page 60

4.1K 254 14
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨






💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*_NA_*
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *_QUEEN BK_* 👸🏼






🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan   zaman  lafiya  da amana    insha    Allah🤜🏻🤛🏻))




















*PAGE 60







*_A hankali ta fara buɗe manyan idanunta tana lumshe su sanadin haske daya gaurayen ilahirin ɗakin, ba abunda ya doke kunnuwanta sai sanyayyan kaɗe-kaɗe na busa, sarewa da algaita irin dai wanda ake yi a gidajen sarautar nan in ana wani gagarumin biki, taro, naɗi ko sha'ani a hankali kiɗan ke tashi yana sauka a kunnuwanta ita ko daɗin kiɗan yasa tana ta lumshe idanu tana ƙara nannaɗe jikinta tana ƙudundunewa kan filonta, wata ni'imantacciyar iska ce ta huro tabi dukan ilahirin jikinta ba abunda hancinta ke iya shinshino mata sai ƙamshin soye-soye da dafe-dafe, ida buɗe idanunta tayi ras akan muhallin da take ciki bayan ta gama karaɗe ɗakin da kallo take komai ya dawo mata a ƙwaƙwalwarta take farinciki ya lulluɓeta ba abunda zuciyarta ke gaya mata sai "Asmah yau zaki ga Ummanki".


Dubanta ta kai kan
agogon dake manne a bangon ɗakin ganin ƙarfe 7 har da rabi yasata saurin tashi tana miƙa haɗe da salati, ahankali ta jiyo hayaniyar jama'a daga waje suna ta hada-hada da raha murmushi tayi tana ƙara gode ma Allahn da ya raya ta har i zuwa yau ranar da take tunanin bata da mafiyiyarta, ranar da zata shiga cikin tarihin rayuwarta har ta gushe kuma bazata manta da ita ba, tsintar kanta tayi da dariya tana faɗin "oh my Allah am so grateful today i gocca see my momma, Allah na gode maka da wannan ni'ima haƙiƙa kai kaɗai kake bakada abokin tarayya, ya Allah na roƙe ka ka kawo mun Ummata cikin ƙoshi lafiya gareni".


Ji tai ance "ameen", dubanta takai ga Mimi dake kwance gefenta tana ƙara luntsumewa cikin filonta tare da ƙudundunewa da alama baccin na mata daɗi, Asmah tayi murmushi tana shafa kan Miemie tare da cewa "morning dearie".

Miemie tace "uhn uhm" tare da juyawa tana ƙara gyara kwanciyarta alamun ta ƙyaleta baccin bai isheta ba, dariya tai tana faɗin "zama ki tashi da hujja ne bari dai su Minal su taso daga nasu baccin" ta faɗa tana dariyar mugunta, ta zuro ƙafafuwanta da niyar tashi taji an turo ƙofa Naty ce ta shigo cikin shirinta da alama har tayi wanka dan sanye take da wata dalleliyar super ɗinkin riga da zani sai ta cora kallabinta irin dai ɗaurin tsofaffin nan murmushi ta sakar ma Asmah cikin zolaya tace "Allah ya maku gyaɗar dogo dan da na iske baku tashi ba da yaran naku zan turo su tashe munku kun kuma san sauran" Asmah tayi dariya, nan Naty ta kai dubanta ga gado ta hango Miemie nannaɗe tace "ashe hamshaƙiyar nan na nan tana baje kolin baccinta ai ban lura ba, maza tashi tashi ƴan a kwana a hantse ko?" ta faɗa tana buga ƙafafun Miemie ita ko ba abunda take sai ƙara maƙale filonta tana faɗin "haba Naty bari in ƙara ko na minti ɗaya ne" Naty tace "nasan maganinki" itako Asmah ba abunda take inba dariya ba, nan ta shiga gayar da Naty bayan sun gaisa ne itama cikin zolaya da yaba shigar Natyn tace "nima dai bari na tashi na ɗau wanka kar kishiyata ta fini kyau".

"Ah to da kin dai zauna na ƙwace fadar na barki a zaure" suka yi dariya.

Naty na fita kamar haɗin baki sai ga yaran nan sun shigo buya guda cike da surutu suka haɗa baki wajen faɗin "Aunty Asmah ina kwana" ta buɗe hannu tana rungume su tare da shafa masu kai tace "lafiya lau boibies ɗina kun tashi lafiya".

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now