Page 9

4.1K 254 0
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨









💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*NA*
_BILKISU ALIYU KANKIA_
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼









🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S*
(( _Gidan zaman lafiya da amana insha Allah🤜🤛 ))_






Wannan page din sadaukarwa ne ga k'ungiyar *ZAMAN AMANA WRITER'S,* *((Z.A.W))* Allah ya k'ara had'e kan mu, yasa albarka a cikin rubutun mu, ya bamu ikon fad'karwa. Y'an uwa one love❤





Page0⃣9⃣






(waiwaye adon tafiya)

A cikin tafiye2 na da nake na sana'a ta, wata rana ina dawowa na tsinci wani mutumi da yarinya k'arama a hannun shi, wadda baza ta wuce shekara ukku da rabi ba, yarinyar sai kuka take shikuma jikin shi jina2 kamar an kwato shi bakin kura, kuma da alamu yana neman taimako sosai, ganin yadda ya firgice kawai neman mafaka yake, ga mutane sai kallan shi suke, ni kuma ganin shi a wannan hali yasa na matso kusa da shi tare da tambayar shi me ya faru da shi, ba amsar da ya bani illah;
banga halima ba wallahi, tana ina?, kar su kashe mun ita, sae ya fashe da kuka.

Niko ganin ba a hayyacin shi yake ba, yasa na mik'o hannu dan in amshi yarinyar in ja shi mutafi gida, in ya dawo cikin natsuwar shi, daga baya sai inji me ke damun shi ko zan iya taimakon sa, da sauri ya kab'e mun hannu tare da k'ara rungume y'ar hannunsa, yana fadin " kar ku rabani da ita ma."

Da kyar da sud'in goshi ya yadda ya bini gida, bayan mun isa na bashi ruwa yayi wanka sannan yasha, raunin hannun sa kam har a lokacin be dena fitar da jini ba, da na duba sai naga kamar harbin bindiga kuma ba'a fitar da bullet d'in ba, banyi k'asa a gwiwa ba, na aika a kira mun ta-sallah, bayan tazo ta riski abun da ya faru, ta rasa yadda zata fidda bullet d'in dan bata tab'a aiki irin wannan ba, cikin dabara dai da taimakon Allah ta fiddo mai, sai dai yaji jiki ba kad'an ba tunda ba k'wararra ba ce, a haka dai ta shafa masa wani magani sannan ta bashi wani yasha, bayan ya huta sosai muna zaune, da kanshi ya fara bani labarin me ya faru.

Ya fara da godiyar temakon da na masa, sannan yace,

" Ni sunana Muhammad maska, ni d'an asalin garin katsina ne amman muna zaune ne a damaturu ni da matata da y'ata guda d'ayan nan da ka gani, ya fad'a tare da nuna yarinyar dake kwance kan tabarma tana ta baccin ta, ita kad'ai Allah ya uzurta muda ita, ita ma d'in har mun fidda tsamanin samun yara, muka haife ta a shekar mu ta biyar da aure da matata mai suna Halima, ita kuma y'ar mai-duguri ce.

Sai da yazo nan a maganar shi sannan ya kalli ni ya ce mun yau laraba ko, ni kuma na gyad'a mashi kai, ya cigaba " kwana biyu da suka wuce ranar litinin kenan, tunda asuba da muka tashi ba mu koma ba kasancewar ina shirin zuwa office, ita kuma halima na ta shirya ma yarinyar mu dan ranar ne zata fara zuwa makaranta, kwatsam muka rik'a jin k'arar raki masu razanar wa, wata k'arar in ta tashi har gidan mu sae yayi girgiza, ga gari tuni ya hautsine ya hau kururuwa tunda ba wanda yasan mai ya faru, haka na tashi naje na kulle mana gidan mu, muka dawo mukai jugum2 in banda add'ua ba abunda muke, dan bamu san me ke faruwa ba, dan daga gani gari ba lafiya.
Halima ta bada shawarar mu kunna radio ko labarai, haka ko akayi muka kunna redio, anan muka ji ana ta shelar cewa " a safiyar yau ankawo wa garin damaturu farmakin ba zata, sun samu nasarar sa bomb a wurare da dama tunda ba'asan da zuwan nasu ba, kamar bankuna, masalatai, churchina, makarantu da dai sauran su, duk da ansamu rashi na y'an uwa da yawa, kar hakan ya tsorata ku hadin kan ku kawai muke buk'ata, dan Allah kar wanda ya fita, kowa ya tsaya a muhallin shi, domina gwamnatin k'asa tana ta aiki kan turo zakarun sodojin ta, dan suzo su yak'i wa'ennan y'an ta'adda, yanzu haka an taro wasu dakarun dan samun tsaro, had'in kan da zaku bamu kawai kar wanda ya fita, ku killace kan ku a cikin gidajen ku, kuyi ta addu'a.

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now