page 3

5.2K 369 5
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨






💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*NA*
BILKISU ALIYU KANKIA
*((QUEEN BK))*




🚩ZAMAN AMANA WRITTER'S ((Z.A.W)) ASSOCIATION  ((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah))


page0⃣3⃣

Tana laxumi taji gwoggo na kwala mata kira, duk tabi tacika gidan da kwakwazon sunanta, ta firgita ainun aranta tace " to me faruwar ta faru, nasan be wuce komai in ba maganar tuwon jiya ba"
Ta tashi ta linke hijabinta ta isa gun gwggo, tun kan
ta isa gwggo ta rarumo wuyanta
tana fadin
" ubanwaye yace kici tuwon nan ma'u"
ma'u kuwa sanin shukar da tayi, sae ta nuna batasan kwanan zancen ba,
ta tab'e fuska tace

" wane tuwo kuma na ci miki gwggo?"

da hannu tayi mata nuni da inda akayi kaca kaca da tuwo da miya na gutsitsiran tuwon a k'asa,
a take tace,

" ayyah gwoggo ni tunda na kwanta ma ban tashi ba sae lokacin da naji saukar ruwan sanyi, ko kinji motsina da daddare ne?"

tayi caraf tace " ay naji"

Ma'u tace " to ko da ganin aikin nan na mage ne, yanxu haka mazurun gidan malam bala ne,dan kin san yana shigowa ya mana b'anna"

gwggo tace to ya akayi ya bud'e k'ofar?
ma'u tace, "kai gwggo bafa ki kulle k'ofar ba don ko kafin in shiga d'aki
na hango k'ofar rabi a b'ud'e, su gwggo da rud'u"

gwggo ko an zura ta kwalba, ba ta gane k'arya bane,
ta saki wuyan ma'u tana fadin

"ubale ne me rud'un bani ba shegiya kawai, kuma in dae haka ne sae naje, har gidan malam balan in baxa su rik'a rufe magen su da dare ba to ko har gaban mae gari sae naje,
ina dalili ina d'an mafari"

Ita
ko ma'u tashi tayi taje ta fara y'an aikace aikacen ta data saba kullum, dama tun
asuba in ta tashi ba ta komawa bacci, zata gama
duk wani abun da tasan tanayi don kar tayi latti a islamiyya kuma tasa lamunde latti,
dan ko duk lattin da ma'un zatayi sae ta jira ta sae dae susha dukan tare,
haka suka saba tun suna k'anana, amman duk da asubancin da ma'un keyi wajen ganin ta gama da wuri dan kauce m lattin ammn gwggo sae ta k'ak'alo
wani abun da zae sata lattin, sauk'in ta d'aya in baffah na nan.

Ma'u ko tashi tayi ta barta anan tana ta banbaminta a ranta tace
" kyaji dashi ciwon ajali a d'an yatsa"

d'akinta ta koma y'ar lotsatsiyar katifarta ta  karkad'e sanan ta shimfid'a labulen da take shimfid'awa
a kai, sannan ta karkad'e tabarmar tsakiyan dakin wadda duk ta zare, kuma ya kasance ita kadae ce
shimfid'ar k'asan dakin,
Sai
y'ar bakkon da take sa kayan ta wanda ba su fice kala biyar ba,
suma duk yan tsunmokarae ne yawancinsu duk sun d'age mata,

ta share tas, duk da kasancewar haka dakin ya ke a talauce
amman baza ka tab'a cewa
kaga datti ko d'aya ba don ma'u akwai tsabta ta azo
a gani, bayan tagama da dakinta ta nufi kicin dinsu
ta gyara tsab sannan ta fitar da wanke wankensu magudada,
ta isa garken shanunsu da
yake bayan gidan ta shareshi,
sharar garken baze mata wuya ba dan kullum tana share shi
ta canja ma shanun ruwan shansu, ta koma d'an
tsakar gidan su wanda be wuce girman d'aki biyu
ba ta share shima, sannan ta soma yin wanke2 bayan tagama ta mayar kicin, ta share magudadar ta wanke masu bayin su k'al,

minti 40 ya dauketa dukkan waennan aikace2n, kasancewar ta yarinya mai kaxar2,

sam batada san jiki irin na yara, hadda had'in ta saba tun tashinta.
Tulu biyu ta dauka ta nufi rafi tun gari bae ida wayewa ba,
rafin babba ne, tana isa tai can gefe inda ake d'ib'ar ruwa
kasancewar d'ayan gefen masu hawa kwale2 ne suna ta aikin kae komo,
bata iske lamunde ba sae a sawunta na biyu,
sawu
uku tayi duk ta cika masu inda suke adana ruwan nasu.

Ta iza ma gwggo wuta ta d'ora mata ruwan kokon saeda wanda take,

tacika wata k'atuwar buta tayo wanka duk da ba sabulu,
ta fito cikin uniform d'inta
mai ruwan sararin samaniya
(sky blue), gaskiya kalar ta haska ta riga da wando ne sai hijabi iya gwiwa,
da y'ar jakar buhunta a hannu ta zira slippers dinta, so take
tayi sad'af2 tafita don inhar gwggo ta fuskanci zata fita da wuri haka, sae ta sata wani abun dan
tayi latti don haka tacira hijabin nata
ta b'oye ta, ta nufi bayi da zummar zata shiga bayi ne sae ta zille, sae dae
me? ta kusa fita kawai sae ga gwoggo ta fito daga madafar tasu tagama
dama koko kenan, tace yauwa ma'u zo ki sayo mun siga shagon saidu,
ma'u ko kamar ta fasa ihu dan haushi, bayacce ta
iya dole ta k'arasa tana zumb'ure2 takarb'a d'arin da gwggo ke mik'a mata,
ta fito amman sae tayi zaune a dakalin da ke waje,
zuciyar ta sae tafasa take tana ta tunanin irin hali na gwoggo,

take mafarkinta yafad'o mata rae, tana yawan yin irinsa amman bata tab'a gaya wa kowa ba har ko lamunde,
muryar shi kawai take iya tunawa,
danbata ganin fuskar shi.

Nan ta tashi ta rasa ina ma zata bi, gaskiy in tace zata shagon sa'idu to za su yi muguwar makara dan tasan lamunde na can na jiranta,
wata zuciyar tace " ki tafiyar ki makranta in kin dawo kice mata kin manta"
take ta k'aryata zuciyar tuno wahalan da tasha jiya,
Tasan in ta aikata hakan linki ba linkinta gwggo xata mata koda ko a gaban baffah ne, zata fake da ta aiketa suyo sukari bata siyo ba, gashi anata xuwa sayan koko amman ba suga.

tashin da zatae kamar hadin
baki taga jalo dan mak'obcinsu, yaro d'an kimanin shekara 7 yazo wucewa
da bokiti akansa da alama
markad'e zaya, tace yauwa Allah na, ta kwala mashi kira yaro ko yatsaya, ta k'arasa inda yake,
" jalo nik'a zaka?"
yace "ayy"

tace "yauwa karb'i wannan dan Allah in ka aje markad'en ka biya shagon sa'idu ka suyo sukarin duka,
in ka dawo kashiga ka kai ma gwggo kace mata bakin  kofar gida na ganka nace kashiga ka kai mata kaji"

yaro ya d'aga kai, duk dan yaji dad'in aiken
hadda cemashi anjima in ta dawo yaxo xata bashi naira biyar, yaji dad'i sosai ya tafi.

Ita ko ta isa bakin rafi da sauri ta taradda lamunde na jiran ta daman anan take jiran ta,
Lamunde na ganin ta, ta yak'e baki tana fadin

" ma'u yau da wuri haka, kice mallan yau sae yayi sadaka"

ma'u tace"aikodae! maxa mu tafi"

suna zuwa ko suka iske me kawle2n, da suka saba hawa yana dawowa,
yana isowa gab'a suka haye lamunde ta mik'a ashirin dinta, mai kwale2
yace
saura ke ma'u  dan kinsan kudin ki ya k'are tun wancan satin.

Dama baffah yana biya mata na sati ne tunda shi baya fiye xama bane.

Tace ya huk'uri habu insha Allah inaga yau baffa zae dawo zan gaya masa yaxo ya biya.

Habu yace "to shikenan" don
yasan baffan nata na biyan sa kud'in nasa.

Ya kai su har d'ayar gab'ar sanna suka sauka
suka
dab'a a jirgin sayada, suna
tafiya suna bitar haddar su,
sun isa da wuri kowa yayi mamakin hakan, y'an ajin su sae
kalansu ake, ya mu'allim ko ranar baki har kunne dan
yana san suruk'a zuwa da wuri
dan sunfi kowa haxak'a a ajin,
barin ma ma'u shi yasa take birge shi.





A /N

I SEND A GOOD PRAYER TO ALL MY GOOD READERS, WITH A GOOD MIND, FOR A GOOD REASON, AT A GOOD TIME, ON A GOOD DAY.

*JUMA'AT MABRUK 2 U ALL.*

❤ TNX 4 D SUPPORT DUDES.

*QUEEN BK*

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now