page 21

4.1K 228 2
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨








💎💎💎💎💎💎💎💎 *ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*NA*
BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼






🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 🖊
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah🤜🤛 ))








ubangiji Allah ya k'ara maki k'arfin jiki my takwarans 🅱k yasa kaffarace Allah ya yaye maki kaf damuwarki ameen ya quddus❤






wannan page d'in naki ne my aunty na *Aunty* *sa'adatu* ubangiji Allah ya raya mun baba na ( *Aliyu* ) Allah ya daukaka shi duniya da lahira ya k'ara mai k'oshin lafiya yasa alumar muslmai suyi alfahari da shi young shall grow, more heavy bones dear inayinku irin totally😍 wannan page naka ne kai d'aya my love😍💋❤









page2⃣1⃣









Washe gari bayan su Mimi sun dawo makaranta, lokacin ma'u ta gama aikinta na safe suna gama lunch suka fita na irak'i (diraban gida) ne ya kaisu wajen gyaran kai, gyaran yayi kyau tubarkallah ba'a magana, bayan sun gama suka isa gun telan wata mace ta gwada Ma'u, a kace ta zab'i styles d'in da take so, ita dai kallo kallo kawai take, Mimi ce ma me zab'ar mata, bayan an gama suma suka bayar da nasu Mimi da Nihal, yasmeen kam sarkin miskilanci sai da sukaje wani shagon ta bayar don ita inda take bayar wa daban ne, sai da ya biya da su suka siyo ice cream kana suka dawo, suna tafe suna sha a mota, Ma'u kam sarkin kwad'ayi sai santi take.

*BAYAN KWANA BIYU*

Ma'u ce a d'akin ya Abdallah tana ta goge ruwan da ya zubda a d'akin, ta lura yau y'an masifar ne ke kan shi, shiyasa bata kula shi ta cigaba da aikin ta duk me yai sai ta gyara, tana fitowa falo turus tai dan ganin falon da ta gama gyarawa tas shine duk yazo yaci ayaba da takai bunch d'aya, kuma duk ya ciccilla b'awon ko ina, tace "to ko ina ma ya tafi " k'ofar falon aka turo, shine ya shigo sai fito yake yana kad'a kai, da alama ya dawo daga gaishe da iyayen nasa ne, ko kallon ta baiba ya wuce d'akin don yin wanka, k'wafa tai tare da k'issima wani abu a ranta sannan a fili tace "wallah zan rama ne " barin ma da ta tuno dukan da tasha wajen shi jiya, ta kwashe b'awon ayaban tas, sai tabar guda biyu, ta zo ta jera su daidai inda zai fara takawa da ya fito k'ofar d'akin, tai murmushin mugunta tuna film d'in da ta kalla mbc2 *(HOME ALONE)* taga kallar wannan muguntar, kana ta koma ta lab'e dai-dai inda zatana hango shi, ya gama wankan shi ya ciyo gayun shi ya tako cikin isa yana k'wanbo, aiko akai rashin sa'a tarkon ma'u ya kamo, d'ora k'afa d'aya yai kan b'awon da yake yana cikin tafiya sai ko santsi ya kwashe shi ya fad'i k'asa timmm,!! duk yadda Ma'u taso kar tayi dariya amman abun ya bata dariya sosai, barin ma da taga duk k'ok'arin da yayi na ya dafa bango ko ya rik'o kujera dan kar ya fad'i amman abun yaci tura, a ranta tace "na rama," tun tana sunne kai tana dariya har ta fito fili, sai da ta d'an k'yaje kana ta matsa kusa dashi don taga baya da alamun tashi, don ko motsi ba yayi, gani tayi jijiyoyin kanshi sun fito rad'a rad'a cikin fargaba tace

"Ya Abdallah me ya faru? sannu, don Alah ka tashi"

A hankali ya bud'e runannun idanun shi tar akanta, a karo na farko taji wani mugun tausayinshi ya d'arsu a zuciya da sassan jikinta, da sauri ta tsugunna daf da kanshi tana mai dana sanin abun da ta aikata masa har k'ok'on zuciyar ta, duk ta rikici d'an kwalin kanta ta cire tana mai fifita, kamar hakan zai sa rad'ad'in ya ragu, cikin wata raunanniyar murya tace

"Sannu, yaya dan Allah ka yafe mun, laifi nane da ban d'auke b'awon ayabar ba, na tuba bazan k'ara ba dan Allah ka tashi kace ka yafe mun kaji yah Abdallah. "

ZAN SOKA A HAKAΌπου ζουν οι ιστορίες. Ανακάλυψε τώρα