page 16

3.9K 258 0
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨






💎💎💎💎💎💎💎💎 *ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*NA*
_BILKISU ALIYU KANKIA_
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼






🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S📝(( Z.A.W))*
[ ~Gidan zaman lafiya da amana insha Allah~ 🤜 🤛 ]





Ina kike 👀wannan zankad'ed'iyar budurwar san kowa k'in wanda ya rasa matso kusa *RUK'AYYAH AHMAD TIJJANI (RAT)* wannan page d'in naki ne my raty kiyi yadda kike so, Queen bk nayinki a yau da kullum.😘



Page1⃣6⃣






Bakin wani tangamemen gida
motar su ta tsaya, suka fito
suna zuwa bakin gate d'in
mai gadi ganin aunty nafi ce
dan ya santa tunda tana zuwa,
cikin murmushi ya wangale
masu k'ofar dake jikin gate
d'in, tunda suka sauka a mota
ma'u ta zuba ido tana kallon
sarautar Allah, don gida tunda
ga waje abun kallo ne, duk iya dubar ta ba ta hango k'arshen gidan ba,
daga
waje anmai ado da dogayan
bishiyoyin nan da ake k'awata
gaban gidan su, wanda ta lura
yawanci gidajen rukunin suma
suna dashi, kalar fetin gidan
ne ya k'ara fito da gidan, zallar
milk ne da touchings d'in lemon
green, gate d'in ma lemon green ne, wanda haka
hakan ya k'ara haska koraye
shar d'in bishiyoyin da su kai
assembly a zagayen gidan, ma'u
ba ta k'ara tsinkewa ba sai
da cikin gidan ya bayyanar
mata a ganinta, lokacin da mai
gadin ya yaye masu k'ofar
suka shiga, nan ta saki baki kunne goshi a yayinda
k'wayar idanta be gaji da zagaye
ilahirin gidan da kallon mamaki
ba, gaba d'aya k'asan gidan
intrerlocks ne shimfid'e, sannan
ga jerin flowers masu kyau
wanda sukayi ma gidan lamuni,
ga kuma wani d'an gefe daga
can gaba wanda yafi k'awatar da
me kallo an zagaye da
flowers
k'asan wajen kuwa a
shimfide yake da grass carpet
sai flowers d'in dake shuke
launi2 kala2, wanda hakan
ze nishad'antar da mai kallo
sai wani fitinan k'amshi mai
sanyin ni'ima wanda ya dami
gidan kasantuwa furannin
dake shushuke waenda suke
bada d'ad'an k'amshin, ma'u
ta k'awatu da kallon wannan
waje sai lumshe ido take tana
shak'ar k'amshin da yai catching
attention d'inta, tana cike
da
mamakin wannan wai gida ne, in aka barta sai tace
aljannah kawai tazo ( niko nace ta duniya ba)
ta
nutsa cikin tunanin ta ji tai
an jata, aunty nafy ce fad'i take
" tun d'azu ina magana kin mun
kunnan uwar shegu, in kin
hak'ura ai nan zaki zauna,
u have all d tym ki tsaya kina
kallon wannan daga baya"
cikin haushi tai magana dan
k'ufula tun d'azu take ta kiran
ta amman tak'i ansawa, kuma
da farko ma har tayi gaba
sai da ta juya taga bata ga ma'u
ba sai da ta komo baya dan har tasha wata kwana,
ta zo ta iske ta nan tsaye,
daga
yadda tai maganar ma'u ta gane
taji haushi dan haka cikin muryar
tausayi tace " ayyah aunty nafyta kiyi hak'uri kinji"
yadda tai maganar sai taba
aunty nafyn dariya, cikin dariyar
tace
"kece d'in ai sai kace ba'a nan
d'in zaki zauna ba ai sai kin ma
gaji dagani"
itako ma'u a ranta cewa tai
ai inda har kallar wannan ganin
ne baza ta tab'a gajiya da kallon shiba,
haka aunty nafy na jaye
da ita suka fara takawa cikin gidan,
duk da haka ma'u bata bar bawa
idonta hakk'i ba, gidan me fad'in
gaske ne wanda ya bar ma'u
cikin kokwanta anya na mutum
d'aya ne kuwa? a haka suka
iso packing loads d'in gidan,
wanda ya k'unshi ratsatsun
motoci da gani na fad'a, shima wajen ya k'yayatu iya
duban me kallo, komai
na gidan tsabtace yake alamun
suna samun gyara dakulawa sosai, gidan part part
ne, wanda suka fara cin karo
dashi wanda duk yafi sauran
k'ayatuwa, kai daga gane zaka gane
Wannan turakar Mai house
d'in ne gaba d'aya, wato ALHAJI MUHAMMAD ZAYYAN
ta bayan part d'in suka bi nan
suka k'ara cin karo da wasu part
biyu kishiyoyin juna ma'ana
suna kama komai iri d'aya
ne, da ga gani dai zakasan
mata biyu ne a gidan, nan
ma ta bayanshi suka kuma
bi, ma'u ta k'ara hango wani
part can k'arshe madaidaici
shima me kyan gaske, iya dubanta ba ta hango k'arshen
gidan ba dan wata k'ofa ta kuma ganin tsakanin ginin
da yai ma part d'in na k'arshe k'awanya,
dan haka tasan akwai
wani
abu a wajen tunda taga k'ofa, ( to ni dai am curious to know what's in there, muje zuwa).



ZAN SOKA A HAKAWo Geschichten leben. Entdecke jetzt