page 36

3.4K 282 29
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨







💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼









🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )










Page3⃣6⃣






*IN AN KAWO MAKI LABARI KADA KIYI FARAT KI MUSANTA, KI SAURARA ALAMAR CIKAR HANAKALI NE, TABBAS BA KOWACCE MAGANA AKE ƘARYATAWA BA, ZAI YU KASAMU MAFITA CIKIN MAGANAR DA AKE KAWO MAKA....*
                          QUEENBK.



"Sati ukkun da suka wuce muna ta nemar ma Abdallah mata, sakamakon ciwonshi sabidda ya samu mai kula dashi sosai, kuma babban maƙasudin da yasa muka tsananta binciken kuma muke so ayi komai da sauri a gama shine, doctor ya shaida mana in dai yayi aure ciwon cikin shi zai daina, saboda matar shi ita kaɗai ce maganin ciwon cikin da yake ta fama dashi ƴan kwanakin nan, to har yanzu dai muna kan nema mashi mata sai jiya kwastam muna zaune da Abdallah sai ya gaya mun matar shi da kansa" nan Ammie ta labarta ma Asmah yadda sukai da Abdallan, sannan ta cigaba "da muka tattauna batun da Abbansu, sai muka ga ay lallai ke yafi dacewa kizamo *MATAR* *ABDALLAH* saboda ba wacce tasan Abdallah kamar yadda ke ki ka sani shi, infact ba abunda baki sani game dashi ba, abuda yake so wanda baya so, cimar shi, har kullum kuma halayar sa ciki da bai, dama kin saba da bashi maganinshi kinsansu, kuma gashi Abdallah duk faɗin gidan nan ko nace duk faɗin duniyar nan ba wanda ya yarda dashi sama dake, cike kuwa hadda mu mahaifansa, dalilin faɗar hakan, kinga na ɗaya duk faɗin gidan nan ba wanda ya isa ya ba Abdallah magani, abinci, ruwa ya amsa in ba keba, ruwan wanka sai inke kika haɗa yake yadda yayi, haka ke kesashi sallah, har kaya sai kin zaɓa mashi yake sawa, koda ko ciwonshi ne ya tashi ke kaɗai zaki iya yi mai waennan abubuwan, shi yasa muka ga ba wace ta dace ta zama *matar* *Abdallah* in ba ke ba Asmah, infact ma ba za mu iya samun matar da zata dace ba irinki, shine mukai tunanin me zai hana mu haɗa ku aure  da ke da Abdallah"







Asmah kam da tunda Ammie ta fara maganarta ta nemi natsuwarta ta rasa, Ammie ta lura da hakan kuma bata kawo komai ba tunda tasan ita Asmah ba zatai zaton za'a kawo mata maganar ba, Ammie ta gyara murya ta cigaba












"Nasan zakiyi tunanin me yasa muka ce ki auri Abdallah bayan munsan ɗan mu baya da lafiya, shiyasa nake so inyi making abunda zan faɗa yanzu clear, kar ki taɓa cewa *ZAKI SO* abdallah *A HAKA* n da yake sabidda mun taimake ki baki da zaɓin da ya wuce ki aure ɗan mu da baya da lafiya ba, in zaki so shi ki soshi dan Allah, kuma kar kiji ɗar wajen faɗa mana ba zaki iya auren Abdallah ba, in kuma kina da wanda kike so to ki fiddo dashi za mu maku aure dashi, domin wallahi kamar ɗiyar cikin mu muka ɗaukeki hakan kuma bazai canja ba dan wani ƙuɗiri na son zuciyarmu, abu na ƙarshe kuma banson ki amsa mun maganata yanzu ina so kiyi nazari akai kiyi istikhara kuma, daga baya sai ki amsa mun ko mai kika yanke ki sanar mun kai tsaye" Ammie na kai dai dai nan a maganarta ta tashi da sauri ta fita tun kafin Asmah ta samu damar magana, a tinaninta ya kamata abar ta ita kaɗai domin tayi tunani ta kumayi shawara da zuciyarta.









Asmah kam jin kanta tayi ya mata nauyi a bisa wuyanta, duk ta rasa ma mafarki take yi ko a zahiri ne abubuwan ke faruwa ohon mata, ta ɗauki wajen kimani minti goma kafin ta iya tattato hankalinta waje guda, haƙoranta tasa ta cija ƙasan leɓenta ta ciki, jin zafi yasa tasan ba mafarki take ba illah zahirin rayuwa da ke faruwa, da ƙyar ta iya buɗa bakinta tace


ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now