page 65

5.2K 312 32
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨







💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*_NA_*
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *_QUEEN BK_* 👸🏼







🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan   zaman  lafiya  da amana    insha    Allah🤜🏻🤛🏻))




*ITZ_QUEENBK @ INSTA GRAM*








PAGE 65







Almighty. We belong to You and to You is our return.Shower Your everlasting Mercy on us always, forgive us and guide us towards that which pleases You at all times. Help us to stay clear of that which displeases You.May You accept all our prayers and grant us ease fidunya wal Akhira. Aameen, juma'at Mubarak.



_ASALAMU ALAIKUM._
*FATAN KUNYI SALLAH LAFIYA ALLAH YA BAMU LADA YA KARƁI IBADUNMU AMEEN. WELL I'VE BEEN TRYING TO UPDATE A PAGE TO SERVE AS MY BARKA DA SALLAH TO YOU GUYS BUT COULDN'T AND DO YOU KNOW WHY? OK PAGE BIYU NA RUBUTA AMMAN SADLY DUK SUN GUDU😭😭😭 HAKAN KUMA BA ƘARAMIN CI MUN TUWO YAYI A ƘWARYA BA GANIN I CAN'T RETRIEVE THEM AT ANY COST, ANYWAY DAI WANNAN PAGE ƊIN BARKA DA SALLAH NE GA DUKKAN MASOYANA MA BIYA KUMA MAKARANTA LITTAFIN ZAN SOKA A HAKA INA MAKU FATAN ALKHAIRI A DUK INDA KUKE A FAƊIN DUNIYAR NAN, WAENDA KUMA SUKA YI MUN MAGANA KAN NASASU A GROUP SUNJI SHIRU NE DALILIN RASA CHATS ƊINA DA NAI GABA ƊAYA BA LAIFI IN SUN ƘARA MUN MAGANA NI KUMA ZANYI ƘOƘARI INGA NASASU INSHA ALLAH.*







*INA MIƘA SAƘON BARKA DA SALLAH TA GA ƘUNGIYAN NAN MAI AMANA KARAMCI SO SANIN YA KAMATA CIKE DA GASKIYA DA SON JUNA 🇸🇦 ZAMAN AMANA WRITER'S FORUM, UP UP DEARIES SHUWAGABANNINMU ALLAH JA ZAMANINKU YA ƘARA GIRMA DA ƊAUKAKA GAISUWA TA MUSAMMAN GA NAMESY NA MY BK, INA YINKU DUKA IRIN SOSAI ƊINNAN❤😍💋*








A hankali ta buɗa idanunta tana miƙa haɗe da salati tare da karanto addu'ar tashi bacci, dubanta ta kai ga agogo taga har sha ɗaya da rabi ta gota da sauri ta tashi tana faɗin "inalillahi ji yadda rana tayi sosai amman muna kwance muna ta bacci hankali kwance" Abdallah ta kalla da yake kwance yana ta shaƙar baccinshi daga gani ma baccin yana mai daɗi dan har ɗan murmushi fuskarshi ke ɗauke dashi ita ma murmushin kawai tayi ta ƙara ja mashi bargo.




A gaggauce ta faɗa toilet sai da ta gyara shi sannan tayo wanka ta shirya kanta cikin wata straight gown ta atamfa abunka da mai diri ga tsawo tsaf rigar ta zauna mata a jiki cas cas tai mata masifar kyau sannan ta coke kalabinta toilet ta koma ta tara ruwan wanka masu ɗumi sannan tasaka turarurrukan wanka a ciki kana ta koma ɗakin a hankali ta yaye ma Abdallah bargon shi sannan ta maye gurbin bargon ji tai ya ƙara ƙanƙameta jikinshi har tana tunanin anya kuwa bacci yake ɗaga kai tai ta kalle shi sannan ta tabbatar da bacci yake sosai, a hankali ta shiga hura mai iskar bakinta a kunne tana shafa mashi kwantaccen sajenshi wani narkewa taga yana ƙarayi yana ƙara jin daɗin baccinsa, cikin wata sanyayyiyar murya ta raɗa mashi "babyna ka tashi gari ya waye kaga har sha biyu tayi yanzu kaga har an kira azahar" buɗa idanshi yayi ya zuba mata su ko ƙiftawa ba yayi ita kuma sai sakar mashi wani ƙayattacen murmushi take, mirginasu yayi ta koma ita ce a ƙasan shi sannan ya rungumeta yace "a'a beauty ki bari mu ƙara bacci ɗan kaɗan sai mu tashi" da kyar ta iya magana saboda nauyinshi gaba ɗaya dake kan jikinta cewa tayi "a'a ya Abdallah ka tashi kaga su Naty na can na jiran mu kuma ka ɗaga ni kar haƙarƙarina su ɓalle kana da nauyi kaifa ƙaton baby ne" ta faɗa tana tura mai ƙirji dan ya tashi, sai da ya kara matseta har tana sakin wata ƴar ƙara sannan ya gangara gefenta yana faɗin "to yaushe zaki suyo mun ƙaramar Baby yadda za muna wasa da ita".


ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now