page 24

3.8K 212 0
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨









💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*NA*
_BILKISU ALIYU KANKIA_







🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S🖊*
(( _Gidan   zaman  lafiya  da   amana   insha   Allah_ 🤜🤛 ))







MURJANATU Y'AR BABA
MAMAN MARYAM
MARYAM YAQUB
MIJINA SIRRINA GROUP

Wanan page d'in naku ne fans kuyi yadda kuke so inayinku irin totally




Page2⃣4⃣






[23/12 4:40 pm] 👸🏼Queen bk👸🏼:




TUSHE MAFARAR DAWA

Alhaji. Zayyan haifaffan garin kano ne, kuma shahararran d'an kasuwa wanda ya bunk'asa ta fannin kasuwanci, su biyu ne a gun mahaifansu, shine na farko sai k'anwarshi Zainab wadda ake cema Aunty uwani, yanzu haka tana aure a garin katsina, tana auren wani d'an siyasa, d'an ta d'aya tilo me suna Muhamud sojan ruwane, d'an uwa kuma aboki ga Abdallah, shi kuma Alhaji Zayyan anan kano ya kafa dangi nan ya auri matanshi biyu, ya kuma tara y'ay'a sha takwas, Muhammad ne na takwas a gidan su yana da k'anne goma kenan, sun taso cikin kulawa da gata domin babansu ba k'aramin mai naira bane, yana da gidajan mai bila adadin na kanshi ma banda wanda suka gada shida Haj.uwani a matsayin gado na iyayensu, ga manyan manyan plazas, super makets, baby's boutique kai da abubuwa ma da yawa da yake dasu, bama garin kano kad'ai ba, don haka iyalanshi ba abunda suka nema suka rasa, ilimi kam ya basu tunda ga kan boko har arabi uwa uba tarbiya, da yaro ya d'an fara tasawa zai fara koya mai kasuwanci, ya nagama secoundary kuma zai bashi jari ya fara ja, yana kasuwancinshi yana karatu a haka har ya samu mata yai aure, matan kuwa duk wacee ta gama secoundary sai ya mata aure ita ma ya bata jari da zatana juyawa, shi Muhammad ya karanci Business Administration ne shiyasa Alh. Zayyan yafi sakar mashi ragamar kasuwancin shi sosai, kasancewar fanin ya karanta kacokan, akwai wata tsohuwar shak'uwa da aminta dake tsakanin su da masarautar Mai duguri tun iyaye da kakanni, to haka abun yazo har kan Alhaji. Zayyan da sarkin dake mulki a yanzu a garin mai suna Sarki Sulaiman Soro da ke kan karagar mulki yanzu, shak'uwa ce ba y'ar k'arama ba tsakanin Alhaji Zayyan da sarki Sulaiman Soro wadda har ta kai soyayya mai k'arfi ta k'ullu tsakanin Muhammad d'an Alh.Zayyan da y'ar wajen sarki Amina, lokacinda iyayen suka tsinci maganar ba k'aramin farin ciki suka shiga ba, don a ganinsu zasu k'ara dank'on zumunci ne, nan da nan aka fara shirye shiryen biki kasancewar lokacin muhammad ya gama karatunsa kuma har ya fara aiki, gashi dama tun kafin ya gama karatun shi ya dogara da kansa, a yayin da ita kuma Amina take shekarata ta k'arshe a secoundary.




*******        *********   
MASARAUTAR MAI DUGURI

Sarki sulaiman gagarumin sarki ne da ake tunk'aho dashi a duk fad'in jahar mai duguri, domin adalin sarki ne, mai son talakawanshi, sam baya k'yamar su kuma yana taimakonsu sasai, shiyasa suma suke son shi, mahaifinsa ya rasu kana ya hau karagar mulki, yana zaune da mahaifiyar shi a gidan sarautar, ana cemata mai babban d'aki, tana da power sosai a gidan shi kanshi bai zartar da hukunci sai ya shawarce ta, duk fad'in gidan daga shi har matanshi ba wanda ya isa ta aje kara ya tsallake, bare kuma bayi da kuyangin gidan, matar sarki sulaiman ta farko sunanta Bilkisu wacce ake kira da Mai gado, auren had'i ne akayi don y'ar uwa ce, y'ay'anta shida kuma duk mata ne, Mai babban d'aki ta kawo mashi mata tace ya aure ta wata k'ila adace ya samu magaji, haka ko akayi ya auri kilishi, sai dai shekararsu hud'u da aure ko b'atan wata bata tab'a ba, nan ma Mai babban d'aki ta kuma kawo mashi wata shuwa me suna Fatima tace ya aure ta ko Allah yasa adace, cikin ikon Allah ko bayan aure da wata tara ta sunkuto k'aton d'anta mai kama da mai martaba sak, hakan ba k'aramin soyuwa yayi ba a zukatan mai martaba da mai babban suna ba, biki gagarumi aka shirya ma sunan d'an, wanda ya tara sarakuna na garuruwa da manyan mutane, anci ansha anyi shagali naira tai kuka, d'a yaci sunan kakansa ma'ana tsohon sarki Aliyu sai ake kiranshi da Yarima Hydar,  duk fad'in masarautar sai ina aka saka ina aka aje ake da d'a da uwan tsabar farinjinin da suka samu gun jama'a, fanin mai martaba kam sai ririta su yake yana tarairayar su, ai kar ku tona a tab'o mai babban d'aki abun yafi gaban wasa, ashe duk abun nan da yake faruwa a gidan Mai gado da Kilishi ba k'aramin b'acin rai suka shiga ba, don haka sai suka had'a kai suka ware ta, suka shiga y'an k'ulle k'ullen su, suna had'a mata makirci, ita ko Allah kawai tasa a gaba, kullum tana cikin addu'a, hakan yasa ta kwanciyar hankali, haihuwarta ta biyu ma namiji ta kuma haihuwa, aka samai Muhammad Areef, sai Nana Amina, sai Nana Halimatu, sai autansu Mustafa, wannan kenan.








ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now