page 42

3.8K 241 7
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨






💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼








🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )












*WANNAN PAGE ƊIN NAKI NE RABIN RAI HAUWA'U UMAR ALIYU KIYI YADDA KIKE SO DASHI, QUEEN BK NAYIN KI HAR ƘOƘON ZUCIYARTA, MATAR USTAZ KENAN😁 ALLAH YA KAI MU MUSHA BIKI YA ƊAIYABA MANA TA MALLAM.😍💋❤🥰*



Page4⃣2⃣









*KADA KANA FIFITA BIN TAFARKIN SHAIƊAN FIYE DA HANYAR ALLAH A BAYYANE KO A ƁOYE CIKIN HARKOKINKA NA YAU DA KULLUM, KA SANI AKWAI MALA'IKU TARE DA KAI MASU RUBUTA AYYUKANKA DARE DA RANA......*
                          QUEENBK.








Shirye shiryen biki ne gadan gadan ke ta wakana kasancewar biki ya ƙara matsowa, yanzu dai halin da ake ciki Ammie da Aunty Nana suna Dubai, da da Auntyn yara aka tsara zuwa Dubai ɗin to kasancewar an taɓo file ɗinta ba damar zuwa, yanzu dai su uku sukai tafiyar daga Ammie sai Aunty Nana, sai ko wata designer dake Abuja ƙawar Aunty Nana, a can za su haɗo kayan ɗaki da kitchen da kuma lefe, sai ko kayan cin biki na Amarya, yanzu kwanan su ɗaya da tafiya dama tafiyar ta tsarin kwana uku sukai dan su tsaya suyi siyayya mai kyau, dan ma abun ya zo masu da sauƙi saboda ita D&J designer da suka tafi da ita mostly tasan kamfanonin ƙasar da yake ita regular costomer ce, kuma tasan farashin kayan su, shi yasa ba zasu sha wahala ba wannan kenan.




Tuni an ɗau gyaran part ɗin Abdallah, masu gyara ne ke ta aikin su, sukuma su Abdallah da zugar abokansa sai suka koma can guest rooms dake gaban gidan suka cigaba da tasu hidimar.




Suka ma a ɓangaren Amare shirye shiryen nasu yai nisa, dan duk wani kati sun gama raba ma mutanensu, kati da kwalin cingam suka rinka rabawa da kuma ankon biki iya ɗinki kawai ya rage, sannan duk wanda suka kaimawa sai suce ya kai ɗinki da wuri dan bikin sati mai zuwa ne, a haka suka raba katin gayyata, sannan duk wata souvernier sun gama tanadar duk abunda zasu raba yana hannunsu, sannan Nihal da kanta ta dawo gare su tare da sheda masu da gaske ranar bata da lafiya ne yanzu komai ya daidai ta tsakaninsu, su Zarah, Mimi da Nihal ko ɗunkinsu takanas har katsina suka kai Green House, sai suka kai wasu House of kaya, ɗinki ne za'a yi masu na gani na faɗa dan sunce a dole wannan biki su gwangwaje su shana, sannan ɓangaren ita Amarya kuwa, tuni shuwa ta zage gyarata yanzu sati ɗaya da farawa amman in ka ganta baza ka gane ta ba tsabar kyan da tayi, wani irin sheƙi take tana fitar da annurin haske, fatar jikin ta luƙui luƙui kamar ka taɓa jini ya fito tayi fayau da ita, fatar ta taushi kamar ta jariri sabon haihuwa, turaren jiki ko kamar an mata ɓarin drum a jikinta, dan wani irin fitinanne ƙamshi take, kowane lungu da suƙo da kukasan ana turarawa ba wanda ba ai mata, duk inda ta zauna ko ta gitta sai ta bar masu tsarabar ƙamshinta, tunda aka fara abun Ammie ta hana Abdallah ganinta duk kuwa da yadda yaso ganinta, sam ta hana bata fita ko daga ɗakin, shiko Abdallah hakan ba karamin ci mashi tuwo a ƙwarya yai ba, don yanzu ko abinci bai cika ci ba dan ya riga ya saba sai girkin Asmah, barin ma cofee ɗinta in bashi ba bai iya shan na kowa.




Naty ta iso, yanzu an ɗan fara cika a gidan domin Aunty uwani (Maman Mahmud) ma ta iso ita da muƙarrabanta, ita ma Naty da muƙarabanta ta iso ga kuyangi da yawa sai kai komi suke, ataƙaice dai an fara taruwa kasancewar biki saura sati ɗaya.





Tuni Asmah Mimi da Nihal sunje gidan su Zarah, kuma sun roƙi Mami akan ta bar Zarah in biki yayi saura sati ɗaya tazo gidansu sai an gama biki ta kuma yadda, sun bata katin da Ammie ta bada sukai mata, ta kuma tabbatar masu da zata zo saboda ma sunyi waya da Ammie.



ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now