page 32

3.4K 272 3
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨







💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼








🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )






Page3⃣2⃣


*KIYI RIƘO DA IMANI DA ƘOƘARIN NEMAN ILIMIN ADDINI DA YAWAN IBADA HAKAN ZAI SA KI RAYU CIKIN YARDAR ALLAH.*
                          QUEENBK.






Asmah ce zaune a falon Abdallah bayan ta gama duk abunda take, zaune take a kasa ta rungume gwiwowinta sai ta kwanatar da kanta bisa gwiwowin nata, kallo ɗaya zaka mata ka gane tana tsunduma tsundum cikin duniyar tunani, Abdallah ne ya fito daga ɗaki yazo ya zauna kusa da ita, amman duk batasan da gittayyar mutum a kusa da ita ba, hanun shi ya kaɗa gaban fuskarta amman bata dawo duniyar ba, jingina yayi da bango tare da miƙe ƙafafuwanshi, sannan ya rungume hannayenshi, shiru ne ya wanzu na tsawon daƙiƙu da basu wuce goma ba, Abdallah ne ya fara katse shirun da faɗin

"Asmah ashe ke matata ce?"
.

firgigit Asmah ta farko daga baccin tunanin da tayi sakamakon jin muryar Abdallah da kuma abunda ya faɗa, dan sarai taji komai domin yadda yai maganar da ƙarfi kuma yake futar da harufan ɗai ɗai, cikin in'ina da mamaki tace

"E...e..h..eh ya Abdallah me.....me kace? Ta faɗa tana sakin baki.

Bai amsa mata tambayar ba illa ƙara jefo mata wata da yayi

"To me yasa baki haifa mun yara ba?"

Buɗa ido sosai Asmah tayi tana kallonshi don tama rasa me zatace, tambayoyi sun zo mata bazata kuma ta bai bai, can kuma ta kaɗa kai tare da doɗe kunnuwanta, a cikin ranta take cewa "Asmah baki ji komai ba, eh banji komai ba, koma kinji kimanta kinji" zunbur ta miƙe sai da ta sosa ƙeya kana tace 

"Ya...ya Abdallah, bari inji in kawo maka coffee yau baka sha ba, kuma naga in kasha kafi.." kasa ƙarashe maganarta tayi sai ta washe baki sannan ta juya da niyar tafiya, ji tayi an riƙe mata hannu, a hankali ta juya taga Abdallah ne, da hannu ya jawota ta koma inda take zaune sannan yace

"Baki amsa mun tambayoyi na ba?"

Fizgar hannunta tayi daga riƙon da yayi mata ta gyara zamanta, buɗa baki tayi don tayi magana amman ba abunda ya fito, a ranta take faɗin "lallai ya Abdallah nan dama ya mun waennan tambayoyin ne don na amsa mashi, is he kidding me? Oh my Allah"
girgiza kai tayi, sannan ta juyo yadda tana fuskantarsa kana tace

"Hmmmn ya Abdallah na farko kace NI MATAR KACE KO? to ni ba matar ka bace, ni ni..ni" sai tayi fuska irin alamun tunani can kuma sai tace yauwa "ni mai maka aiki ce, mai aiki kagane mai maka hidima" ta faɗa tare da mai nuni da hannu alamun aiki sannan ta cigaba "kuma kaga maganar yara bata taso ba tunda ni ba matar ka bace"

Tun kan ta ida rufe baki ya fara magana

"MAI AIKI? MAI HIDIMA?" ya faɗa kamar yana lissafin wani abu can kuma yace "yeees, ai Ammie tace mun wacce zatana mun aiki da hidima kuma tana biya mun ko wace buƙata tawa itace matata, kuma aike kina mun aiki ko? Infact yanzu ma kika gama faɗa ko?"

Iska ta zuƙa a bakinta sanan ta furzar da ita tana fitar da sautin "hashhhhh" yanzu kenan duk bayanin da tayi mai be ma gane inda ta dosa ba kenan, to yanzu tama rasa yadda zata mai bayani, hanayenta duka biyu tasa ta kama goshinta tana ɗan murzawa kaɗan kaɗan, can kuma ta juyo cikin ƙarfin gwiwa da tuna abunda zatace ta fahimtar dashi tace

ZAN SOKA A HAKADonde viven las historias. Descúbrelo ahora