page 27

3.4K 197 0
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨




💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼






🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )


Ina mai baku hak'urin rashin jina kwana biyu  duk na gode da kulawa da kuke ban fans, ku cigaba hakan na sani nishad'i, kuma kusani da bazar ku nake rawa,  muje zuwa,  love y'all❤😘💋

Y'an uwana masoya na wannan page d'in naku ne boibiesssss nd babooooos
HAFSAT DALHA KANKIA
MARYAM IBRAHIM D'AN MALLAM
AND
AISHA IBRAHIM DAN MALLAN
kusani inayinku a yau da kulkum ku huta ku shekara 1500😄 boibies.






Page 2⃣7⃣









*Bayan sati biyu*

Rayuwa ta cigaba da gudana kamar yadda ya dace a gidan Alh. Muhammad Zayyan, bangaren Asmah kam komai gaba gaba yake, don yanzu matakin karatun da suke kai shine sun gama covering duka syllabus d'in primary school gaba d'aya, yanzu in kuka ga Asmah ko ku kaji tana zubo turanci baza kuce Ma'un rugar nagge bace, yabawa da k'wazonta da lesson teachern nata yayi ya kuma lura gaskiya k'ok'arinta nan yaci ace an sata makaranta duk da ya fahimci matsayinta a gidan, baiyi k'asa a gwiwa ba ya sanar ma Ammie kan cewar yana da kyau a sa Asmah makaranta domin basu san amfanuwar da za suyi da karatun nata ba, Ammie taji dad'in batun kuma itama taga dacewar hakan domin a zahirin gaskiya tana ma Asmah tsananin so ji take kamar ita ta haife ta,  haka kuwa akai sun tattauna da Abbah kuma ya bata goyan baya don haka aka amso ma Asmah form d'in makarantarsu Mimi kasancewar an gama k'arshen zangon karatu na shekara 3rd term, lokacine na d'aukar sabbin d'alibai y'an jss1, an cika mata form da sunanta na asali wato ASMA'U MUHAMMAD MASKA kamar yadda ta fad'a masu Ammie dasu ka tambaye ta meye sunan babanta, taje ta rubuta common entrance examination cikin sa'a tasa mu addmission a makarantar su Mimi mai suna DEMOSTRATION SECOUNDARY SCHOOL KANO,  duk wani fees an gama biya mata ranar komawa makaranta kawai ake jira Asmah kam kullum cikin d'auki take, farinciki gun Mimi kar ku tona.

Asmah ana ta d'aukin zuwa makaranta, duk wani shiriAmmie tagama mata shi an anso mata d'inkin uniform ranar kawai ake jira, wannan kenan bangaren ya Abdallah kam sauk'i sai na ubangiji, sai dai wani abu da ya d'aure ma ilahirin gidan kai shine wata shak'uwa ce mai tsanani ta shiga tsakanin Abdallah da Asmah, ko in ce maku ta b'angaren Abdallah kawai don ita Asmah tausayin Abdallah kawai take ji saiko son musulunci in banda haka ba komai,  shiko abun ya wuce gaban wasa wanda har yake sa su Ammie suna mamaki sosai, don yanzu takai matsayin in ba Asmah ba,
ba wanda ke bashi abinci ya amsa ciki kuwa hadda Abbah, haka kuma in Asmah bata kusa to baiyin bacci haka dai ake shan daga, kullum Asmah sai dai ta tsaya a b'angaren shi suyi ta surutu tana bashi labarai a haka in bacci ya d'auke shi sai ta fito ta koma makwancinta, wanka ma baiyi sai in Asmah ta had'a mashi ruwa, kai in tak'ai cemaku surutai he just can't blend without her and he can't explain how and why kamar yadda su Abbah sun kasa gano komai akan sabuwar shak'uwar da ke tsakaninsu illah iyaka sun barshi akan shirmen Abdallah ne ya motsa, itako Asmah abun mamaki ma yake bata yadda Abdallah ya canja mata salo.




*********      ************

Auntyn yara ta samu go ahead d'in tafiyar ta gun Abbah kamar yadda suka k'udurta, kud'i Abbah ya baje mata akan ta kaima majinyacin domin k'arya tayi mai akan cewa zata gaido marar lafiya, duk yadda Abbah ya dage akan cewa da Na iraki za ayi tafiyar amman abun yaci tura don ta tubure tace sam a cewar ta ita da Jumman Jos za suyi tafiyar kawai abun da take so a basu mota, direban Jumman Jos d'in za sutai tunda shi ya saba zuwa Jos sosai ya gama lak'antar hanyar sosai, dole Abbah ya hak'ura yabi ra'ayinta, haka kuwa akai ranar tafiya mutumin da suka ce shine diraban Jumman Jos yazo kamar yadda ita ma Jumman ta iso duk matafiyan sun shirya sun kuma yi sallama da gida, Ammie kam fruit da drinks masu yawa ta siya tace akai ma marar lafiya, haka suka tafi suka kama hanyar Jos da yake tafiyar asuba sukai don haka ana kiran sallar magaruba suka isa garin Jos, a gidan Auntyn yara suka sauka anyi murnar ganinsu tunda dama ta sanar masu zuwannasu duk da dai basu san ainihin dalilin zuwan nasu ba,  kawai dai ta ce masu ne za suje gaisuwar wata k'awar su dake nan wani k'auye kusa dasu, da k'udurin dake zuciyar su suka kwana, washegari da safe misalin k'arfe 10 suka d'au hanyar k'auyen, har sai da suka zo inda mota bata bi suka sauka suka cema ya'u abokin harkar jummai wanda ya tuk'o su da ya jira su, shi dai ba ruwan shi iyaka a baje mai kud'i yai aiki koda ko na kisa ne, Jummai tai jagora wasu mandala mandalan duwatsu suka rink'a hawa da k'yar a wahalce suka isa k'arshen duwatsun, suka isa wani waje, wajen yana d'an da duhu kasancewar wasu dogayen bishiyoyi masu yalwataccen ganyaye da suka ma wajen k'awanya, ita dai Auntyn yara bin jummai kawai take haka suka rink'a ratsa bishiyoyin har sai da suka isa wata y'ar k'aramar bukka, wadda aka sa karare da ciyawi aka zagaye ta wata irin k'ara suka ji wadda ta hassada ma Auntyn yara wata mummunar fad'uwar gaba,  tare da yankewa k'asa tana fad'uwa, ita ko gogiyar da yake ta saba bata ji wani tsoro sosai ba, take ta d'ago Auntyn yara tare da rad'a mata cewa duk abunda zataji dake wa zatai, kai kawai ta d'aga mata, itako ta jata suka cigaba da tafiya, basu daina jin razanannun k'ararrakin ba har sai da suka isa gaban bukkar, wani waje jummai ta nuna mata tare da mata alamar ta zauna a gun,  sannan ta juya ta baya saitin bukkar wani gwale gwale tai ta fad'i kamar daga sama kawai suka ga bokan zaune a gabansu, da sauri itama jummai ta baje k'asa tare da durk'usar da kai, wani abu mai gashi gashi yasa ya tab'a mata kanta, ta wutsiyar ido ta kalli Auntyn yara take ita ma tayi kamar yadda taga k'awar tan tayi, boka darb'usa ya saki wata shed'aniyar dariya,  sannan yace "yanzu ya kike so ayimai" a ida burkar da k'wak'awalwar ko ma aka she shi gaba d'aya"

"A'a Mallam k......

"Keeeee dakata waye Mallamin?"

Jummai ce tai caraf wajen cewa " ayi hak'uri Darb'usa laifi nane da ban fad'a mata ba, dan wannan shine farkon zuwanta a gafarceta"

"Gwara dai kuje ku nemo Mallami in shi kuke nema"

Wannan karan Auntyn yara tai magana " Ayi hak'uri darb'usa tuba nake"

"Hehehheheheh inajinki"

Tace"A'a banson a kashe shi, ai ganinshi a haka sai yafi bak'anta masu rai akan ganin gawar shi, don haka kawai a ida tabbatar mashi da hauka akansa"

"Hehhhehehehehehe yayi manyan shed'anu aljannu ma suna sara maku,  yanzu indai wannan kawai kike so bai da wahala, ina masu maganar taku? "

Jumai takalle ta, ta fahimta dan haka ta bud'e jakkarta ta baje mashi damen kud'i a gabansa, dariyar shi ya saki sannan yasa wannan abun me gashi gashi ya bugi kud'in tsab suka b'acce, sannan ya ce " zan baku wani ruwa ku tabbatar ya wanke fuskar shi dashi kuma ya shak'e shi sosai, to buk'atarku ta biya, yanzu ku tafi yanzu zan aika aljannu a samo mun ruwan a can fadar sauraniya Akisa can k'asan ruwa, kafin ku fita a dutsen fada sak'onku zai iso"

Dariya ya k'arayi sannan ya b'ace, itako Auntyn yara sai mamaki take, da baya baya suka bar wurin sannan suka doshi hanyar komawa, sun hau kan wani dutse kenan kawai suka ga wata kwalba, Jummai ce ta d'auka tace gashi nan ruwan ya iso, Auntyn yara tace "kin jiki daga ganin kwalaba a hanya kice itace"

" Inace yau ne farkon zuwan ki wajen nan, to ki banni in yi magana, ke dai amsa kisa a jakka ki kuma tabbatar kinyi amfani dashi kamar yadda ya ce maki za kisha mamaki"

Da k'yar suka baro gurin suka dawo suka cimma ya'u, suka d'au hanya suka koma gidan su Auntyn yara, Jummai ta wuce gidansu da zummar gobe da safe ta dawo gidan su k'awar tata, don da safe kuma za su juyo kano.




A/N

Sorry 4 d late update😔


AS HOW ALLAH PROTECT KA'ABAH AMONG @LL HOUSES,  AND PROTECT ZAM ZAM AMONG @LL H2O ND PRITECT MUHAMMAD PBUH AMONG @LL MANKIND,  HE PROTECT QUR'AN AMONG @LL BOOKS, MAY HE PROTECT U ND UR BELOVED FAMILY 4RM ALL EVILLS. AMEEN
JUMMUA'T MUBARAK FANS❤💋😘

👸🏼 *Queen bk* 👸🏼

ZAN SOKA A HAKAOnde histórias criam vida. Descubra agora