page 61

4.2K 247 20
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨








💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*_NA_*
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *_QUEEN BK_* 👸🏼








🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah🤜🏻🤛🏻))








*PAGE 61






Asmah ta rungumeta tana haɗe nata kukan ganin kukan Umman yana so yaci ƙarfinta cikin duɓara ta lallameta da kalamai masu taushi nan suka rufe shafin kuka, bayan sun masa addu'a nan ma sukai ma Baffah addu'a, Asmah tace "Ummah me kike nufi da mijin da Abbah ya zaɓa mun shina aura?".




Ummah tai murmushi tana tuna baya:

*Flash back (Tuna baya)......*








Zaune yake yana ta zane a paper, wani farin kyakyawan yaro da bazai wuce shekara tara ba, sosai kamaninsa da Ammie suka gaza ɓoyuwa a kyawawan halittun fuskar sa, zaune yake a wani babban ɗaki hankalinshi kacokan ya ta'allaƙa ga zanen da yake tayi a paper cikin ƙwarewa domin shi tunda ya tashi yana matuƙar san zane, a hankali aka turo ƙofar ɗakin Haleemah ce ta shigo riƙe da tray ɗin abinci a hannunta dubanta ta kai kan yaron ganin kwata kwata ma bai san da shigowarta ba don hankalinshi nakan abunda yake murmushi tayi ta isa gurinshi sai da ta dire tray ɗin hannunta sannan ta shafa sumar kanshi cikin so da ƙaunar yaron sai a lokacin ya ɗago yana faɗin,



"Habibty kalla motar dazan siya ma beauty inta girma sai in riƙa tuƙata ina kaita makaranta" ya faɗa yana nuna mata zanen haɗaɗɗiyar motar da ya zana da hanayyensa.




Murmushi ta ƙara sakar masa sosai cikin matuƙar son da yaron kewa ƴartata wanda har ya zarce wanda ita take masan kuwa domin komai nashi beauty ne dan tunda ma aka haifeta randa ya fara ganinta ya samata "Beauty" a cewarshi bai taɓa ganin kyakyawar baby kallarta ba, kuma tun daga ranar yake mugun son beauty kwata kwata bayasan abunda zai sata kuka ko kaɗan dan in tana kuka shima har kukan yake haka zaita lallashinta bai samun sukuni kuwa har sai tayi shiru, su Naty kuwa har mamaki abun yake basu kallar son da yake tsakanin nasu, dan dama Haleema a gida ta haihu bayan haihuwarta ne su Ammi sukazo hadda Abdallah a lokacin Ammie nada cikin Mimi, tun kuwa da Abdallah yasa idansa yaga Baby Asmah ya manne mata koda aka gama suna akai komai dasu Ammie suka tashi komawa Kano sam Abdallah yace bai san zancen ba dan shi sai dai abarshi wajen beauty yata ganinta kullum, duk yadda aka ja dashi kuwa yaƙi saki dole su Ammie suka haƙura suka tafi suka barshin kasancewar an shiga hutun long vocation, kullum yana manne da beauty kwata kwata bai bari a amsheta in tana hanunsa wata sa'in ko baƙi akai sunzo ganinta bai yadda ya basu ita sai dai su ganta a hanunsa inko akai nasarar amsarta daga hanun nasa haka zai ɗau fishi ya ta gungunai, har kuka yake a goya masa ita da rigimar tai rigima dole ake goyo masa sai yai kwance bisa gwado a ɗora masa ita bisa bayanshi a goya masa a haka suke bacci, sai sunyi nisa da bacci Haleemah ke kwance mashi goyon ta gyara mai kwanciya shima, inko akazo yi mata wanka har kuka yake jin yadda take kuka gako Asmah da kuka gani yake kamar cutarta ake haka kuwa mai wankan zatasha murguɗe da harara har ta gama yai sauri ya amasheta yana lallashinta tun abun na ɗaure masu kai har ya daina duba da kallar son shima da ya samu gurin Haleemar a sa'ilin da yake yaro dan ita ma Haleemah tun yana jinjiri take kiransa Habiby tana matuƙar sonshi a lokacin ma batai aure ba haka ya taso shima cikin shaƙuwa da ƙaunarta, shiyasa ma Naty ke cewa ai shi so kuikuyo ne ba shakka kuwa san da Haleematun tai mashi ne ya koma kan ɗiyarta har yafi nata ƙarfi, a haka Haleematu da baby Asmah suka fita daga wanka suka shiga shirin komawa Damaturu tuni akazo ɗaukar Abdallah domin an koma makaranta da ƙyar da suɗin goshi ya bisu duk da ba adaɗin rai ya tafi ba dan da tirjiya da zille zille aka kaishi mota dan a dole a barshi yabi beauty gidansu, ko a gida kuwa ba ƙaramin fasa kwakwa a kayi ba kuwa ganin ya dawo normal dam fushi ya ɗauka da dukkan mutanen gidan Auntyn yara ce ma ke tasa shi gaba yana cin abinci dan a lokacin suna mugun tare sai da suka sha wuya suka shawo kanshi a haka ma kullum suna cikin waya da Habibty kamar yadda suka saba kullum sai dai yanzu labarinshi baya wuce ina beautynshi? ya take? tayi kuka yau? me ya sata kuka?.





ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now