page 68

3.1K 225 22
                                    


🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨



💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*_NA_*
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *_QUEEN BK_* 👸🏼



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan   zaman  lafiya  da amana    insha    Allah🤜🏻🤛🏻))





_Itz_queenbk @ insta gram_





_YOU SHOULD NEVER COMPARE UR LYF WITH OTHERS, YOU WILL NEVER BE HAPPY IF YOU DO SO FOR U WILL FEEL THE GRASS IS OLWAIX GREENER ON D OTHER SIDE WHEN IT IS ACCTUALLY A BARREN LAND._
         *QUEEN BK...*








PAGE6⃣8⃣








Ajiyar zuciya Asmah ta sauke wacce ta rasa dalilin fitarta, a hankali ta d'ago kai suka had'a ido da Mahmud, kad'a mata kanshi yayi alamar ta fahimce inda maganganunshi suka dosa kuwa?, Jinjina kai tayi tare da cewa "eh" duk da Bata gama fahimtar inda ya dosa ba tukun tana da buk'atar ta zauna ta gano bakin zaren, murmushin gefen baki yayi tare da fad'in,



"Very good bari na tafi sai naji daga gare ki".



D'aga kai kawai tayi shi kuma ya tashi ya tafi, ta d'auki ak'alla minti 15 tana zaune a gun zuciyarta nata luguden maganar duk da ta kasa fitar da ansa d'aya k'wak'wara, a hankali ta Mike ta aje gyalenta gefe kitchen ta nufa dan ta d'auko tsintsiya da makwashi domin kwashe abunda Abdallah ya zubar.








Tazo fitowa kenan taga Abdallah ya turo k'ofar d'akinshi da sauri ta tsaya tare da mak'alewa jikin k'ofa dan har ga Allah ta tsorata dashi sosai, ganin yana sand'a ya sata lek'owa taga me yake yi, gani tayi ya je ya kulle k'ofa yana ta lek'e kamar bai San wani ya ganshi juyowa yai har suka kusan had'a ido da sauri ta k'ara mak'alewa sai da ya cigaba da abunda ya ke sannan ta k'ara lek'o da kanta gani tayi ya isa wajen abincin da ya zubar ya zauna ya fara ci kamar wani maye loma daya na korar wata yanayi yana zubar da hawaye yana waiga k'ofa hakan da yake ba k'aramin tausayi ya bata ba bata san sadda ta fashe da kuka ba sai tafin hannunta tasa ta toshe bakinta.




Hannunshi ya Kai kan plate d'in glass d'in da ya fasa aiko akai rashin sa'a hannun ya yanke sosai jini sai zuba yake Asmah bata San sadda ta d'auko first aid box ta isa gabanshi da sauri tana k'ara zubar da hawaye, zama tai gab da shi a hankali ta kamo hannun da yake jinin tare da fad'in "sannu ya Abdallah Dan Allah kabi a hankali ba sai kaci na k'asan nan ba ga wani DA yawa a kula k....." fizge hannunshi yayi yana mata tsawa, k'ara fashewa tayi da kuka cikin kukan take cewa






"Dan Allah ya Abdallah kar kamin haka ka taimakeni Dan Allah wallahi na gaji da kallar halin da kake nuna mun, zuciyata na gaf da tawarwatsewa a sanadin ko in kula da kake mun, ko kasan yan kwanankinnan da k'yar nake iya bacci? Da k'yar na ke iya cin abinci inba wani abunda ke mitsintsinata na dole sai naci abinci ba? ko kasan kwata kwata ba walwala a tattare dani? Ko kasan babu kwanciyar hankali a cikin zuciyata kona misk'ala zarratun? Wallahi kana azabtar da zuciyata ya Abdallah ba haka alkawarin da ke tsakanina da kai yake ba, ba haka muka gina soyaryarmu ba ya Abdallah, a tunani duk fad'in duniyar nan ba mahalukin da zai iya shiga tsakani na dakai, ya kake k'ok'ari k'aryatar da wannan tunanin nawa da nake ganin ba abunda zai iya canja shi, dan Allah kar ka cemun nayi babban kuskure da nake kallar wannan tunanin, ka ceto zuciyata daga k'angin daka jefata, ni nasan mijin da na aura jarumi ne mai juriyar gaske, be kamata ace wani abu ya hau kanka ba har ka d'auka pls try to overcome it nasan abun kamar da wuya amman kar ka manta matar kama jarumar macece idonta a bud'e yake tana gani sarai haka ma kunnuwanta suna iya jiye abunda ba kowa bane zai iya jinsa ba, kuma tana tare da kai komin rintsi komin wuya Asmah take ce bazata tab'a rabuwa dakai ba ya Abdallah, a tare zamu rayu cikin dad'i da rashinsa".








ZAN SOKA A HAKADonde viven las historias. Descúbrelo ahora