganin ta saki jikinta, haka kuwa akai
dan ma'u bata da bak'unta, barin ma gashi taga
fuska, dama ance shimfid'ar fuska tafi ta tabarma.

Sai da ma'u ta ida murmurewa tsab sannan aunty nafy ta nemi jin labarinta,
Ma'u ta fed'e mata biri daga
kai har wutsiya, jin labarinta
yasa ta k'ara jin tausayin ta
sosai, taso ta taimake
ta amman ita ma bawani hali
ne da ita ba, cikin share kwallan labarin ma'u aunty
nafy
tace "ni yarana biyu
duk
y'an makaranta ne kuma ni
ke d'awainiya dasu saboda
babansu ya rasu kuma dagin shi
ba wani taimaka mana suke
ba, gashi ni iyaye na sun rasu
kum dangi na bawani hali ne
dasu ba, gidan nan ma da muke
ciki gadon babansu ne, ni sana'a ta itace ina kwaso y'an
aiki daga k'auye ina kawo su
nan ga masu so, in lokacin
d'an hutun su yayi in kwashe
su in maida su gida su d'an kwana biyu, to duk cikin
su kowacce ina da share ta
na kud'in aikin ta, sannan ina
da mota wacce aciki nake
wannan zirga2 kuma ana mun
haya da ita, to da haka nake
samun da d'an biya mana
buk'atun mu wanda suka zama dole ni da yara na,
ranar da hatsarin ma ya faru
naje kai yaran hutune hanyar mu ta dawowa ne abun ya faru,
shi yasa ba kowa daga ni sai
direban da ke tuk'a motar tawa,
zan so in aje ki a hannuna
amman hakan ba zai yu ba,
saboda ina yawan tafiye2 kuma
ba wata wadata gareni ba
da zance zan k'arbi maraicinki
hannu bibbiyu ba amm.... ma'u
tai sauri katse ta da fadin wallahi
ita baza ta damu ba ai ita
ma d'in cikin talaucin ta taso
kuma da arzik'i da rashinsa
duk na Allah ne, aunty nafy
tad'an yi murmushi tace " bazaki gane
me nake nufi ba amman nan gaba za ki gane, yanzu
taimako d'aya zan maki wanda a halin yanzu shi
k'adai
zan iya maki, kuma nasan
zakiji d'ad'in hakan shine....




THE PROPHET MUHAMMAD ( S.A.W ) SAID: ANYONE WHO THOSE NOT SHOW MERCY TO OUR CHILDEREN NOR ACKNOWLEDGE D RIGHT OF OLDER PPLE IX NOT ONE OF US.



👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now