page 1

17.9K 804 27
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨

💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*NA*
BILKISU ALIYU KANKIA
*((QUEEN BK))*


🚩ZAMAN AMANA WRITTER'S ((Z.A.W)) ASSOCIATION (( Gidan zamam lafiya da amana insha Allah))


~GODIYA~ 🙏🏻
Ina mika godiya ta ga Allah mai kowa mai komai, da ya bani ikon rubuta wannan karamin littafin, kuma yasa mu amfana da abun da ke ciki mai kyau, ya kuma bamu ikon guje ma abunda ba yada kyau, ameen.

~SADAUKARWA~✊🏻
Na sadaukar da wannan littafin ga kakanni na dasu ka riga mu gidan gaskiya, da duk wasu musulmai da suka riga mu gidan gaskiya, Allah kaji k'ansu ka lullube su da mafificiyar rahamar ka kasaka masu da gidan aljannarka, bayannan ina rokon Allah ya jibanci al'amuran iyaye na yayi masu jagoranci mai kyau duniya da lahira, yaji k'ansu kamar yadda suka ji k'aina da ina k'arama, ameen ya rabhil izhati.

~SANARWA~ 🗣
Duk wani ko watan, da yaga suna, ko halayya, ko labari, yazo daya da nasa, to ina mai sanar masa, arashi ne aka samu, domin wannan littafin nawa k'irk'irarrene.

_
_I devoted this page to the family of ALHAJI, MUHAMMAD KISKON KARATU_

Page 01⃣

Zaune take, cikin jerin masu saida fura da nono a kasuwar "nagge dadi goma", na rugar fulani da take cikin garin kaduna.

Ta tasa kwaryar fura da nononta a inda suka saba siyar wa, sanye take da sak'i fari na kayan fulani wanda daga gani kasan sunji jiki sosai,
Tana zaune ne a inda ta saba zama kan wani dutse kusa da wata mai dai dai shekarunta,
Wanda ita ma kayan fulanin ne a jikin ta, amman nata sun danfi sabunta,
duk wanda ya kalleta sai ya k'ara, saboda kyawunta irin na asalin fulanin nan ne.

Sai kalle kalle take taga ta ina jauro zai futo amman babu shi babu alamun shi, ta d'an b'ata rae domin bai taba kaiwa kamar haka bai xoba, cikin xuciyar ta take fadin

" ohh ni ma'u ko ina jauro ya shige ne har yanxu baixo ba nasan dae kamar yanxu ya gama aikin shi na shagon shayin shi sae dae na dare."

( ( dama jauro yana aiki da wani mai shagon shayi da indomie a can sabon layi a burni, yana taya shi aiki dasafe kuma da dare, shagon yana cikin KADSU ne))

Kullum in ya tashi aikin safen shi ta kasuwar nagge yake branch yaje yasha fura sannan ya wuce ruga, don shi bai gane ma cikin shi in dae ba furar yasha ba, to a haka ne har suka saba da ma'u, har yagano matsananciyar wahalar da take sha wajen gwoggon ta, kasancewar kuma rugar su daya yana jin yan jite jite a bakin mutane, don haka yake tausayin ta kuma yake taimakonta,
A haka abun har yarikide ya xamar masu soyayya, kasancewar ita kuma bata da gata duk fadin rugar nan tasu, tun tana karama daga baffanta sae ko jauron. shiyasa suka saba sosai
Kullum in yagama aikin safen shi zae zo yasha furar ~N~ 70 wajen ma'un shi, sae ya bata d'ari sai tasa talatin a asusunta don gwoggo ba ta bata ko y'ar ficika cikin kudin cinikin,
Wannan saba'in din da yake shan furar ba karamin taemakon ma'u yake ba wajen cinikin furar ta, dan dama furar da gwaggo ke daura mata ba ta wuce ta dari biyu, duk kuma radda bata saido ba to suna kwasan y'an kallo da ita.

To yau gashi shiru ba mai taimakon nata, ma'u taja k'aramin tsaki ta harari kwaryar furar ta wadda take cike don yau ko ba sa'a, tunda ta fito cinikin hamsin tayi, dama tana hasashen in jauro yaxo ya amsa tasa ta had'a zae kama dari da ashirin ko ba komai ta saida abunda ya fi rabi, baza ta sha masifar gwoggo ba sosai, tunda dama ita dae ko yane taji dumus, ma'u tak'ara jan tsaki tace

"gashi har na dama furar".

Ji tayi an dafata, ko bata juya ba tasan lamunde ce dake zaune kusa da ita, lamunde ta cigaba da fadin cikin hausa tasu irin ta fulanin da hausa bata kama bakinsu ba,

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now