page 50

4.3K 228 9
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨






💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼








🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )

















Page5⃣0⃣











Muryar Auntyn yara taji ta ƙara faɗin,

"Ai nifa ban yadda da bokannan ba, yace in suka ci sau ɗaya Abdallah sai yaji ya tsane Asmah ita ma haka, yadda ba abunda zai shiga tsakanin su balle a samu tsatson Abdallah, to ni dai sati nai ina zuba masu a abinci, amman ni ban ga sauyi daga yadda suke ba sam, in ma banda sabuwar shaƙuwa da suke ƙarawa, kwata kwata ma bai son yayi nisa da ita fa, dan ma na samu Abbansu cikin dabara nace ya riƙa tafiya da Abdallah kasuwa yana nunnu mai harkar kasuwanci ko zai fahimta, to shine ma fa suke ɗan rabuwa shi ɗinma da ƙyar Abbah ya shawo kanshi ya yadda zaina binsa".


Tai shiru jim kaɗan can kuma tace "haba Jummai na tabbatar sunci abincin nan, sai dai akwai ranar dana hango Asmah tana juye ma Uwar talle abinci a roba, ko da na tambaye uwar talle ce mun tayi kingi ne Asmah ta bata tace ta raba ma almajirai a hanya, shine na tambaye ta ko ta taɓa bata tace yau ne kawai tabata, ke na tabbata sunci abincin nan fa kullum sai na zuba shi kuma ita Asmah ba girki take yi ba balle ince ta girka ance ta huta na sati, kuma ai baza su zauna da yunwa ba ko?".


Can ta ƙara cewa "in ma wannan aikin bai ci ba, zamu koma wajen boka ne kawai ya bamu wanda za'a lalata mahaifar Asmah gaba ɗaya yadda baza ta taɓa haihuwa ba, in kuma har ta samu ciki to tabbas kawai mu kashe Abdallah da ita da abunda ke cikin nata *duk mukashesu*".

Wannan kalmar ta rinƙa yawo a ƙwaƙwalwar Asmah dake tsaya, amman bata jin kanta kamar mutum mutumin ta ce ke tsaya kwata kwata ta rasa mafarki take ko a zahiri take jin wannan mugunta da zaluncin da za'ayi masu su bayin Allah da basu san komai ba, leɓenta ta ciza taji zafi nan tasan tabbas a farke take, zahiri take ji ba mafarki take ba.



Can ta ƙara jiyo muryar na faɗin "ba wata matsala Jummai ai dane nake jin tsoro matsawar haka ta faru kawai *a kashe su*".


Asmah bata san sadda ta saki tray ɗin alabasa ba, ya faɗi yana sakin ƙara, muryar taji ana faɗin "waye nan!".


Da sauri Asmah ta duƙe tana toshe bakinta da ƙarfi kar kukan da yake ƙoƙarin kwace mata ya tona ta ji tai an maimaita, da sauri zuciyarta tace mata "duk abunda za kiyi kar ki yadda ta kama ki anan".


Hannu tasa tana kwashe alabasar da ta zubar da sauri sai da tabbatar ta kwashe komai ta ɗauki tray ɗin da sauri ta wuce part ɗinta Allah yaso cikin duhu ne ila da sai Auntyn yara ta ganta, tana shiga ta aje tray ɗin albasar ta kulle ƙofar ta jingina da ƙofar ta zame a hankali ta zauna tana maida numfashi, ji tai ana buga ƙofar sai da gabanta ya yanke ya faɗi, da sauri ta tura tray ɗin albasar ƙarƙashin kujera ta share hawayenta saɗaf saɗaf tayi ɗaki, sai da taji an ƙara buga kofar ta fito a hankali tana miƙa tana hamma kamar mai bacci tace "gani nan zuwa".


Buɗa ƙofar tai tana hamma, da sauri kuma tace "ahhh Auntyn yara sannun da zuwa ashe kune".

Auntyn yara ta kutso kai ciki tana faɗin "yanzu kika shigo?".

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now