page 64

6K 300 44
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨








💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*_NA_*
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *_QUEEN BK_* 👸🏼







🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan   zaman  lafiya  da amana    insha    Allah🤜🏻🤛🏻))







_Itz_queenbk @ insta gram._





Page 64



Cikin ikon Allah ƙarfe biyu dai dai su Asmah suka isa garin Katsina sai kallon garin take yana burgeta sosai, gidan wata aminiyar Ummah suka fara zuwa nan sukai sallah suka ci abinci suka ɗan sauke gajiya kana suka nufi gidan Baba Yawale ɗan tsoho mai ran ƙarfe kenan sai dai cike yake da ƙarfi da kwarjini ga dattako da sanin ya kamata da son jama'a, kallo ɗaya zaka mai kasan namijin duniya ne dan ba alamar tsoro ko da wasa a fuskarshi irin su ne basa gudun ko ta kwana, daga gani an sha gwagwarmaya dashi lokacin samartakan shi, hatta aljanu suna sara mai don a tsaye yake ƙyam da ƙafafunshi yanzu haka masu matsala irin ta iskokai ko sammu in suka zo wajenshi tas suke samun waraka da yardar Allah, kuma ko kaɗan ba bokanci yake ba shi da Allah kawai ya dogara iyaka ya ma mutun ruƙiya kuma tas zai rabu da alajanun dan suna tsoron Baba Yawale sosai ya kuma iya karya asiri sosai koman wuyar shi kam, wani abun so tattare da Baba Yawale shine akwai mugun kirki har na keta misali uwa uba riƙo da addinin da yai zam zam da yanzu haka babban malami ne me zaman kansa dan banda ma yaran da yake koyarwa hatta manyan mutane su na zuwa ɗaukar karatun addini wajensa da hikimomi da dabaru kalar na mutanen da, sosai Allah ya zubawa tsohon nan ƙarfi domin ya bama tamanin baya amman yana nan da ƙyar da ƙyar dashi dan zai je inda ransa yake so da ƙafafunshi, gani da jinshi kuwa kullum kamar daɗa ƙaruwa suke.

Gidan shi gida ne ɗan madaidaici dai dai kima na rufin asiri daga shi sai matar shi a ciki dan sai bayan mutuwar mahaifiyar su Muhammad da shekara takwas sannan ya auro ta ana ce mata baba Gaje ba suda ɗa ko ɗaya da baba Gaje amman ƴaƴanshi takwas reras kuma duk Zainabu mahaifiyar Muhammad ce ta haifa masa su kamin rasuwarta, cikin ƴaƴan shi takwas ɗin kuwa shida ke da rai, dan banda Muhammad da ya rasu akwai Fateemah Binta da ta rasu ana goyonta shine haihuwar ƙarshe da Zainabu tayi ta samu mace aka maida mata sunan yayar tata Fateema wannan kenan.





Da fara'arsa ya tarbesu dan yasan da bayanin zuwan nasu dan dama tun ba yau ba Ummah na kai masu ziyara sosai tana gaishesu kuma akwai kyakyawar alaƙa tsakanin Mai martaba da Baba yawale shi yasa yana yawan yo masa aiken alkhairai kala kala, bayan sun gaisa ne ya maida dubanshi ga Asmah yana kara jinjina batun ita ce ɗiyar marigayi Muhammad sosai kuwa yaga yanayinta da baban nata, kuma ba ƙaramin shiga ransa tayi ba da hannu ya yafitota yana faɗin "haba Uwar gida na dawo daga nan mana mu gaisa sosai" ya faɗa yana taɓa tuntun take kusa dashi.



Asmah tai murmushi cike da son kakan nata ta taso dan ita ma lokaci ɗaya da ta ganshi taji tana matuƙar sonshi, a ranta take faɗin Allah sarki wannan ne baban Abbahna.


Zuwa tai gefensa tare da kama hanunsa da yake miƙa mata tace "Baba Yawale barkanku da warka" kamar yadda taji Ummanta ta faɗi sunan domin Baba Yawale kamar general name ɗinsa ne kowa haka yake kiransa har ƴaƴansa kuwa.

Nan ya cigaba da amsa mata yana mata ƴan tambayoyi akan karatunta, dai dai nan baba Gaje ta shigo a karo na biyu bayan fitarta da tayi bayan sun gama gaisawa dasu Ummah, babbar ƙwaryar dake hannunta ta dire gaban Ummah tana faɗin "to ƴata kusha fura kan na kawo maku abinci" sosai Ummah ke son matan dan sam bata da kwaramniya ga kirki kuma kowa nata ne, Ummah tai murmushi tana faɗin "to an gode baba gaje kawai mun ta daku tsaye".

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now