Page 34

3.3K 221 2
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨






💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼








🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )









Page3⃣4⃣





*KIYI NAZARI KI DUBI RAYUWARKI DA KYAU, ABIN FATA SHINE KI YAWAITA AIKATA ALKAIRI FIYE DA SHARRI, HAKA KUMA KI YAWAITA FAƊIN GASKIYA.....* **
                          QUEENBK.





Wani heart box ta fara cin karo dashi, chocolates ne a ciki kala kala, dariya tai cikin jin daɗi take faɗin "ohh my Allah as if he knows am craving for chocolates right now"
Ta buɗe DELUX ta ɗauko ta ɓare ta saka a bakinta, sannan ta rufe box ɗin ta aje gefe guda.



Ta koma kan paper bag ɗin ta ciro wata ƙaramar teddy fara, teddyn mai kyau, tana taɓa cikin teddyn ta fara kukan *I LOVE YOU ASMAH* abun ya bata mamaki a lokaci guda kuma ya birgeta yadda take jin teddyn na faɗin sunanta, haka tai ta dannawa tana shinshina teddyn dan ƙamshin turaren Aliyu take, sai da ta daɗe tana wasa da teddyn tana latsawa tana sauraran abunda teddyn ke cewa domin ta kasa yadda da abunda take ji sai kace a film ko a littafi.



Daga bisani kuma ta aje, ta kuma fiddo da wani ƙaramin ring case daga cikin bag ɗin, case ɗin ya haɗu shi kanshi abun kallo ne, a hankali ta buɗe wani zoben azurfa ne mai ɗan karan kyau sai ƙyalli yake, a hankali take jujjuya shi a hannunta a bayan taga an sa *A&A* a fili tace " **ALIYU AND ASMAH** kenan, kai kai amman ya Aliyu first class ne, ya iya soyayya" zira zoben tayi tana yaba kyan da yayi mata a hannu, sannan ta fiddo abu na ƙarshe dake cikin bag ɗin, card ne *MAROON* mai kyau sai kyalli yake, a fili tace "Ya Allah my best colour" a hankali ta buɗa ga abunda ke ciki:





  *"IF I SOMETIMES HOLD ON TO YOU TOO TIGHTLY IT'S BECAUSE I LOVE U SO MUCH, IF I WANT TO TAKE UP ALOT OF YOUR TIME IT'S BECAUSE YOUR PRESENCE GIVES ME SO MUCH PLEASURE, IF I WORRY ABOUT YOU TOO MUCH IT'S MY OWN FEAR OF LOOSING THE ONE I TRULLY LOVE, IF I DON'T WANT TO SHARE YOU WITH SOMEONE ELSE IT'S BECAUSE MY HEART WANT TO BE WITH ONLY YOU. AND IF MY EYES SEE ONLY U MY HEART HOLDS ROOM FOR NO ONE ELSE BUT YOU ASMAH.*
                     LOVE YOU
                      FORVER.
डगैराव गैवपेर ंरोकदलक गौर




A bangon katin ansa A&A FOREVER, wani murmushi tayi tace "ya Aliyu ina farin ciki amman bansan me yasa ƙasan zuciya ta take mintsinana, hakan a duk lokacin da muke tare sai in riƙa jin "kamar ban kyauta ba" na rasa wannan yananyin da abunda nake ji me yake nufi, bacin haka nasan ina sonka, indai yadda zuciya ta take fayyace mun so haka yake to ina maka shi"











##################

*RANAR JUMA'A*


Misalin ƙarfe 11:00am
Aunty nafi ta diro gidan, Asmah taji daɗin ganinta sosai tace

"Laa Aunty nafy bansan kina tafe ba, naga baki kira ta wayar Mimi ba kamar yadda kika saba"

Aunty nafy tace "aikuwa nima bansan da tafiyar ba sai shekaran jiya, Hajiya ce ta kira tana nema na"

"Meya faru" cewar Asmah

"Bansani ba tukun bari dai na shiga"

"To Aunty Nafy ɗan bani wayar ki na kira su ya Marwan mu gaisa"

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now