page 5

4.5K 289 5
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨




💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
         *NA*
BILKISU ALIYU DALHA
*((QUEEN BK))*





*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITER'S*
'''(Gidan zaman lafiya da amana insha Allah) '''🤜🤛





Page0⃣5⃣


A dandali kuwa ba abun da kake ji sai surutu da
shewar yara suna wasa da
alama suna cikin nishad'i,
yara kamar masu shekarun ma'u, suna a tsakiyar
fili suna ta 'yar gad'ar su maza
Kuma tsaitsaye sai kallon su suke,
wasu daga cikinsu kuma
suna wasan 'yar kara amman da sanda,
can k'arshen fili wa 'yanda
suka tasa masu ma'u ne maza da mata suna ta hira,
Wasu in group wasu kuma
saurayi da budurwa ne suka keb'e suna tasu hirar,
yawancin su duk sun isa aure,
da yawa daga cikin su ma ansa masu rana,
wasu daga cikin mata za'a masu shad'i wasu kuma namiji d'aya ne
ya futo neman su,
yara k'anana kuma suna daga
bayan fage suna ta wasan su irin nasu,
daga
gefe kuma ga masu talla nan
irin su gyad'a ta soyu, aya,
iloka, hanjin ligidi, da dai suransu.

su ma'u na isowa lamunde
ta shige cikin 'yan sa'o'inta suka cigaba da gad'a,
itako ma'u ta lura da
manyan
mata wanda tana shigowa
suka hau harararta, da mata
gatsine, wasu har da buga tsaki,
dama hakan ba bak'on yanayi
bane a gurinta, ba komai
ya jawo hakaba, in banda k'in kulasu da jauro yake
Sai ita, wai wannan y'ar fificiyar yarinyar,
dako k'irgar dangi bata
fara ba.

Su suna matuk'ar san jauro, amman shi bai kulasu,
dan haka ne yasa basa
'yar
ga maciji da ma'u, itako in suna yi halin ko in kula take
nuna masu, ko a jikinta wai
an tsikari kausashiya.

Bata jin wasan yau dan
haka
ta koma can gefe inda suka
saba zama da jauron suyi tad'i
tai zamanta,
tana y'an wak'e-wak'enta cikin
fulanci,
tana kallon wasan da ake gudanarwa a dandalin,
bata
jima da zama ba taji an kulle mata
idanu da hannu ta bayan ta,
ko ba'a gaya mata ba, tasan
mamallakin wannnan hannu,
don haka tasa tafin hannunta, ta kama hannun
ta juyo dashi ta gabanta,
suna
arba da fuskokin juna, kowa
ya sakar ma d'an uwansa lallausan
murmuhi suka zauna suna fuskantar juna,
Jauro yace "cigabarmun da wak'an mana."

Hannu tasa ta rufe  fuskar ta
alamun kunya, haka suka cigaba
da hirar su cikin nuna soyayya
ga junansu, kamar daga sama suka ji wata kak'kausar
murya na fad'in ma'u! ma'u!!
a razane suka d'ago a tare.

Nima d'agowa nai dan inga waye mamallakin wannan rikitacciyar muryar,
da yake shirin shiga hirar masoya,
na d'an razana ganin surar
shi wani guntu kakkaura
mulmulalle ne yana da jajayen
ido wanda suke firgita mai kallon sa,
a take na yanke hukunci yana
Kama da zakious (lol y'an demo ku zaku gane, zakious😂).

Jauro ne yayi k'arfin halin tashi daga inda yake zaune yace "lafiya tanko kake ta wani k'wala kiran sunanta,
ai ko kai ka rad'a mata sai
haka."

Take tanko ya d'aga mashi
hannu, tare da fad'in "ba da kai na ke ba dallah dan
haka ka man shiru," kafin ya
jauro ya b'ud'e baki ya bada
martani, ma'u tayi gatsal tace
" to wai miye ne kake k'wallan kira sai kace wani ubana."

daga ganin yadda tai maganar kasan
tana cike da tsoro da fargaba,
dan ma tana ganin ga jaruminta
Jauro a kusa da ita, tasan in yana nan ba abun da ze iya mata,
dan duk fad'in rugar su da kewaye,
ana tsoran Jauro dan ba k'aramin
jarumi bane, shiyasa ma tun
da ya fito yana son ma'u ba
me shiga gonar shi, don sun
san ba su iya karawa dashi wajen shad'i,
shiyasa
ma duk masu san ma'u  sai
dai ta zame masu kallo daga
nesa dan tafi k'arfin su, shi kuma
Tanko d'an sarkin mafarautan garin ne,
dama
can akwai tsumammiyar d'anyan
ganye tsakanin 'yan gidan su jauro dashi Tankon,
ba wani abu bane ya jawo haka
illa rashin jituwa dake tsakanin
sarkin mafarautan, da baban su
Jauro wanda sana'ar shi ta kasance
fawa.

a sabilin haka ne sam su jauro basa jituwa,
shi tanko kuwa haushin da yake ji wai anfi
kuranta Jauro akan shi a rugar tasu.

Shi kuma ana shi tunanin yafi Jauro
k'arfi kuma dama yana son ma'u,
shine yaga ba abun da yafi
illa shima ya fito a matsayin
manemin ma'u, yadda za suyi
fad'an ga wuk'a ga nama, ma'ana
suyi kare jini biri jini a filin
shad'i, yadda duk wanda yaci
yafi k'arfi kenan, shiyasa ma yazo
tun yanzu dan Jauro yasan
da zaman sa, tun da yasan ma'u bata kai minzalin aure ba.

a take Tanko ya isar da nufinsa,
cikin rashin shakka yace
" ma'u ina sonki kuma duk fad'in rugar nan banga
wanda ya isa yaja dani ba,
A take idon Jauro ya rikid'a ya zama ja ya dunk'ule
hanun shi yana fitar da huci,
itako ma'u dajin maganar da
Tanko yayi a yatsine ta tofar da
miyau tana fad'in " Allah
sitiri buk'ui abun banbarakwai wai namiji
da suna Hajara,
ilahirin mutanen dandalin kuwa
da suka yi masu k'awanya tun lokacin da hargowar
ta fara, mazan cikin su ko,
so suke kawai aba hammata iska suga wa yafi k'arfi a cikinsu, fannin
matan
ko gulmammaki kawai ke tashi,
daga mai cewa wai da me
Ma'u ta fisu ne da har ake fad'a a kanta, wasu ma tafiya
sukayi dan haushi,
Shiko Jauro tak kawai yake jira
Tanko kamar ya sani yace,
"  ko kana da ja" ai be ida rufe baki ba Jauro ya kai mai
naushi a fuska kan kace me
sun kacame dama abun da suke nema kenan suga
ranar da za su b'ud'a suba hammata iska, kowa ya tattara hankalin shi
kan fad'an da ake, ma'u ko
tun tana magana har ta gaji
sai dai kukan da take ta rabza wa.

ilahirin mazan gun sun sha
jinin jikinsu domin sun kasa
raba fad'an sakamakon shakkar da suke masu,
hata yarorin Jauron da na Tankon
sai dai suka zuba na mujiya
suka ja na Akku, masu tsoron cikin su kuwa har sun
fara zamewa, haka aka cigaba da gabza fad'an k'arfi a tsakanin jaruman biyu,
wanda cikinsu duk wanda ya kai duka ma d'ayan
to ba ya yadda a cigaba da fad'a
ba tare da ya ramaba, haka
wuri ya hargitse wasu na kwala
kiran Jauro wasu kuma Tanko,
Mal. Datti ne da gidan shi ke kusa ya fito dan neman
ba'asin wannan hargowar, da isowar sa ya riski
abunda ke gudana, be yi wata-wata
ba ya kira mal. Mudi, dan
ya taimake shi raba wannan
fad'a, da isowar su suka sa
wasu maza su kakkama su,
haka aka kamasu kowa na tirjewa
sanan akace kowa ya tafi gida.

Suko aka tafi dasu gidan mai unguwa
Lamunde ce ta kama ma'u suka nufi gida,
tana k'ara bata baki a hanya
suka had'u da Baffah ya fito
neman ta dan yasan bata saba dad'ewa haka ba.

ganin yanayin ta sai ya k'ara
tsinkewa yace " ma'u lafiya kuwa?"
tace, " lafiya baffah"
take ya k'aryata ta da cewa  " a'a ban yadda ba" ta
k'ara sakin fuska tace " laaa baffah ba fa abun da ya faru dama na ci karo ne da gini shine na bige
kai, yace "wa iya zubillah, Allah
ya sawak'e ya k'ara kare gaba ina lamunden?"
tace
"yanzu had'uwar mu da kai muka rabu da ita"
yace " to mu tafi gida"
ma'u na biye da shi amman xuciyar ta
sai
bugawa take da k'arfi tana
barazanar fasowa, sakamakon abunda ya faru
da kuma k'aryar da ta tsinci
kanta tama baffah dan bata
saba mae k'arya ba, to ta rasa
ya zata ce mai, cewa za tayi
wuri ya hargitse duk dan ita? kuma wai ma ana fad'a ne akan wai ana sonta ita da duka duka ba
ta fi shekara ta tara ba,
ranar ma'u  bacci sama2 tayi
dan cike take da fargabar
me me gari zai zartar.







*QUEEN BK*

ZAN SOKA A HAKATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang