page 63

5.1K 243 17
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨








💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*_NA_*
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *_QUEEN BK_* 👸🏼








🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah🤜🏻🤛🏻))









*Page* 63







*"ANY PERSON THAT ALLAH PUTS IN AUTHORITY OVER OTHERS AND THEN THE PERSON DIES BETRAYING HIS TRUST: ALLAH WOULD NOT LET HIM SMELL THE FRAGRANCE OF THE GARDEN (PRADISE)"*
_MUSLIM_ .









Yanzu satin su Asmah ɗaya da kwana biyu cif a Mai duguri sosai kuma hankalin Ummah yake kwance luf ganin komai na tafin mata dai dai kamar ta tsara, sosai ita ma Naty hankalinta ya ƙara kwanciya ganin ɗiyar tata ta samu natsuwa sosai ba kamar da ba ta wani ɓangaren kuma auren jikokin nata yana ƙara soya mata rai so ba adadi, a hankali Ummah ke ɗan zagayawa dasu cikin dangi da suke kusa dan sada zumunci, yau take alhamis kuma yau ta kama ranar da zasu tafi katsina domin kai ziyara gurin dangin mahaifin Asmah tare da gano kakanta don shi baizo ba sai dai matarshice tazo, tafiyar daga Asmah sai Ummah za'ayita dan sam Abdallah yace baya zuwa sun rasa mai yahau kansa, ba dagar da ba'ayi dashi ba amman yaƙi yadda duk kuwa da bai masan dalilin tafiyar tasu ba, dole Naty tace a ƙyale shi tunda daman ba zuwanshi bane na farko can ɗin dama can yana zuwa, da yake wata sa'in Ummah na tafiya dashi in yazo wajenta hutu konan wajen Naty ita kuma lokacin ya kama zata kai ziyara wajen dangin shi marigayi Muhammad ɗin tana zuwa dashi suma sun sanshi, tunda dai ya fara ciwon shi ne be taɓa zuwa ba sai dai suzo gaishe shi su daga can, hakanan suka haƙura zasu tafi ba dashi ɗin ba, Asmah kam ko kaɗan bata ji daɗin ƙin zuwan nasa ba hakanan dai kawai ta danne.





Zaune take gefen gado tana ƙara zuge ɗan ƙaramin akwatin da suka zuba kaya ita da Ummah domin kwana uku zasuyo can ɗin, sanye take da wata doguwar riga na atamfa ɗinkin yayi kyau sosai ya ƙara haskakata, cikin sanyi jiki take komai don jikinta asaluɓe yake da lamuran Abdallah duk sai taji bata son tafiyar ma kwata kwata ba abunda yafi ci mata tuwo a ƙwarya kalar yadda bata ma san dalilinshi nayin fushi haka ba, Ummah ce ta shigo itama cikin nata shirin tana faɗin,

"Asmah i maza mu tafi kinga jira bayada daɗi gashi tun ɗazu Mal Habu ke jira zai kaimu kuma kinga sauri yake yaje ya dawo a yau ɗinnan".


"To Ummah" ta faɗa tana tashi ta isa gaban madubi a gagauce ta ɗaura kallabi ta jawo mayafinta ta yana har kai ta jawo akwatin ta fito nan ta iske Naty da Abdallah sai surutansu suke, duƙawa tayi gefen Abdallah tace "ya Abdallah ina kwana".



Sai da ya kalleta sosai sannan yace "lafiya lau beauty".


Samun kanta tai da harararsa ƙasa ƙasa a ranta take faɗin "kamar dagaske hmm ni wannan miskilancin naka yana cuta ta wallahi".



Ko kallansa bata sake ba ta koma kusa da Naty tana ƙara gaisheta tare da faɗa mata zasu tafi, Naty tai murmushi tana kamo hannun Asmah tare da faɗi "Allah ya kiyaye ya tsare maku hanya kuje lafiya ku dawo cikin amincin Allah amman ta wajena sai naga fuskarki kamar bata cikin yayayin da ya kamata ta kasance sai ma akasin hakan ke bayyana a fuskarki meye damuwarki ne ƴannan?".




ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now