page 81

4K 253 65
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨















💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*_NA_*
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *_QUEEN BK_* 👸🏼













🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan   zaman  lafiya  da amana    insha    Allah🤜🏻🤛🏻))













_Itz_queenbk @ insta gram_













Ku marmatso kusa fans😘😍😍 wannan page ɗin na baku shi kyauta, domin yabawa da votes ɗinku da kuma comments ɗinku kai harma da addu'oinku masu daɗi ubangiji Allah ya karɓa ya biya maku buƙatunku inayin ku irin totally 😎 ɗinnan, Allah ya barmu tare ya kuma haɗa mu a gidan aljannah Ammen saƙon gaisuwata mai tarin yawa a gare ku duka😍😍😘😘😘💋💋💋.

















Page 8⃣1⃣









Wata ɗaya da sati biyu cif kenan da yi ma Abdallah aiki, yanzu likitocin sun shaida masu cewa ya warke tagaragas dan haka suyi expecting tashin shi a ko yaushe hakan ba ƙaramin farin ciki ya sanya su Ammie ba yanzu hankalinsu kacokan ya koma kan Asmah dan tunda ta shiga watan haihuwa take cin wuya sosai kullum da inda ke mata ciwo gashi ba komai take ci ba yau safiyar laraba ta tashi da matsanancin ciwon mara gadan gadan da abun yazo kamar gaske sai kuma ya lafa abu kamar zata haihu sai kuma ya tsaya haka tayi ta naƙudar on and off har na tsawon kwana uku likitocin sunce inta wuce yau bata haihu ba za suyi inducing ɗinta haka ake ta fama, su Ummah kam sai addu'a suke Allah yasa ta haihu da kanta tun kamin akai ga inducing ɗinta ko ma ace CS.






Duba ɗaya zaka mata kasan tana cikin jin jiki sosai domin duk jikinta zufa yake fitarwa sai tauna baki take ga doctors ɗin nan zagaye da ita suna bata agaji cikin ikon Allah kan baby ya kunno kai nan likitocin suka tare tazarar sakon biyar wani kan ya taho nan ma suka ƙara tare shi a tare suka tsala kukansu na jarirai Ammie Ummah dasu hajiya zainab dake wajen ɗakin sai suka shiga hamdala a dai dai lokacin kuma Abdallah ya farka.




A hankali ya fara buɗa idanunshi Dr.kb ne da Mahmud kawai a ɗakin hannunshi ya motsa nan suka gane ya tashi da sauri suka isa gare shi dai dai lokacin kuma doctor da ke kula dashi ya iso ɗakin yazo duba shi ya iske ya farka, nan suka tallaboshi ya zauna amman kanshi sai rawa yake nan doctor yayi mashi wata allura tuni bacci ya sure shi ce masu yayi da ya ɗan samu bacci zai tashi normal insha Allah saboda yanzu jiri yake ji kasancewat daɗewar da yayi a kwance amman yanzu in ya tashi zai dawo dai dai.




A can kuwa Asmah na gama haihuwa suka mata allurar bacci saboda tasha wahala sosai, sannan suka gyara yaran duka mata ne masu tsananin kama da juna identical twins ne ƴan ƙanana dasu nauyinsu 3kj ko wacce a cikinsu, bayan sun gama tsaftace su suka sama su kaya blue da pink sunyi kyau sosai.




Su Mahmud suka shaida ma su Ammie farkawar Abdallah da yadda abun ya faru, ba su gama murna ba aka fiddo masu da Babies ɗin Asmah ƙudundune cikin shawal likitocin da nurses ɗin sai taya su murna suke suna yaba kyawun yaran nan suka shaida masu uwar tana nan lafiya za su fito da ita anjima in ta samu hutu, Ammie ta karɓa ɗaya Ummah ma ta karɓi ɗaya nan suka taru suna ganin yaran suna ƙara mika ma Allah godiya, duk wanda ya kallesu sai dai kaji yana faɗin masha Allah, yaran yadda kasan an ƙenƙesosu daga kwai kamar ƴan tsana suke tsabar kyau da Allah ya zuba masu har rasa wa ma suka biyo sukai wannan yace babansu ne wannan yace mamansu ce, sai dai in kai masu duban tsaf ba wanda basu fizgo cikin iyayen ba har sun ma fisu kyau.









ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now