page 26

3.5K 221 0
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨







💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*NA*
_BILKISU ALIYU KANKIA_
*QUEEN BK*




🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S🖊*
(( _Gidan   zaman  lafiya  da   amana   insha   Allah_ 🤜🤛 ))





Page2⃣6⃣


Mimi ta nisa tace "to kinji labarin mu dana ya Abdallah"

Asmah kam da idonta yai ja dan kukuan tausayin Abdallah, ta sharb'e hawaye tare da cewa "hak'ik'a wannan ake kira da k'addara, kuma ya Abdallah abun tausayi ne" take wani tausayi da sonshi suka d'arsu a zuciyarta, ta cigaba "yanzu Mimi kenan ma abun bai d'ad'e da faruwa ba, nazo ko?"

"Eh da zuwanki lokacin abun yayai wata d'aya da faruwa"

"Ubangiji ALLAH ya kawo mai sauk'i mai d'orewa"

Mimi tace "Ameen y'ar uwa, haka k'addara ta riga fata sai dai muta addu'a"

"Insha Allahu kam zamuta addu'an"

"To Asmah sai da safe don ni na rigada na fara jin bacci sosai, gashi har k'arfe d'aya da rabi yanzu kyaga asuba tayi"

"Haka ne abun ba wuya, nima baccin nake ji sai da safe"

"Allah ya kaimu" cewar Mimi

Daga nan suka kwanta Asmah zuciyar ta cike da tunani kala kala bacci yayi awon gaba da ita.


*************       ********
INDIA

Yau ne ranar fitar da result, yanzu haka Abbah na zaune a office d'in likitan dake incharge d'in case d'in Abdallah, bayan ya gama tattara wasu takaddu ya k'ara zira gilashin shi akan karan hancinshi sannan ya maida duban shi ga Abbah, hannu ya mik'a mashi suka k'ara gaisawa, bayan sun gaisa ya fara koro mai bayani kamar haka

"A gaskiya komai ya tafi akasin zaton mu, domin munsha maganin da allurorin da muka d'ora shi akai zasu taimaka sosai wajen ganin mun cinma burin mu nayi mai aikin, dama asalin buguwar da ya ma kan, ya haddasa juyawar k'wak'walwarshi kad'an daga nomal position d'inta, mun gano akwai wasu homones da take over screating d'insu, da kuma wanda take under screating d'insu, to shiyasa muka d'ora shi akan waennan magungunan da alluran na baya wanda suke controlling komai, kuma akwai waenda suke sa jijiyoyin su zama active, so in dai aka samu akayi mashi aiki a ka gyara wannan slight shift d'in da k'wak'walwar tashi tayi, ma'ana muka maida ta dai dai mazaunin ta, komai zaizo da sauk'i za'a samu waraka bi izhinallahi, to amman matsalar da aka samu shine dai dai inda ya kamata ace mun yanka in za'ayi operation d'in to dai dai wajen wata jijiya ce wacce sanadiyar juyawar k'wak'walwar ne itama ta canja guri, kuma da mun yanka wannan jijiyar mutuwa ce kawai don ita don itace ke controlling bugun zuciya (heart beat) muna kuma yankawa sai mutuwa, shiyasa yanzu ba za mu iya ba, amman jijiyoyin suna motsi ko ya aka samu slight shift d'inta ( koya aka samu matsawarta kad'an) to za'a iya mai aiki, yanzu dai za mu k'ara d'ora ku akan wasu allurai da magunguna na tsawon wata shidda rabin shekara kenan, at the process kuma Dr. KB kuma zai rik'a gwada shi da an samu sauyin position d'in jijiyar, sai kui sauri kuzo dan ayi aikin, yanzu dai kawai ku dage da addu'a ita kad'ai zata fidda ku"

Dr.Kb dake tsaye yace "Thank you very much doctor Alex"

Dr Alex yace "Don't mention please its my duty" sannan ya fita daga office d'in.

Abbah kam da tuntuni jikinshi yayi sanyi tunda doctor ya fara bayani, da k'yar ya tattara natsuwar shi waje guda ya fawalla ma Allah komai, ya tashi daga kan kujerar, ji yayi k'afafuwanshi sun gagara d'aukar shi tangal tangal ya fara alamun zai fad'i, Dr. Kb ne ya kamashi suka fita daga office d'in, suna fita Khalil ya taso da sauri ganin an kamo Abbah yazo ya amshe shi daga hannun Dr. Kb, shima ya girgiza jin bayanin da  likitoci sukai a bakin kb, an basu sallama bayan  an ba Dr. Kb sabin magungunanshi, sun isa gida lafiya zauna suke a babban falon Abban, Dr. KB ne ya koro masu bata yadda yake don Abbah ma kasa magana yayi, ilahirin falon kowa ka kalli fuskar shi za kaga yana cikin matsananciyar damuwa, addu'a mai tsawo akayi mashi sannan aka kaishi part d'inshi, du kuwa da damuwar da Ammie ta shiga Amman Abbah har yaso ya fita shiga damuwa, Auntyn yara ko bayan tagama munafurcinta ta nufi part d'in ta da zakwad'i.

Zauna take ita kad'ai kasancewar yaran gidan duk suna makaranta, ita kad'ai ce a b'angaren nata saiko mai aikinta dake can kitchen tana ta hidimarta, tana zaune ne kan kujera ta aza k'afa d'aya bisa d'aya, wata hamshak'iyar dariya ta saki ta jawo wayarta ta danna wasu lambobi bugu d'aya aka d'auka, ta d'aya bangaren aka fara magana

"Yayi hajiyar sama kina cin duniyar ki da tsinke fa"

"Hehehe Jumman Jos kenan ban kaiga cinta da tsinke ba tukun har yanzu dai da cokali nake ta fama" cewar Auntyn yara.

"Hahaha ai zaki k'ware mane tunda dai kin shigo harka"

"😃duk da taimakonki Jumman Jos aikin ki na kyau y'ar gari"

"Bakida case hajajju, dama abun da nake taso in tambaye ki kenan, ya aiki komai yana tafiya yadda ake so dai ko?"

"Sosai ko fiye da yadda baki zato"

"Hehehe ai na gaya maki boka Darb'usa bai da na biyu, aikinshi naci kamar ruwa"

"Na ko gani ganin idona, gaya nan Sun dawo dashi a haukacensa, ba abun da ya canja sai wanda ya k'aru"

gaba d'aya suka d'au dariya, Jumman Jos tace "To yanxu sai ki bada hinma muje mu amso d'ayan maganin da yace, dafatan akwai dai boza a hannunki ko, kinsan yace yana da tsada saboda aikinshi kamar yankan wuk'a ne"

"Indai boza ce akwai ta wannan ba matsala bace, matsalar dai itace mai zan cema Abbah ya banni in fita"

"Haba hajiya kar ki bani kunya mana, ina matantakar taki mana"

"Jumman Jos kenan baki son halin Abbansu ba"

"Bari kiji yadda zakiyi.............."


*******     **********  

Asmah kam duk ta k'agara taga ya Abdallah ko ba komai tayi kewar shi da yawa, cikin k'aguwa ta nufi part d'inshi suna arba da juna sai suka tsaya kallon kallo, hawayen tausayi ne suka rink'a bin kumatunta, Abdallah kam hannunshi ya rink'a bugawa a kanshi da k'arfi, dama haka yake in yana son ya tuno wani abu, can ko ya fad'i "Asmah" da k'arfi, da sauri ta k'arasa inda yake tare da rik'e hannun da yake ta buga kan dashi, tace "sannu ya Abdallah" d'ayan hannunshi yasa yana goge mata hawaye kana yace "Asmah ina kika tafi kika barni? me yasa kika zab'i kiyi nesa dani?"

" To gani gare ka yanzu ba zan k'ara nesa da kaiba kaji yaya"

d'aga kai yayi alamun "ay, tace " bari in kawo ma coffee ko?" da sauri ya k'ara d'aga kai alamun eh yana murmushi daga gani yayi missing cofee d'in nata, taje had'o mashi ne Khaleel ya shigo ya aje travelling bags d'insu a d'aki kana ya dawo ya zauna kusa da abokin nashi, tagama had'o mashi ta dawo tazo ta fara bashi a baki kamar yadda ta saba bashi, ita duk bata ma lura da Khaleel a wajen ba, shiko da tun shigowarta yake binta da idanu don dama bai santa ba, sai mamakin yake ina aka samu wannan y'ar larabawan cewa yayi "ya sunanki" sai lokacin Asmah ta d'ago ta dube shi, tsintar murya sukai ana cewa "sunanta Asmah k'awa tace" Mimi ce ta fad'a haka tare da shigowa, d'ago kai khaleel yayi yace " Ah Miminaye yaushe kika dawo" turo baki tayi tace "ai ni ya Khaleel mun b'ata da kai, lokacin da ka dawo ina ta murnar zan ganka sai kuma naji an cemun wai ka tafi"

"Ayyah miminaye tuba nake nima da son ganin ki na shigo gidan sai kuma nai kicib'is da mummunan labari shi yasa duk na rikice dole nabi mukatai India"

"ohhhh dama da kai aka tafi India, ai nasha Katsina ka wuce to Allah ya soka mun shirya"

"A'a Miminaye kin k'ara girma fa"

Tafin hannunta tasa ta rufe fuska alamun jin kunya, sai kuma ta falfala da gudu waje, girgiza kai yayi ya maida kallon shi ga su Abdallah, yadda kasan basu a falon don daga ganinsu bama susan me su Khaleel da Mimi ke tattaunawa ba, ita Asmah ta dage sai bashi cofee take shi kuma ya zuba mata idanu, cewa yayi "Asmah kawo in taya ki bashi" take Abdallah ya galla mai harara, itako Asmah cewa tayi "kabar shi kawai nama kusa gama bashi" shiko Khaleel dariyar hararar da Abdallah yayi mai yayi tare da mamaki domin acan asibitin ba ya yadda kowa ya bashi abinci daga shi sai Abba, Amman yanzu ji yadda ya kushe shi a bisa Asmah, wata dariyar ya k'ara saki sanadiyar wani tunanin da yayi.

muje zuwa

LEARN LIFE'S DANGEROUS LESSONS FROM OTHERS.

👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now