page 49

4K 211 1
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨






💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼








🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )



















Page4⃣9⃣

*KA NISANCI DABI'AR ROWA DA MATSIN HANNU DA TAƘAMA DAN ZASU JAWO FUSHIN ALLAH AKAN KA DA SHAFEWAR ALBARKA GA RAYUWARKA, SANNAN ALLAH ZAI SA MUTANE ZASU TSANE KA, KUMA TSATSONKA SUYI GADON ƘI, KUMA ZA'ANA MA MUMMUNA SHAIDA DA AMBATO KO KANA RAYE KO BAYAN KA MUTU, DA YAWA MASU NAUYIN HANNU DA RASHIN SAKA ALHERI BASA YIN KYAKYAWAR ƘARSHE......*
                          QUEENBK.





Mimi tazo sun sha surutunsu tare da yaushe gamo, sai da akai la'asar sannan suka tafi.

Abdallah ya dawo can yamma lis, dama Asmah na falo duk ta ƙagara ya dawo dan bai taɓa daɗewa ba kallar na yau, tana jin bugun ƙofar shi da sauri ta buɗe, jawo ta yayi yana faɗin "babyna nayi missing ɗinki".

Ita ma rike shi tayi tace "Nafi missing ɗinka ina kaje ka daɗe?".

"Ai munje kasuwa da Abbah ne, Abbah ya nunna mun shaguna na da yawa kalla ma abunda na siyo maki" ya faɗa yana fiddo wani abu daga aljihunshi, Asmah ta bishi da idanu wani ƙaramin case ne, buɗe mata yayi yana juya mata dan ta gani, wani zobe haɗaɗɗe simple ta gani bata taɓa ganin zoben da ya birgeta kallar shi ba, hannun ta ta wurga a kafaɗar shi ta rungume shi tana faɗin,


"Wow baby na wallahi zoben ya haɗu ina son shi sosai na gode" ta faɗa tana bashi peck a kumatunsa.

Hannunta ya kamo dan yasa mata sai yaga wannan zoben da Aliyu ya bata tuni ya ɗaure fuska, ita sai yanzu ma ta tuna zoben na hannunta da sauri ta fara ƙoƙarin cirewa yadda taga Abdallah na kumbura, fisgo hannun yayi ya cire zoben ya wurga shi a bango yana huci har zai juya ya tafi Asmah ta riƙo shi ganin ya bata rai sosai tace,

"Haba babyna kar ka juya mun baya dan Allah ba zan iya tolerating ba, ka gafarceni kuskure na ne" ta faɗa tana mamakin ko ya akai Abdallah yasan namijine ya bata zoben.



Ganin bai juyo ba yasa cikin kamar muryar kuka tace "dan Allah babyna ka yafe mun kaji, ina sonka" ta faɗa tana rungumo shi ta baya, kamar bazai kula taba kuma sai taji ya juyo da ita ya rungumeta yana shafa mata kai.


Cewa tayi "babyna ka yafe mun?".

Hannunta ya jawo yasa mata zoben yayi kissing hannun, tace "na gode sosai".



*WASHE GARI*

Tunda sassafe Asmah ta shirya Abdallah ita ma ta shirya ta jashi suka tafi, falon Abbah suka fara zuwa nan suka taras da Ammie, nan suka zauna suka gaishe su, bayan sun gama gaggaisawa, Ammie ta miƙo ma Asmah wata takadda tace gashi, Asmah ta amsa check ne ta gani na dubu ɗari biyar.

Cewa tai "Ammie na gani check ne".

"Ay Asmah naki ne, kuɗin sadakin kine".

"Amman Ammie duk wannan kuɗin sadakina ne ai sunyi yawa".

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now