page 39

4.2K 212 10
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨






💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼








🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )












Page3⃣9⃣




*YAYIN NEMAN AURE DA ZAMA DA IYALI KADA KI TOZARTA SOYAYYA, KA ƘAUNACI MAI SONKA DON ALLAH KA GUJI YIN SANADIN ZUBAR HAWAYEN MASOYI, A RAYUWA DUK ABUNDA KAYI ZA AYI MAKA KO AYI MAKA WANDA YAFI SHI.*
                          QUEENBK.






"Kunsan su maza so kala kala suke, shiyasa nace maku zamu masu jarabawa don tantance mai maki son gaskiya".

Mimi tace " wane kaloli ne son dasu mazan suke yi?".

Zarah ta cigaba " kinga akwai son tsakani ga Allah wanda daga zuciya yake zuwa kuma shine son da bai taɓa mutuwa kuma ko a ya kike zaiji shi dai kawai ke yake so ko ya kike, sannan akwai so domin wani abu naki ko abin da kika mallak ko kyawunki ko surar jikin ki wannan son shi yafi hatsari domin duk ranar da aka wayi gari kin rasa wannan abun da yake sonki don shi to kuwa shikenan son da yake maki ya mutu tunda dama abun yake so to kuma yanzu bashi, shi son surar jiki shine son sha'awa shi kawai yana sonki ne don waennan surorin naki, to kunga ko da anyi aure with time kina tsofa yana rage sonki tunda kina lossing shape dinki sannan shi dai kawai ya biya buƙatarsa dake shine kawai muradinsa baya da haka kamar tarkace kike a wajensa, sannan akwai son halayya da ɗabi'u wani saboda kyawawan halayenki da ɗabi'unki kawai yake son ki kuma wannan baya da matsala domin ya halatta a musulinci, akwai son ganin girman iyayenki shima ba haram bane wanda ya ga iyayenki ya san halinsu ya kuma gamsu dasu yana ganin girmansu kuma suna birge shi to zai iya jin yana son ɗiyar da suka haifa don shima ya gina gidansa kamar ko fiye da yadda iyayen naki sukai, sannan akwai son tausayi shi kuma yana sonki ne kawai don yana tausayinki ko kina basa tausayi, akwai son mugunta, bari dai kar muyi zurfi nasan zamu samu amsoshinmu a iya waennan, dan haka a taƙaice kunji yadda maza suka kasa son da suke ma mata kashi kashi, dan haka sai ka bi a hankali wajen tantance mai sonka na gaskiya ".


Mimi tace "Gaskiya ba banza ba ƴan ajinku ke zama kina basu lectures ba sunsa abunda suke kwasa"

Zarah ta juya idanu tare da faɗin "ba banza nake karatun novel ɗin turanci da hausa ba, nasan amfanuwar da nake"

Mimi tace "ahhh muma mun shiga system ai" ta faɗa tare da miƙa ma Asmah hannu suna tafawa, sannan ta cigaba "to yanzu munji wannan yanzu meye jarabawar da kika ce za'a masu?"

"Owk a ganina yadda situation ɗin yake, jarabawar da zamu ɓullo masu da ita domin tantance mai ma Asmah son tsakani ga Allah shine" ta faɗa tare da maida kallonta ga Asmah sannan ta cigaba "Asmah zaki samu ko wannen su ɗai ɗai sannan ki faɗa masa cewa *yayi haƙuri ya yafe maki bata mashi lokacin da kikai masa ke dama ba sonsa kike ba kina da wani* to duk wanda yayi zuciya ya tafi ya barki ko kuma yace to ya haƙura to dama can ba son tsakani ga Allah yake maki ba, in kuma son domin wani abu ne to zai fito maki da zalamarsa a fili, wannan itace jarabawar da nake tunanin zata warware mana matsalar nan ya kuka ce sis?"

Mimi ce tai sauri faɗin "gifted mind sis barakhallahu fihki wallah tayi sosai" ta faɗa tare da ɗaga mata thumbs ɗinta duka sama alamar tayi ƙoƙari.

Zarah ta juya wajen Asmah tare da faɗin "Asmah banji kince komai ba?"

"Zarah komai yayi, sai dai ina ganin har yanzu ban san meye son gaskiya ba, domin ni duk wanda yai mun dariya ya sake mun fuska sai na ɗauka sona yake shi yasa na ke ƙarewa ina cutuwa daga ƙarshe, ina so ki kuma mun bayani akan dmso da kuma son gaskiya"


ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now