page 54

4.8K 271 17
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨







💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼











🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana insha Allah🤜🤛 )




















Page5⃣4⃣






Sai wajen sha ɗaya da mintoci suka tashi Abdallah ne ya fara buɗa idanunshi tsayawa yayi yana kallon fuskarta yana murmushi ji yayi jikinta zafi rau, hannu yasa yana zana mata fuska jin lumfashinta yayi yana fita iskar mai zafi gashi sai zufa take, a hankali yace "beauty mai ya faru naji jikinki yayi zafi".




Bata bashi amsa ba amman tana jinshi dan tun lokacin da ya fara zana mata fuska ta tashi, hanunshi ya sa cikin rigarta yaji wuyanta da ƙirjinta duk zafi rau, cewa yayi "wayyo beauty baki da lafiya wallahi jikinki zafi kamar fa ruwan zafi".




A hankali ta buɗa idanunta tana jin jikinta duk ba daɗi ga wani azababben ciwon kai da ya addabeta, ruɗewa yayi gaba ɗaya ganin yadda duk ta faɗa lokaci guda da sauri ya tashi yace "beauty ina zuwa" sannan ya fice.






A falo sukai kiciɓis da Ammie dake shigowa da sallamarta yana ganinta ya isa gareta yace "Ammie kizo kiga beauty bata da lafiya fa" Ammie murmushi tai kawai jin yadda ya ƙara canja ma matar tashi suna, ganin ya ƙura mata idanu yana son yaji tayi magana yasa tace,



"To muje na gani", ta faɗa tare da wucewa ɗakin yana binta a baya.




"Inalillahi Asmah jikinki da zafi masassar kike ne? akwai ciwon kai?".





Ɗaga kai tayi Ammie ta ƙara cewa "kuma kinsha maganinnan dana kawo maki ɗazu".






Ta ƙara ɗaga mata kai, take Ammie ta fiddo wayarta ta kira Dr. Aisha dama kallar wannan case ɗin ita suke kira bayan Dr. Aisha ta tabbatar ma Ammie akan zata taho yanzu ta kashe wayar ta dubi Asmah tace "yo bama kici abinci ba ko naga kalacin dana ba uwar talle ta kawo maku yana nan bisa tebur ko taɓa shi bakuyi ba".







Asmah tace "Ay", komawa Ammie tai falon ta zubo farfesun ƴan ciki da chips da wainar ƙwai sai tea mai kauri data haɗa mata ta dawo ta zaunar da ita zata fara bata, Asmah tace "Ammie bari naje nayi brush".


"Zaki iya ko?" murmushi Asmah tayi tana jin daɗin yadda Ammie ke kulawa da ita, tace "zan iya Ammie".



Da ƙyar ta faɗa toilet tai brush duk jikinta a mace yake bayan ta fito ta zauna bisa gado Ammie ta fara miƙo mata abinci da sauri Asmah tace "zan iya ci da kaina Ammie".




Abdallah dake gefe yana ta binsu da kallo tun ɗazu da sauri yace "Ammie kawo na bata".




"To imaza gashi ni bari naje kafin Dr. ta iso dan baƙi na baro a falo" ta faɗa tana miƙa ma Abdallah plate ɗin tana tafiya bayan ta mata addu'ar samun sauƙi.





Abdallah ya dawo kusa da ita ya zauna ya shiga bata abincin yana hura mata da bakinshi, duk sai taji ya bata tausayi yadda duk ya tada hankalinshi akan ciwonta duk ya marairaice kamar ya cire mata ciwon yake ji, tana iya hango hawaye kwance a ƙwayar idonshi, gashi ya dage so kawai yake taci abincin shi bai ma damu da cikinsa ba sai ya tabbatar ya hura mai zafin sosai yadda bazai ƙona ta ba, fuskar shi ta kamo suka haɗa ido cewa tai "baby na ya akai? me aka maka? me kake so?".






ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now