page 67

3.1K 234 24
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨


💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*_NA_*
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *_QUEEN BK_* 👸🏼


🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan   zaman  lafiya  da amana    insha    Allah🤜🏻🤛🏻))




_Itz_queenbk @ insta gram_









__STAY AWAY FROM HURTING OTHERS,  THE HURT YOU CAUSED AND THE PAIN IS INFLICTED AND WILL COME BACK TO HARM YOU IN A DIFFERENT WAY......._
             *QUEEN BK*











PAGE6⃣7⃣











Mamaki ne ya kama Asmah jin muryar namiji ce ke sallamar dan ba kasafai take bak'i maza ba Abdallah ma ba wai ya cika kawo mata abokanshi bane kuma ko da bakʼi maza yʼan uwa sun sun zo sai dai a kirata b'angaren Ammie ko Abbah.




Kashe gas d'in tayi kasancewar ta kammala girkin, ta coridor d'in da zai sada ta da d'akinta tabi ta yadda wanda ke falo bazai ga gintanyar mutum ba, mayafi ta d'auko ta yafa sannan ta wuce falo, Abdallah ne da Mahmud zaune Abdallah rik'e da remote a hannunshi yana so ya kamo masu tashar k'wallo dan wani match zasu kallah shi kuma Mahmud ya dage yana ta bashi dariya yana ta k'yak'yatawa.



Da fara'a a fuskarta ta shigo da Abdallah suka fara had'a ido da sauri Abdallah ya had'e dariyar shi tare da shan kunu yana kawar da kanshi daga gareta, tas akan idon Mahmud bin Abdallah kawai yayi da kallo cike da tsantsan mamaki duk da dama ya d'an lura akwai abunda ke faruwa tsakaninsu tun zuwanshi dan Abdallah ya canja halayenshi towards ita Asman sam baya maganarta kamar yadda ya saba kuma bai so yaji ana maganartan, kuma bai cika zama a gidanba hasalima tun da yazo yake ma Abdallah mitar suzo b'angarenshi amman yak'i yadda sai yau, yau d'in ma wayau ya mai sannan ya yadda,  shi dai abun mamaki yake bashi dan bai tab'a kawo hakan a ranshi ba amman yaci alwashin koma meye a tsakanin nasu zai daidaita shi da yardar Allah, Amsah ce ta katse mashi tunani da fadin,


"Haba ya Mahmud ai ni nayi fushi dakai sai yau kaga damar shigowa nan tun zuwanka, sai dai mu hadu a waje ko a bangaren Ammie ko?".




"Haba sis wallahi ba haka bane kin dai san halin mutumin naki ko? To sai yau ya gayyaceni shiyasa" ya fad'a yana satar kallon Abdallah, shiko gogan kamar ma ba ya falon dan hankalinshi kacokan nakan wasan kwallan kafar da ake nunawa a gidan talabijin.





"To shikenan ya mahmud kun tashi lafiya?".



"Lafiya k'alau ya jarabawa kun gama Waec ko? ".



"Eh, jarabawa Alhamdullilah".



"To Allah ya taimaka yabada sa'a, wai shin dakata ma tun kafin mu shigo nake jin k'anshin dad'i mun shigo falon kamshi yana nema ya cika mana ciki, da fatan da rabona dai a ciki"




"Aikuwa ya Mahmud dambune na girka maku" ta fad'a tana duban Abdallah dan tasan yana san dambu kamar tasan ko za'a rina tana fad'ar dambu ya juyo ya kureta da ido yana had'iye miyau can kuma ya kauda kai yaa had'e fuska kamar bashi ba, ita abun ma dariya yabata ta dai hadiye gudun kar ta b'allo ruwa.



ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now