page 70

3.3K 237 31
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨








💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*_NA_*
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *_QUEEN BK_* 👸🏼










🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan   zaman  lafiya  da amana    insha    Allah🤜🏻🤛🏻))








_Itz_queenbk @ insta gram_









Page 70







Da yanma bayan la'asar Asmah ce sai kai komo take a falonta ta rasa yadda zata tunkari Ammie da batun zuwa katsinan, wata zuciyai taji tana fad'a mata,

"Dole fa sai kinyi k'arya zaki sha Asmah dan duk yana cikin yak'in".

Hannunta ta d'ora a baki tana fad'in "karya? " murmushi tayi ta d'auki fruit juice d'in da ta had'a ta wuce b'angaren Ammie , a falo ta sameta suna ta k'idayar kud'i ita da aminiyarta wadda suke buisness tare ita ma yar jahar katsina ce sunanta Hajiya Zainab k'awar kasuwancin Ammie ce wadda tazo yau dan su d'an tattauna wasu batu da suka taso a hanzarce dangane da kasuwancin nasu kuma gobe zata koma.
 

Asmah ta shiga da fara'a tana masu sallama, sanye take da dogon hijab wanda y'an kwana kin nan bata san me yasa ba indai zata fito daga b'angarenta sai ta samu kanta da sanya dogon hijabi, waje ta samu ta zauna tare da ajiye jug din drink d'in a gefe guda sannan tace,

"Barkanku da hutawa Ammie".

Dukkansu suka amsa da "barka kadai" Hajiya zainab ta dubeta tana murmushi dan tun farkon ganin ta da Asmar taji tana santa saboda hankali da natsuwarta.

Sai da suka kammala k'idaye k'idayensu sannan suka zo suka baje suna cigaba da lissafe lissafensu, Asmah ce ta tashi ta isa kitchen cike da kewar Miemie dan tun lokacin da suka gama Jamb ta wuce Mai duguri wajen Naty, cups d'in tangaram biyu ta d'auko sannan ta koma, zuba masu tai ta babbasu duka suka karb'a suna yaba hankalinta, matsawa kusa dasu tayi tana fad'in "ko a maku tausa ne Ammie? " dan tasan Ammie da san tausa ta fad'a tare da fara danna k'afar Hajiya Zainab,  kafad'arta ta dafa tana cewa "madallah da d'iyar kirki ki barshi kinji ki zauna ki huta".


Ammie tayi murmushi tare da fad'in "zo nan y'ar d'iyata na lura kamar da akwai magana bakin ki fad'i inji miye? ".


Asmah ta matsa kusa da ita kamar yadda ta buk'ata cikin sigar magana da manya tace "Ammie dama Baba yawale ne bai ji dad'i ba shine nace in zaku mun izini inje in gano shi dan Allah kamin mu fara Neco".


"Wa iya zubillahi ashsha shine kika tsaya nuk'u nuk'u Asmah ko kin canja Ammie ne ban sani ba ban sanki da haka ba irin wannan ki rink'a samuna direct kina fad'a mun kinji? ".

"Ban canja Ammie ba kuma bazan taba canjawa ba zan ki yaye gaba insha Allah Ammie".



"To shikenan meye ne ya ke damun Baba yawalen? ".



"Ban kai ga sani ba tukun Ammie".

"To shikenan Allah yabashi sauk'i, yanzu abunda za ai tunda kinga gobe ne Mahmud yake komawa kuma shine dama zai wuce da Hajiya Zainab to kawai ki shirya sai ki bisu alabashshi sai ki kwana uku can zanzo duba jikin nashi sai mu juyo tare kuma insha Allah zan kira shi ta waya na fara gaishe shi kafin na iso".


ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now