page 18

3.6K 261 0
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨









💎💎💎💎💎💎💎💎 *ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*NA*
_BILKISU ALIYU KANKIA_
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼










🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S📝(( Z.A.W))*
[ ~Gidan   zaman   lafiya   da   amana   insha   Allah~ 🤜 🤛 ]









Tiririn ♨ gaisuwata gare ki sarauniyar mata, halayan ki na birgeni wlh, *SADIYAH .G. MATAZU (YAR MUM)* my bestie ina yinki irin tottaly😍 wannan pege na ki ne ke d'aya kiyi yadda kike so, much love😘💋
















Page1⃣8⃣













A hankali ta d'auki basket d'in ta fito
tayi part d'in da aka cemata
na yayan ne ta isa bakin k'ofa
tayi sallama, tayi ya kai sau ukku amman ba amsa, jin shiru yasa ta murd'a k'ofar take kuwa taji ta bud'e, sai data kuma sallama sannan ta shiga, wani sanyi had'e da daddad'an k'amshi ne ya dake hancinta da ilahirin jikinta, ba laifi akwai tsabta, ba taga kowa a falon ba sai t.v dake kunne, ta k'arasa bakin diny table d'in ta aje basket ta cicciro kulolin da jug d'in kunun ayan ta aje, kamar yadda aka umarceta taje ta bud'e k'ofar dake mak'ale da diny area d'in, d'an k'aramin kicin ne, ta isa inda ake aje plates ta d'auko da cokulla da dai duk abunda za'a buk'ata na cin abinci ta kuma wanke su, sannan ta jera su kan diny kamar yadda taga uwar talle ta jera na ammie, ta d'auki jug ta isa wajen despencer ta tara mashi ruwa kamar yadda uwar talle ta koya mata,ta dire jug d'in kan tebur, sai da ta k'ara dubawa taga komai yayi yadda aka cemata sai dai abu d'aya ance mata inta jera mashi abinci ta sanar masa, gashi ita bata ga kowa a falon ba, ta k'arasa k'ofar kad'ai da ke jikin falon inda take tunanin d'aki ne tayi sallama nan ma shiru, tace

" yaya abdallah ga abincincin naka an jera" tana gama fad'a ta kama bakinta tana guntse dariya, dan jin abun tai wani banbarak'wai, ta fara bin fallon da kallo can idon ta ya sauka akan wani maxi size emlargement na wani saurayi fari mai jini a jika, sanye yake da uniform farare da ratsin baki kad'an a kafad'a, beret d'in kanshi ma fara ce, sai wasu igiyoyi golden colour da aka ratso su daga kafad'ar shi zuwa hammata har suka zagaya, tafin hanna yanshi sanya cikin fararen hand gloves, duk da ba fara'a yayi ba hakan be gaza kyawunshi fitowa ba, a fili ma'u tace "wannan ko shine yayan oho" sai kuma ta tsaya tasa hannu d'aya a goshi ta mak'e d'ayan kamar yadda taga yayi a hoton, ta k'yalk'yale da dariya tana fad'in "wahala", ji tayi ana k'ok'arin bud'e k'ofa cikin sauri ta fita tare da turo mashi k'ofar shigan ta kwashi takalmanta tafalfala a guje, taje dai2 shiga part d'in ammie taga wata yarinya me kamar daidai shekarunta da uniform a jikinta da alama ta dawo daga makaranta ne, ta rugo ta wace ta tana tsalle tana fad'in "ammie ammie na dawo ina kike?"
ma'u ta k'arasa ciki cike da sha'awar yariyar, ammie ce ta d'ago yarinya daga rugumar da tai mata tana fad'in "oyoyo auta kin dawo lafiya ya karatun"
Miemie cikin zak'uwa take cewa " lafiya lau ammie, yau nagaji sosai kuma an bamu home work da yawa bari dai inje inyi fitsari, in dawo in nuna maki" ta aje jakar ta ta cire safar k'afarta, ta ruga a guje tai bayi dan a matse take, bayan ta dawo ne tai turus ganin ma'u dan duk shigowarta bata ganta ba, ba ta cire idonta akanta ba tasa hannu tana tab'o ammie tana fad'in " ammie na wace wannan?."

" sabuwar k'awa na maki miemie"
cikin murna ta rungume mahaifiyarta ta, tana cewa " thank u my dearest ammie, dama kamar kinsan na gaji da zama ni kad'ai tunda aunty shaila tai aure duk da ita bawai ta cika shiga harkata bane amman da ta tafi banji dad'i ba"
ta k'arasa kusa da ma'u ta kama hanun ta tareda cewa " ya sunanki" ma'u cikin washe baki tace " ma'u sunana"
take mimi ta kyalkyale da dariya tace "bantab'a jin sunanki ba kamar na y'an k'auye" ammie ce tai saurin katse ta da cewa " kinjiki auta, sunanta fa Asma'u ba ki tab'ajin ana kiran masu sunan da ma'u ba"

mimi ta girgiza kai sannan ta cigaba " sunan ki Asma'u kenan amman ni Asmah zanna kiranki, wata k'awa tama da sunan ku d'aya haka muke ce mata, to ni sunana Bikisu amman ana cemun Miemie" ta fad'a tare da mik'o mata hannu tana fad'in "friends", ma'u tsaya wa tayi tana kallonta dan bata fahimceta ba, ammie ce cikin dariya tace " to Asma'u ki mik'a mata hannun ku gaisa mana" sannan ta mik'a mata suka gaisa, a haka suka ci abinci mimi sai cika ta take da surutu, itako sai dai ta bita da uhm a'a ko ta d'aga mata kai duk da itama ba baya ba wajen surutun sai dai dan bata ida sakewa bane shiyasa itama bata baje kollin surutun nata ba, haka suka ci abinci cikin nishad'i itako ma'u sai santi take dan bata tab'a cin abinci kallar wannan ba ga nama zak'ok'o sai murmushi suke mata, ga wani abu da taga sun had'a da aya, kunun aya kenan yai mata dad'i tai tasha kamar ba gobe, tana gode ma Allah dan bata tab'a cin mede-mede kalar wannan ba, sai da taci tai nat, bayan sun gama ne ammie ta fad'a mata yadda zatana ma yaya aiki da abubuwan da yake so da wana baya so, su ka gama magana akan cewa gbe zata fara, nan mimi ta fuskanci me aiki ce Asmar, duk da basa wulak'anta masu aiki suna jansu a jiki kamar y'ay'an gidan amman bata zaci asmah mai aiki bace yadda ta ganta tsab da ita ga kyau, dama tana jira ne su gama cin abinci ta jata d'aki ta tambaye ta wane skul take kua inane gidansu, duk da yadda taga Asmah nacin abinci kamar wata mayunwaciya, tasha kawai tanada ci ne, to yanzu ta gane, da haka tace

" Asmah zo muje in nuna maki d'aki na, kina son kina kwana a d'akina?"

Asmah ta d'aga kai alamun eh, itako ammie dariya tai ta wace turaka dan ita zata amsa girki, bayan sun isa d'aki mimi ta hau nuna mata abubuwa tana bata labarai kala2 har itama Asmah ta sake ta fara biye mata dan mimi akwai saurin sabo, bayan sallar magruba suka ci wani lafiyayyen tuwo da ammie ta girka da kanta, dan Abbah baya cin abincin y'an aiki dan haka  duk me girki cikin su, ita zata mai girkinshi alabadhi na yaran sai mai aiki tayi, bayan sun gama sallar isha'i mimi tace ma Asmah zataje wajen yaya Abdallah daga nan zata wuce wajen Abbah tai home work d'inta, tace "kiyi wanka kan in dawo" ta fiddo mata wata night dress Ash da pink doguwar riga ce iya gwiwa cotton, Asmah ta ansa tana godiya, mimi ta d'auki jakar makarantartar ta tafi, itako Asmah shiga toilet tayi ta tara ruwa masu yawa ta d'ad'e tana cud'a jikinta, a ranata ko tana ta k'ara gode ma Allah dan zata iya cewa tunda take a rayuwarta bata tab'a farnciki da nishad'i yini zungur ba kallar na yau ba ( Best day ever), sai da tagaji da wankan dan kanta sannan ta fito tai brush dan tana san yi abun birge ta yake ga macline d'in k'amshi dan sai ma tasha mai isarta take farawa, sannan ta fito ta cud'e jikinta ta mai sannan tasa rigar ta tufke gashinta da ribon kamar yadda taga ammie ta mata duk da da k'yar ta d'aure amman baiyi tsakiya ba sai yai gefe, kallon kanta tayi a madubi wani farin ciki taji ganin yadda tai kyau, ita da bama taganin kyawunta sai dai taji mutane na fad'a, amman yau taga tai kyau, duka kwana d'aya fa kenan, sujudul shukru tayi sannan ta jawo hotan ummanta ta bata labarin komai sai taga fara'ar ta ta yau kamar tafi ta kullum, har da d'an tsallenta na murna tayi kissing hotan ta maida ta aje bayan ta mata sai da safe, lol
ta kwanta saman gadon kamar yadda mimi ta umarceta, taja lallausan bargon ta lullub'e, a gaskiya taji dad'in zuwanta gidan nan sosai, ji yadda suke janta a jiki ba tare da nuna k'yama ko hantara ba, don haka ta d'auri aniyar itama zatayi masu aiki tuk'uru tunda bunda ya kawo ta kenan, tana ta santin ranar a haka bacci yayi awon gaba da ita tana tunanin aikin da zata fara gobe.






Ahhh sabon matsayi su ma'u an tashi daga ma'u an koma Asmah☺







*Qur'an and prayers have guided me at every step of my lyf, inspired me to do d righteous deeds, Ahamdullilah, guys keep ur recitation, ur memorization of d holy Qur'an and also ur  beautiful  prayers constant they do actually inspired & motivate u 2 do d righteous deeds trsut me!*





👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now