page 57

4.7K 300 32
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨





💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼







🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )















Page5⃣7⃣







Ya faɗa yana karkaɗa idanu yana kallon waje, juyowa yayi sai kuma yayi sakakai ganin yadda yanayinsu yake, ƙarasowa yayi yace "Ammie! Beauty! me yasa ne kuke ta kuka wai?".


Ammie ta share sabbin ƙwallan da suka zubo mata tace "Abdallah kukan farin cikine, Beautynka ƴar uwarka ce ta ƙut da ƙut".

Murmushi yayi kamar ya fahimta sai kuma yace "ai Ammie na sani ai beauty ƴar uwata ce ba shiyasa muke zaune gida ɗaya ba? kuma har ta zama matata ba?".

"Ay yayansu shiyasa bacin haka kuma ita ɗiyar hab........." da sauri ya tari lumfashin Ammie da faɗin,

"Yehhh wallahi an fara ruwa kuzo muje muyi wasa a ruwa dan Allah" ya faɗa yana jansu da hannayensu, ammie ce ta zare hannunta ganin shi da gaske janta zai yi su fita cikin ruwa tasan Abdallah da san ruwa, cewa tai "ni rufa mun asiri yaro na shiga ruwannan ai sai wata ba ni ba".


Nan Ammie tasa sukai sallar magruba sannan ta zubo masu tuwo a plate suka zauna suka ci tare, suna ta hira Asmah da Ammie ne ke firar dan shi Abdallah hankalin shi na window yana kallan yadda ruwan ke sauka yana ta murmushi shi kaɗai abunshi yana ƴan suratan shi, ganin ruwan ya ƙara zugewa Abdallah ya buga tsalle ya tashi yana cewa "yeeeeee Allah kawo ruwa muje malali mallam na gyangyaɗi yana saka lomar tuwo" yana yi yana ƴar rawar sa, tun daga Asmah har Ammie ba wanda bai dara ba, ganin suna dariya shima ya ɗau sowa.

Hannun Asmah ya kamo yana faɗin "Beauty i sauri kizo mu tafi wallahi kiyi sauri kar ruwa yafi mu gudu" ya faɗa yana janta.

Ammie ta kalle ta tace "ai ki tashi kawai ki bishi dan ya matsa kuje kawai sashenku sai gobe amman bari na ɗauko maku lema sabidda kar ruwa ya jiƙa ku".

Ammie ta ɗauko masu lema ta basu duk taji bata son su rabu kamar yadda itama Asmah taji nan dai da ƙyar sukayi ma juna sai da safe sanna ta bi Abdallah suka wace suna fita waje ta buɗa lemar tana rufesu su duka amman Abdallah sai zillewa yake yana shiga cikin ruwan yana ihun daɗi yana faɗin "Beauty shigo cikin ruwan kiji wani daɗi wallahi".

Haka ya yaye mata lemar tuni iska tai sama da ita, ganin ya tsaya sai wasa yake a wajen tace muje can part ɗin mu sai na taya ka wasan dan yau ina cikin farin ciki, hannunshi taja su ka tafi suna shiga garden ta rufe ƙofar garden ɗin da sakata, gani tayi ya isa tskaiyar filin yana ta jujjuyawa yana jin ruwan a kowane sassa na jikinshi daka ganshi kasan yana matuƙar farin ciki, ƴar varender shiga part ɗinsu ta isa ta aje jakarta da gyalenta sannan ta dawo inda yake ta shiga yin abunda yake, ba ƙaramin daɗi yaji ba ganin Asmah na taya shi tsayawa yayi da abunda yake yana kallonta yana jin wani shauƙin ƙaunarta na shigar shi ba ƙaramin birgeshi tayi ba, ita ma tsayawa tai tana kallon shi tana dariya da hannu take mashi alamar me ya faru mu cigaba mana, dariya ya saki shima yace "kalla beauty haka akeyi" ya faɗa yana ɗaga kanshi sama tare da buɗa bakinshi yana juyawa a hankali can kuma sai ya sakko da kanshi yana nuna mata ruwan da ya taru a bakinshi sai ya haɗe yana faɗin "kin gani na sha ruwan Allah".


ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now