page 15

3.8K 253 1
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨






💎💎💎💎💎💎💎💎 *ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*NA*
_BILKISU ALIYU KANKIA_
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼






🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S ((Z.A.W ))*
[Gidan   zaman   lafiya   da   amana   insha  Allah🤜🤛]




Ban manta dake ba y'ar autar mama, wlh matsayinki daban yake a zuciya ta *KHADIJAH ABUBAKAR ZAYYAD ( KAZA)* my cutepie, ina yinki irin sosai d'innan, ma'u na mik'o sak'on gaisuwarta😘





Page1⃣5⃣









Zan kaiki wani gida kina masu aiki, saboda halin da
nake ciki banzan iya kula da
ke sosai ba kamar yadda matar
da zakina ma aikin zata kula
dake, saboda na santa nasan
halinta sosai, tana da matuk'ar
kirki da dattako da sannin
ya kama ta, haka ma mijinta,
kuma ni na gaya maki ba za ki
tab'a da na sanin had'uwar
ku ko zama dasu ba, ina so ne ki samu gatan da baki
samu ba ada ma'u, kuma insha
Allah matar zata nuna maki gata,
dan halinsu ne ba sa k'yashin
taimakawa talakawa balle
maganar k'yamar su ta taso,
ni kuma nayi maki alk'awari
zan zame maki kamar uwa,
duk in hutun ku yayi zan d'aukoki
in kawo ki gida na har hutun
ya k'are, kafin Allah yasa sana'ata
tayi
k'wari sai na karb'o gaba d'aya
in baki kulawar da ya dace
da maraicin ki kinji,
ma'u
ko da fuskar ta tagama b'aci
da ruwan hawayen da yake
ta sintiri a fuskarta, duk da kukan
dad'i take, don bata tab'a zaton
zata ci karo da masu kirki
irin su aunty nafy ba, in ta tuna
shekarun da sukai da gwggo
amman dai2 da rana d'aya
bata tab'a nuna tausayi a gareta
taba, amman ita wannan daga
had'uwar su ba a dad'e ba
amman har tana ik'irarin zata
zame mata uwa kuma tasan
da ta na da halin rik'etan a yanzu
ba abun da zesa ta kaita gidan aiki,
Kuma ita tama ji hankalinta
ya kwanta da aikin da zatai,
tunda aikin da zatayi ma ai arzik'i
ne a wajenta tunda bata da wajen zama, ta ma yi bautar da ba abiya ta bama
balle kuma wannan taji hadda biyanta za'ana yi,
duk da yanzu kud'in bashi ne gabanta ba,
dan ta rigaya ta yanke aunty
nafy zatana ba,
barin
ma gashi yadda taji aunty
nafy na yaba halin uwar rik'on
nata sai taji sauk'i, oh Allah
d'aya gari bam bam, mutane kowa da kallar
ZUCIYAr shi,
ma'u ta d'au alk'warin zata
taimki aunty nafee da duk
abunda Allah ya hore mata,
kamar yadda tai k'udurin taimakonta,
kuma zata d'auke ta a matsayin uwa kamar yadda ta fad'a.

Ji tayi aunty nafy na share
mata kwalla, take ta rungume
ta tana jero mata godiya ba
k'ak'autawa, sai da aunty nafy
ta nuna fushin ta akan hakan,
Kafin ma'u ta dena, tana fad'in
Allah na gode ma da samun
uwa ta gari, aunty nafy ta d'ago
ta, tana share mata sabin kwallan
dasuka fara fito mata tana
fad'in ameen y'ar d'iya ta, nima
ma na gode mai da ya bani
d'iya kalar ki mai hankali, da
natsuwa ga kuma masifaffen
kyau,
Ma'u ta k'yalk'yale da dariya
cikin nishad'i suka cigaba
da hirar su, kafin ma'u ta tashi ta d'ora masu tuwo bayan
ta hura wuta.



Ma'u cikin kulawa da so tai
jinyar k'afar ta har ta warke
garas, daga nan aunty nafy
ta shiga koya ma ma'u yadda
ake gyare gyare da goge2
irin dai su glass da dai abubuwan
gidan zamani, waenda take
d'an dasu ta nuna mata wanda
ba ta dasu kuwa sai dai ta
mata bayani ta baki, kamar
in taga abun da ake juya shi
kar ta juya shi dan ze iya jan
had'ari barin ma irin su gas,
komai dai duk ta fad'a mata
sai
dai abun da yafi bata mamaki
duk abun da ta fad'a ko ta
koya  ma ma'u sau
d'aya tas zatayi shi ko ta fad'a
mata kamar yadda ta fad'an,
cikin dad'i za tace " wow ashe
d'iyar tawa akwai k'wak'walwa
bansani ba, ita ko ma'u sai
dai tai ta murmushi dama
ta k'ware akan shi,( ni ko nace ba dole ma'u tai k'wanya ba tasha madarar shanu tayi wanka da ita lol).


cikin sati biyu ma'u ta k'ware
wannan fanin sai dai abunda
baza'a rasa ba, dan haka aunty
nafy ta ce zata kaita gidan
aikin nata washe gari don
zataje k'auye d'auko y'an aiki,
dan ana ta mata waya kan cewa
ana so, ma'u tace to duk da
tasaba da aunty nafy sai taji
kamar kar ta barta, ta zauna
a gidan nata sui tacin d'umamen
kullum, dan dai aunty nafi tace
ba zata gane dalilinta nayin
hakan ba, amman nan gaba za tagane,
da sai tace ta yadda sui ta zama
a haka, ta k'ara maimai ta
GABA ZAN GANE a ranta, tare da addu'ar ko meye zata
gane gaban ya zamto alkhairi.


Ana gobe za akai ma'u daren
ranar aunty nafy ta zaunar da ita cikin kulawa
ta k'ara mata nasiha mai shiga jiki,
ta k'ara da "na lura ke yarinya ce
mai natsuwa da hankali ma'u
da kuma k'wazo a zaman da
mukai, halin ki yana da kyau
sosai, kin sha bam2 da kallar
yaran da nake kawo wa, dan duk
yawancin su d'an zaman da
da zasui dani wanda nake koya
masu aiki kafin in kaisu gidan
aikin su, yawancin su bamu rabuwa
ba tare da kin ga su nuna halin
b'era ba, wanda hakan yawanci
shi ke sa a kore su daga gidan
aiyukan su, to kamar yadda
na ga halinki kar inji ko in gani
an kawo man k'arar ki, ki cigaba
da rik'e mutuncin ki kar ki yadda
kamar yadda kika nuna jarumta
kika kwaci kanki daga hannun d'an iskan mutumin nan,
ki cigaba da yafa rigar mutuncin
ki a duk inda kika tsinci kanki, sannan wadda
zan kaiki
wajen ta ina son itama ki d'auke
ta a matsayin uwa duk matsalar ki
ba sai kin bari sai nazo ganin
kiba, ki fad'a mata za kiga ta jaki a jiki sosai, kuma
zaki same ta me k'ok'arin  warware
maki matsalar ki, ki saki jiki dasu duk da na lura baki
da bak'unta wanda hakan na
kyau, ma'u tace naji nabi auntyna,
kuma insha Allah zaki sameni
me tsananin biyayya, tace yawwa tawan suka cigaba da hira cikin raha.


washegari da asuba bayan
ma'u tagama sallah ta gyara
ma aunty nafy gidan ta tsab,
ta janyo ruwa tayi wankanta
tasa sabuwar rigar da aunty
nafi ta d'inka mata na jar atamfa
mai fulawowi bak'i d'inki duguwar
riga A shape ya mata kyau
sosai sannan ta d'auko bak'ar
hijabi dai2 gwiwa ta saka,
ta kwaso kayan ta data wanke
talinke tasa su a wata y'ar k'aramar
jakar
da aunty nafyn ta bata tare
da aje wallet d'in cikin wani
zip, Aunty Nafy ta fito cikin
shirinta tayi tsab dan itama
tafiya zatai ranar, ta d'auki
wayarta ta kira direban motar
ta, kan ya iso har sun gama
kalaci sai suka d'au hanya sai gidan Alhaji Muhammad Zayyana.







*
*A BEAUTIFUL THING CALLED SMILE DRIVES AWAY ALL THE VARRIERS BTWN 2 HEARTS IRRESPECTIVE OF THEIR DIFFERENCES.
**


👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼

ZAN SOKA A HAKAحيث تعيش القصص. اكتشف الآن