page 43

4K 205 2
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨






💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼








🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )















*WANNAN PAGE ƊIN GABA ƊAYA SADAUKARWA NE GA ZAN SOKA A HAKA FANS GROUP, NAKU NE WANNAN PAGE ƊIN KU KAƊAI, INA SANKU LODI LODI❤😍😎🥰*





Page 4⃣3⃣




*KADA KA RAINA MUTANE KO KANA ƘYAMAR SU DAN WATA NI'IMAR DA AKA YI MAKA, WANDA AKA BASHI ILIMI, MULKI, DUKIYA DA HIKIMA YA GODE WA ALLAH, KA SANI ALLAH YANA SON BAYINSA IN KA TOZARTA KO KA WULAƘANTA SU ZAI SAKA MASU.........*
                          QUEENBK.







Suna fita suka ci karo da Mahmud nan ya ja mimi dan dama ita yake nema, suka isa ɗakin a bakin ƙofa suka tarar da Mustafa don haka Asmah ita kaɗai ta shiga, da sallama ta shiga muryar Abdallah taji ya amsa mata, kafafuwan shi ta hango da yake rabin fuskarta a rufe yake, zaune yake kan gado ƙarasawa tayi bakin  gadon ta aje mug ɗin hannunta akan bedside drower sannan tace " barka da dare ya Abdallah".


Ganin bai amsa mata ba yasa ta cewa "ya Abdallah ga cofee ɗin nan sai da safe" ta faɗa tare da tashi tana tafiya sai dai taji an riƙe mata hannu, jawo ta yayi ta zauna kusa dashi, hannu yasa ya ja hijabin da ta rufe fuska da ita, gani tai ya kafe ta idanu yana ta kallonta, itama tsintar kanta tai da kallonsa tana yaba hallitar da Allah ya zuba mai a fuska, kallon ƙwayar idon juna suke sun daɗe suna aika ma juna saƙonin da baki bai iya furtawa, Asmah ce ta fara yanke kallon, ji tayi Abdallah yace,



"Asmah da gaske wai nan da sati ɗaya zaki zama matata?" ya faɗa yana ƙara ƙoƙorin kallon ƙwayar idanunta, sai dai Asmah ta kauce, ita tambayar ma kunya ta bata.

Ganin tayi shiru ya kara cewa "dagaske kin yadda zaki zama matata?".

"Ay" ta faɗa kanta a ƙasa.

"kenan kina sona ko, kin manta ke kika taɓa cemun sai anyi soyayya ake aure ko, to kuma naji Mahmud yace za'amana aure".


Cikin tausayi ta kalle shi tace "Ay ya Abdallah da gaske ne".

"Wallahi naji daɗi to yanzu muyi soyayyar kafin muyi aure tunda kinga an kusa ko?".

"Ban fahim ceka ba ya Abdallah".

"Ba kince sai anyi soyayya ake aure ba?".

Rasa me zata ce mai tayi can kuma ta tuna wani abu tace "Au ya Abdallah kaga na manta ba haka nake son cewa ba, ina nufin sai anyi aure ake soyayya ka gane".

"Kenan in mukai aure za muyu soyayya?".

Kai ta ɗaga mai, shi kuma ya ɗaga kafaɗa yana murmushi sannan yace "na ƙagara ma muyi auren yadda za muyi soyayyah, amman fa sai kin koya mun dan ban iya ba kinji?"

Abun yaba Asmah dariya, tace "to shikenan ai ba wahala kalmomine ake faɗa".

"Meye kalmomi shine soyayyar?".

"Ya Abdallah bari na tafi kaga dare yayi, kasha cofee ɗinka kafin ya huce".

"A'a kar ki tafi dan Allah ban gaji da ganinki ba".

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now