page 66

5.3K 328 75
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨



💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*_NA_*
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *_QUEEN BK_* 👸🏼



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan   zaman  lafiya  da amana    insha    Allah🤜🏻🤛🏻))





_Itz_queenbk @ insta gram_









PAGE  66



Ba inda ta zame sai folder da zata ga duk abunda camera recoder dinter yai mata recording amman sam bata ga new record ba abun ya bata mamaki nan ta shiga neme neme sam bata gano ba komawa tayi main recoder dan ta hasko mata ɗakin Auntyn yara yanzu amman sam yaƙi in banda blank bata ganin komai sai  ma cemata da computer keyi "you have'nt set your camera recoder yet" wani mummunan faɗuwar gaba taji ji take kamar ta kwarma ihu dan haushi da takaicin da ya addabi zuciyarta tunani take to me ya faru ne bayan tafiyarta? ko Auntyn yara ta gano ta cire ne ita ma ta wayance a zuwan bata san komai ba? kai a'a ko tagani ma bazata gane komeye ba kuma bazata san ni na saka ba to ko abun ya faɗi ba wanda yasan meye may be aka share dan in ba mutun yasan meye ba gani ɗaya baze gane meye ba da kuma amfaninshi ba, to ya ya akai ne? haka ta rinƙa jero ma kanta tambayoyi ta kuma rasa mai amsa mata, hannu ta ɗora akai tace "ohh ni Asmah yau naga ta kaina me ke shirin faruwa damu ne ya Allah ka kawo mana agajin gaggawa cikin wannan lamarin" ganin damuwar tana neman yi mata yawa da sauri ta faɗa bayi ta ɗauro alwalla tazo ta shiga kai kukanta wajen rabbil samawat a haka har bacci ya sureta akan daddumarta.


_WASHEGARI..._

Misalin ƙarfe 10 Asmah ce a falonta sai zagaye take ta saƙa wancan ta warware duk lissafinta a jagule yake ta rasa gano mafita sam so kawai take taje har ɗakin Auntyn yara ta gano me ke faruwa sai dai wani ɓangaren na zuciyarta nata gargaɗar ta akan haka, Abdallah ne ya leƙo da fuskarshi daga bedroom ɗinsu fuska cike da annuri yace "beauty kizo Habibty na kiranki" sannan ya koma, binshi kawai tai tana tunanin ta ina Umman ke kiranta tana shiga ɗakin taga ya tasa laptop ɗinshi gaba yana ta surutu yana ƙyalƙyace dariya ƙarasawa tayi kusa dashi ta zauna tana kallon screen ɗin ta hango Ummanta a cike zaune take tana cin abinci nan ta gano ashe vidio call ne, da sauri ta saita fuskarta tace "ayyah Ummana ina kwana ya makaranta ya karatu yasu Aunty Sarah?" (Aunty Sarrah cousin dinsu Ummah ne dan ƴace ga shaƙiƙiyar ƙanwar Naty itace wacce Ummah ke zaune wajenta tana karatunta).

"Lafiya ƙalau ɗiyata ya na barku".

Muryarta na rawa tace "lafiya lau Ummah alhamdulillah".

"Ya naganki haka Asmah kamar kina da wata damuwa" da sauri zuciyar Asmah ta shiga bugawa ji take kamar ta faɗi abunda ranta keso faɗa a dai dai wannan lokaci kamar ta fasa ma Ummanta ƙwan ta fallasa Auntyn yara, kamar ta faɗa mata duk abunda ya faru har kawowa yanzu sai dai kash ta kasa dan ba tun yau ba tun lokacin a Mai duguri sai tazo tana san ta faɗa ma Ummah duk abunda ke faruwa sai ta kasa ta rasa dalili yanzun ma hakan ce ta faru cewa tayi "ba komai Ummah bacci ne nakeji".

"To kije kiyi baccin an jima zan kiraku dan yanzu ina da lectures zan wuce makaranta ne".

"To Ummah Allah ya bada sa'a" nan Abdallah ya ɗauke da "Habibty Allah ya bada sa'a sai kin dawo".

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now