page 33

4K 237 0
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨






💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼








🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )






Page3⃣3⃣




*KAFIN KIYI RUBUTU KIYI NAZARI AKAI, KUMA KAFIN KIYI MAGANA KIYI TUNANI AKAI, YIN TUNANI ZAI RABA KI DA YIN ABIN DANA SANI A RAYUWA.*
                          QUEENBK.








Misalin ƙarfe 2:30pm zarah tazo gidan, tuni dama ta daɗe tana zuwa, bayan ta gaishe da Ammie dake falo, Ammie tace "kai kaji zarah sai kace baƙuwa ki wuce ciki mana suna ɗaki" ƴar dariya tai tace "to ammie".

Tashi tai ta wuce ɗakinsu mimi, mimi na zaune kan gado tana rubutu a littafinta, ita kuma Asmah na ƙasa tana cin ɗan wake, jefi jefi suna ƴar hirar su, zara ta turo ƙofa a hankali batai sallama ba saboda so take tayi suprising ɗinsu, tana leƙo kai da Mimi suka fara haɗa ido, Mimi har ta buɗa baki zatai magana zarah tai sauri tai mata alamun tai shiru da hannunta, ɗaga mata kai mimi tai tana murmushi, ita ko Asmah ba tasan meke wakana ba da yake ta juya ma ƙofar baya ne, ga ɗan wakenta yana kai mata karo, a hankali Zarah ta tako har inda take, tana zuwa ta daidaici bayan Asmah ta ɗaka mata duka.




Asmah ta saki wata ƙara tana dafe gurin, juyowa tayi tana kukan shagwaba ganin Zarah ce me wannan aikin, gaɓa ɗaya Zarah da Mimi suka sa dariya.




Asmah tace "Amman Allah sai ya bimun haƙƙi na wallahi, haka kawai dan mugunta ki wani dake ni, bayan na gaya maki banson duka, yanzu da kinsa na shaƙe fa kinga abinci nake ci ko, wai ke Zarah duk na kusa dake ne sai yasha wahalar wannan hannun naki mai shegen zafi, nikam ina tausaya ma mijinki"

Nan ma suka ƙara sa dariya,
Kana Zarah tace "kar ki tausaya mashi, shi ba zai ji komai ba duk cikin so ne ai"

Asmah ta cigaba " wannan matsalar kuce, ni dai bashi kika ci zan rama ne yarinya" sannan tayi ƙwafa ta haɗe rai ta cigaba da jefa ɗan wakenta.


Zarah ta zauna gefan gado ta cire gyalanta ta
aje jakar ta kana tace " ya haƙuri Asmah dan Allah, bansan zaiyi zafi sosai ba" ta faɗa tare da zaro halshe tana mata gwalo.


"Ba wani in banda iskanci kinsan da ƙarfi kika mun sannan ki wani ce baki son zai yi zafi ba ko? Rashin mutunci kawai"

"To ya haƙuri dan Allah, na tuba bazan kuma ba kinji?"
Mimi ma tace "ya haƙuri Asmah duk cikin wasa ne tunda kuma ta baki hakuri au shikenan"


Asmah tace "ai wannan bata son wasa ba, yanzu na mata haƙuri anjima karawa zatai a makaranta fa kullum sai tasa kafaɗata ciwo tsabar duka"
dariya Mimi tayi, Zarah kam hannu tasa ta kama kunnuwanta alamun ban haƙuri duk da tasan sarai Asmah cikin wasa take, can tace nasan yadda zan yi maki a ranta a fili kuma tace

"To Mimi ni bara na tashi na tafi dama ya Aliyu ne ya aiko ni, to naga wacce aka aikenin gunta she's not in the mood, so i better go" ta faɗa tare da ɗaukar gyalanta tana tashi, da sauri Asmah tasa hannu ta jawo ta inda take zaune tace

"Ina zaki dan Allah, dawo ƙawar arziƙi na yafe maida wuƙar plz"
gaba ɗaya suka sa dariya.


Zarah tace "hahahaah dama nasan lagonki"
Asmah ta ɗaka mata duka a cinya tare da faɗin "ba kare bin damo na rama, kinga anyi 1 1 kenan"
Zarah cikin ihun zafi tace "Amman Asmah naki yafi zafi"
Asmah tace "Ramuwar gayya ai tafi ta gayya zafi"
Mimi tai dariya.



ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now