page 35

3.5K 196 1
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨







💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼









🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )











page3⃣5⃣







*KI NATSU SOSAI YAYIN MU'AMULA DA MUTANE, KI SAURARI MAI ZUWA MAKI DA MAGANA, KI SANI BA KOWACCE MAGANA AKE YARDA DA ITA BA, DON BA KOWANE MAI BAKA SHAWARANE KE NUFIN KA DA ALKHAIRI BA...*
                          QUEENBK.





"Ki natsu sosai Asmah, ki saurari abun da zan faɗa maki yanzu, mun tattauna akan wani batu nida hajiya, zata zo maki da magana kar ki bada amsa cikin gaggawa kiyi nazari sosai kafin ki fidɗa amsar, sannan ki zaɓi abunda kika ji ya kwanta maki a rai, kuma kiyi istikhara dan neman zaɓin Allah, kisani ni ina bayan ki a duk zaɓin da ki kayi, ita *MATAR MUTUM KABARINSHI CE* , kamar yadda kabarinka bai canjawa haka ma matar ka bazata canja ba" ta kamu hanayenta duka tana dannawa a hankali sannan ta cigaba "ina bayan duk zaɓin da kikai, kinji ɗiyata"




Asmah cikin rashin gane inda maganarta ta dosa tace " Aunty Nafy zaɓin me zanyi? kuma wace magana ce Ammie zatai mun? Kuma kinc......."





Aunty Nafy ta katseta ba tare da ta amsa mata tambayoyinta ba tace " Asmah ina fatan kin san saƙon zaciyar *MARWAN* dan yace shi zai sannar maki da kansa shiyasa ban kawo maki maganar ba, dan kar kiji kamar ina ƙoƙarin tilasta maki abunda bakya ra'ayi shiyasa na fita daga maganar iyaka nawa in an shirya ne, kinga tuwo na maina, amman duk inda ta faɗi sha ne a wajena, saboda duk cikin ukkun banga wanda keda kushen hali ba, dukkansu musulinci ya halasta ki aure su, dan haka yanzu kawai ki nemi zaɓin ubangiji, ni yanzu zan tafi zan dawo cikin satin nan insha Allah, zanzo na ɗauke ki"
tana faɗar haka ta amshi wayarta dake hannun Asmar ta fita da sauri daga gidan tabar Asmah tsaya cike da abubuwan da za'a iya kiransu mamaki, rashin fahimta, rashin sanin abunyi, ina na dosa da kuma fargaba duk ita ɗaya.










A hankali ta zauna gun flowers ɗin wajen, take wata zuciyarta tace mata " Asmah shiyasa kike mutum dan za ki iya tunani mai faɗi" a hankali ta fara playing maganganun Aunty nafy a zuciya da ƙwaƙwalwarta, bayan ɗogon nazari, a fili take faɗin







"Na farko in na fahimceta tana nufin
kenan koma meye maganar da Ammien zata mun akan aure ne, sannan kuma maganar zaɓi kennan tsakanin YA ALIYU da YA MARWAN kenan, sai dai na kasa fahimtar inda tace _"duk cikin ukkun banga wanda keda kushen hali ba"_ kenan banda ya Aliyu da Ya Marwan akwai wani kenan, to waye? sannan na ƙara fahimtar wani abu kenan Aunty Nafy tasan abunda ya Marwan ya faɗa mun ƴan mintinan da suka wuce, kuma bata tilasta ni akan zaɓen ɗanta, sabodami?" dai dai nan wata zuciyar tace mata "sabidda tana sanki kuma ta ɗauke ki kamar ɗiyarta bata so ta tilasta maki akan abunda ba ra'ayinki bane, ki manta da bakinta tace zata rungumi maraicinki ta zame maki uwa a lokacin da kika rasa ɗaya" a fili ta ƙara faɗin "Ni Asmah nayi adalci kuwa in ban so ɗan wacce ta taimake ni alokacin dana rasa taimakon kowa, ta zame mun gata a lokacin da banda, ta zame mun rumfa ga rana da taso illatani" wata zuciyar tace mata "shiyasa tace tana bayanki a duk zaɓin da zakiyi kuma ki nemi zaɓin Allah dan shine mafi alkhairi"
Asmah ta cigaba da faɗin "to amman in haka ne mai yasa tun farko basu sanar dani wannan mahimmin bato ba? me yasa sukayi nauyin baki wajen faɗa mun? sun manta ni macece? Kuma ina fita ina mu'amulla da mutane kuma sun sani, bazan iya zargar zuciyata ba in ta faɗa tarkon son wanin Ya Marwan ba, domin ita zuciya bata da ƙashi zallar tsoka da jini ce, yanzu dai abunda nafi so in sani shine na ukkun, zanyi ƙoƙarin fidda wanda zuciya ta ke muradi domin in nemi zaɓin Allah" a cikin zuciyarta tace " yanzu in ba ya Aliyu bane zaɓin Allah a gareni ba, ya zanyi? Ina zansa soyyayar Aliyu? Me zai ce? Na yauɗare shi? Wayyo Allah na" ta faɗa maganarta ta ƙarshe tana ɗora hannu a ka kamar wadda aka turo ma saƙon mutuwa, a hankali ta furzar da iska daga bakinta yana fitar da sautin "whoashhh" sannan tace "Asmah sheɗan ne ya ke maki waswasi"a ranta a fili kuma tai saurin faɗin " *AUZU BILLAHI MINASHAIƊANIR RAJIM* Allah na tuba zaɓinka kawai nake nema"








ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now