page 40

4.6K 250 15
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨






💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼








🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana insha Allah🤜🤛 )










page 4⃣0⃣




*IDAN KAGA MUMMUNAR TARBIYA KO MAI AIKATA LAIFI KADA KAYI SAURIN LA'ANTARSA ABIN SO SHINE KAYI MASA ADDU'A TA NEMAN SHIRIYA KUMA KAYI SHIRU.......*
QUEENBK.





Suna isa gida suka wace ɗaki ganin har lokacin Asmah ba ta daina kuka ba gashi taƙi faɗa masu komai akan abunda ya faru tsakaninsu da ya Aliyu, Zarah ta fiddo tape ɗin da ta maƙalama Asmah a baya, Mimi ta kunnna system ɗinta sukai playing.



Gaba ɗayansu sun natsu suna sauraren tattaunawar tasu tun daga farko, sai dai kusa da ƙarshe duk suka canza fuska cikin mamaki suke jin meye dalilin kukan Asmah, Zarah ta ƙwallah wata uwar ƙara da duk suka maida dubansu kanta, riƙe kai tai tana faɗin


"Ya Aliyu ne? Ya Aliyu ne? shi ya faɗa haka da bakinshi? yaushe ya Aliyu ya sauya halinshi ban sani ba? ko dama haka yake ban gano bane tun asali, kai ƙaryane ba haka yake ba ruɗin shaiɗan ne, na san halinshi duk gidan mu ba wanda ya kai ni sanin ya Aliyu, me yasa ya kasa cinye jarabawar da tafi komai sauƙi?" ta faɗa tare da fasa kuka.


Asmah ganin haka ita ma sai ta sassauto, tasan ba halin ya Aliyu bane ruɗin shaiɗan ne, matsawa tai kusa da Zarah ta kama ta tana faɗin,


"Kiyi shiru Zarah dan Allah ki daina kukan nan, nasan ba haka ya Aliyu yake ba?"


"Ba haka yake ba ada, amman yanzu ban iya shaidar shi Asmah da bakin shi fa yake faɗin zai aikata masha'a, da bakinshi Asmah har yake ikirarin ba wanda zai sani, ya manta Allah yana nan a madakata yana kallon kowa kuma yana jiran kowa, ya manta? anya ya Aliyu yayana ne kuwa Asmah, anya su Mami ba tsunto shi sukai ba? yau na shiga uku na wai ya Aliyu da bakinshi" ta ƙara fashewa da kuka.

Mimi tace "dan Allah ki share hawayenki ki daina kukan nan, shi fa ɗan adam ajizi ne tara yake bai cika goma ba, tunda musan ba halinshi bane mun san ba'a son ransa ya aikata haka ba, sai mumai uzuri mana tare da addu'ar Allah ya yaye mai shine kawai abunda za mu iya mashi mu taimake shi mu ceto shi daga hallakar da yake son faɗawa ba wai muyi ta aibatawa ba, to kuma bai aikata abunda yake so ya aikatan ba ai kunga da sauƙi yanzu kawai ya cigaba da azumi yana roƙon Allah yafiya, Allah gafurur rahim ne, there is no point makin matters worst, dan Allah ku daina kuka ku duka kawai kumai addu'a".


"Mimi in kince haka ina zaki aje furu cinsa na ƙarshe fa?" cewar Zarah.

"Kar ki damu yayi magana cikin fushi ne ba abunda zai faru sai alkhairi".



"Shiyasa tun farko nace maki mu fidda cewa muna da alaƙa da su don mu warware matsalar, wallahi namiji ba abun yarda bane, namiji buhun barkono ne, namiji ɗan bushiya ne ka goya shi ya soke ka, duk macen da ta maida namiji uba to zata mutu marainiya, nifa shiyasa ban gaskata maza in ba na tantance su ba, ni ta wannan ɓangaren ko baba na bazan iya yadda da shi ba domin ai ban san baƙin cikin da ya ƙunsa ma mahaifiyata ba".



Duka suka zaro ido suna kallonta, ta cigaba "Namiji Namiji ne bai canza suna ko yaya ne sai kin samu ɗan halin su, ko ku yarda ko kar ku yadda".



ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now