page 82

4K 292 57
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨














💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*_NA_*
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *_QUEEN BK_* 👸🏼
















🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah🤜🏻🤛🏻))
















_Itz_queenbk @ insta gram_











Page 8⃣2⃣














Washegari da sassafe Abbah ya iso ya baro Auntyn Yara da wata ƴar uwarta budurwa me kimanin shekaru 18 a gida dan yanzu an sallamota daga asibiti ta warke garas sai tabunnan ciwon da taji, keken guragu aka bata yanzu dashi take tafiya, wannan budurwa mai suna Zeenah ita ke kula da ita ɗiyar ƙanwarta ce, yarinyar akwai mutunci da hazaƙa ita ke mata komai dan gane da jikinta, a inda mai aikinta ke sauran, yanzu Auntyn yara ta safko sosai barin ma da taji yadda Ladi tayi mutuwar wulaƙanci shi ne take tunanin fidda wannan muguntar a ranta tazo tai ta aikin tuba wajen ubangiji da waenda ta zalunta sai dai labari ya canja a lokacin da haihuwar ƴaƴan Abdallah ya iso kunnenta sai da tayi ƙaramin hauka tsabar baƙin ciki bugu da ƙari kuma Abdallah ya samu sauƙi.
(Ni ko a raina nace anya matar nan tana da alamar tuba a ranta kuwa muje zuwa muga ina ta dosa).




Bayan Abbah ya iso likitoci sun mai bayanin duk abunda ake ciki yayi murna sosai ta wani ɓangare kuma bai ji daɗi da Abdallah ya manta matarshi mutuniyar arziƙi ba, Allah sarki baiwar Allah dan ma Allah ya bata haƙuri da ya zata ji ga jego ga wahalar yara har biyu da ba babansu a kusa da zai na ɗebe mata kewa yana taya ta wahalar oh Allah me tsarin shi a sadda yaso akan ko me yaso, Allah kasa mana fahimta a zuciyoyinmu.


Ɗakin da Asmah ke ciki ya fara nufa yaga babies ɗin ya nata sa ma Asmah albarka yana ƙara yabawa da hankalin ƴarinyar, daga nan ya wuce ɗakin da aka kwantar da Abdallah cikin murna uba da ɗan suka tarbi juna suna masu matuƙar farin ciki.






Ƙarfe sha biyu dai dai aka ba Asmah sallama suka wuce gida wankan jego mai kyau Hajiya Zainab tayi mata ta shiryata tsab Ammie kuma tayi ma babies ɗin wanka aka feshesu da turaren yara mai sanyi, turaren wuta mai daɗi aka kunna a gidan ya hau fitar da ƙamshi mai daɗi ɗakin mai jego kuwa room heater aka kunna kasancewar weather su ta can ana wani muku mukun sanyi ne, kamar yadda al'adar su tacan ta tanadar, jama'an unguwa mata sukai ta shigowa nan sukai ta dafa abinci da kayan maƙulashe irin dai nasu kala kala, da suka gama suka gyara wajen tas sannan suka rinƙa fito da kyaututtuka kala kala suna ba Babies ɗin da uwar jegon, haka suke tarbar sabon jariri suyi mashi kyauta sannan suyi ma uwarshi abinci kala kala, kasancewar suna fita kullum shi yasa suka saba da mutan unguwar.


Washe gari aka sallamo Abdallah bayan an ɗora shi akan magunguna, suma nan suka yo gida koda ya tambayi wacece Asmah ce mai sukai ai beautynshi ce ta dawo nan suka bashi labarin yadda akai ta ɓace da kuma yadda Allah ya ƙara haɗa su da ita ba tare da sun sha wata wahala ba sai suka yanke mai sauran labarin saboda gargaɗin likita na cewa kar a sake a tuna mashi wani abu da ya faru da shi a baya domin zai ta ƙoƙarin tunowa ne wanda hakan hatsarin ne ga ƙwaƙwalwarshi, sun ƙara mashi da cewa Asmah tayi aure har ta haihu yanzu haka mijinta yayi wata tafiya mai tsawo ne, ya ji daɗi sosai da beautynshi ta bayyana gashi yanzu har tayi aure har Allah ya albarkace ta da ƴaƴa.





ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now