page 30

3.7K 214 0
                                    

[10/02 2019 9:43 pm] 👸🏼Queen bk👸🏼:  🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨


💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼




🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )



Assalamualaikum my lovely readers, i don't even know where to start, wallah am short of words, i know saying sorry only won't settle the explanations you owe me, i know u've been expecting my update, zoo sorry for d disappointment, sincerely speacking am a lazy writter😞, so bear with me, i promise u i will see to that, abin nawa ne sai addu'a fans ku riƙa sani a addu'oinku dan Allah🙏🏻










Page3⃣0⃣

Wahse gari ranar asabar,  tun safe Asmah taje sashen Abdallah, sai dai tana shiga ta fito a gigice ta koma sashen Ammie, sai ko akai sa'a sukai kicib'is da Ammie a kitchen, ganin yadda ta shigo a firgice yasa Ammie saurin tambayar ta me ke faruwa, cikin in ina Asmah ke faɗin "Am-m-mie ya Ab-da-ll-ah" Ammie kam duk ta sha jinin jikinta ganin yadda Asmah ke magana kuma tana kiran ɗan nata, ta san ko meye akwai matsala, da ƙarfi take faɗin "meye ya samu Abdallannnnn"
cikin ƙwalla Asmah ke faɗin "Ammie ya abdallah zai mutu kizo fa kiga me yake"
Ai tun kafin Asmah ta ida magana Ammie ta ɗau hanyar part ɗin shi da sauri tana jin an anbaci mutuwa, Asmah ta rufa mata baya, Ammie na tafe tana maimaita *inalillahi wa inna ilaihir raji'un,* da sassarfa ta ƙarasa d'akin, ba ƙaramin karaya zuciyarta tayi ba ganin ɗanta a ƙasa yana ta birgima yana riƙe cikinshi, duba ɗaya zaka mai kagane yana cikin matsananin zafi na ciwo, idanunshi duk sun kakkafe ga bakinshi sai zubar dan farin kumfa yake, da sauri Ammie ta ƙarasa inda yake ta tallafo kanshi ta rungume shi, hawaye ɗaya na bin ɗaya a kan kuncinta, "ya Allah, ya rabhi ka kawo mun agaji, dan darajar maganganun da ke cikin Al Quraninka mai girma, da son da kake ma fiyayyan halitta Annabi MUHAMMAD (SAW), ya Allah ka sauwaƙe maɗana wannan zafin ciwon, ya Allah ka kawo mashi sauƙi cikin gaggawa, domin a gare ka sauƙi yake, ya mamallakin kowa da komai" duk cikin kuka take maganar, Asmah tace Ameen kana ta matso tace "Ammie a kira doctor mana?" take Ammie ta dawo duniyar dan ita da lissafinta duk ya toshe, duk ta ruɗe ma ta rasa abun yi.

"Yauwa Asmah maza jeki wajen Auntyn yara kice ta kira Dr.Kb, yazo da sauri urgent issue ne, gashi Abbansu baya nan i maza"

Bayan fitarta, Ammie ta maida dubanta ga Abdallah da yake shirin shiɗewa, ganin yadda yake riƙe ciki yana mutsumutsu, bata taɓa ganin Abdallah cikin irin yanayin ciwo haka ba, don shi baya da rakin ciwo shi yasa ma duk ta ruɗe haka, a hankali ta sa hanunta tana shafa mashi kumatu tare da tofa mashi AS'ALULLAHUL AZHIM RABUL ARSHIL AZHIM AN YASH FIKHA, so bakwai, sannan ta karanta mashi LA ILA HA ILLA ANTA SUBUHANAKA INNI KUNTU MINA ZALIMIN so ukku, ta karanta ayatul kursiyy, amanan rasulu da fatiha ƙafa ɗaya ɗaya, sannan ta ɗora da ALLAHUMMA LAKAL HAMDU, WA ILAIKHAL MUSHTAKHA, WA ANTAL MUSTA'AN WA BIKHAL MUSTAGAZ, WA ALKHAL TUƘULAN WALA HAULA WALA ƘUWATI ILLA BILLA, sannan tace ya Allah na roƙe ka da sunayenka kyawawa, kuma nayi tawassali da wannan addu'ar, ya Allah kai ka tseratar da Annabi musa daga kaidin fir'auna ta wannan addu'a, ya Allah ka yaye ma ɗana duk wata cuta, ka raba shi da duk wani mai cutar shi, kamusu katangar ƙarfe ya Allah, kai kace mu roƙe ka zaka amsa mana ya Allah kai me iko ne akan komai, ya Allah kasa ciwon nan kaffara ne kuma ka yaye mashi duk wani cuta da cutarwa gareshi ya rabhi" nan ta shiga tofa mai ko ina a jikin shi.

"Ammie me ya sameshi haka" cewar Auntyn yara muryarta cike da mamaki.

Girgiza kai kawai Ammie tayi, kafin suka ji sallamar Dr.KB, dama tuni Auntyn yara ta gaya mai, kuma dama gidan shi na kusa, infact ma shiyasa ma ya zama resident doctor ɗinsu, kuma an ci sa'a yana gida domin baya call jiya da dare yayi dutyn shi, yana zuwa ya amsa Abdallah bayan sun mayar dashi kan gado take ya shiga duba shi,

ZAN SOKA A HAKAМесто, где живут истории. Откройте их для себя