page 41

4.7K 255 4
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨






💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼








🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )









*WANNAN PAGE ƊIN GABA ƊAYAN SA SAUDAUKAR WANE GA  ZAMAN AMANA WRITTER'S FORUM, GABA ƊAYAN KU, ALLAH YA ƘARA MA ƘUNGIYA ZAMAN LAFIYA DA AMANA DA ƊAUKAKA, YA KI YAYE KU DAGA SHARRIN MAHASADA, INA YINKU ƳAN UWA ONE LOVE,🥰😍❤💋ILYSVM DEARIES🥰❤❤💋💋*

*AUNTY AISHAN UMMA* .
*AUNTY* *RAHEENAT* _( *tawan* )_.
*🅱K (namesy).*
*SEE SEE.*
*LISSAH* .
*MUMMY'S FRIEND.*
*HAPSAY* .
*QUEEN RUKY.*
*AMISA'S GLAM.*
*MEELAT* .
*MAMAN SURAYYA.*
*MAMAR DEEJAH.*
*HAJ CEEYMAR.*
*MARYAM KWARE.*
*REAL KHADY.*
*UMMU AISHA.*
*SAMIRA HAROUNA*

*WANAN PAGE ƊIN NAKU NE KU KAƊAI KUYI YADDA KUKE SO DA SHI, INA KUMA ROƘAN ALLAH UBANGIJI YABA MA 🅱K LAFIYA YASA KAFFARA CE, TAKWARA GWS PLS.*



*INA KUMA SO IN GODE MA DUKKAN WAENDA SUKAYI MUN BIRTHDAY WISHES, A GASKIYA NAJI DAƊI SOSAI GANIN SAƘONNIN KU DA ADDU'OINKU A GARENI, NA GODE NA GODE ALLAH YABAR ƘAUNA, ALLAH YA BIYA MAKU BUƘATUNKU DUNIYA WAL AKHIRA, ءان اءحبك💋😍.*




Page4⃣1⃣




*KI RIƘE ƘAUNAR ANNABI MUHAMMAD (SAW) SAFIYA DA MARAICE TABBAS YAWAITA SALATI GA ANNABI YANA SAMAR DA LADA MAI YAWA DA ƘARA IMANI, KI SANI YAKE ƳAR UWA WALLAHI BAKI DA KAMAR ANNABI MUHAMMAD (SAW).*
                          QUEENBK.






Ammie ta kamo Asmah ta rungumeta wani sanyi taji kamar ta rungume ƴar cikinta, a hankali take faɗin,

"Asmah na gode na gode ɗiyata".

"Ammie me yasa kike gode mun, banyi abunda ya cancanci godiya ba saboda nima ina son ya Abdallah" ta faɗa tare da sunne kanta cikin kunya.

Ammie ta ɗago da ita tana faɗin "ki dai najin kunya ta ni kamar mahaifiya nake a gareki, kuma ke kika cancancin godiya domin ke kika so Abdallah a lokacin da ba kowa bane zai iya sonsa, dan haka kin gama mun komai Asma'u".

"Dan Allah Ammie ki daina faɗar haka, ni wallahi ina son ya Abdallah ne tsakani na da Allah kuma zan kula dashi har karshe rayuwata matuƙar ni Asmah ina shaƙar lumfashi a doran ƙasa bazan karya alƙawarin nan dana ɗauka ba, kuma ni hasali ma bana ganin wata makusa ta ya Abdallah a haka nake son shi, kuma a haka zan cigaba da sanshi".


Idon Ammie ya cika da hawaye, har bata san sadda suka sulalo ba sai dai taji hannun Asmah na share mata tana faɗin "Ammie dan Allah ki daina kuka kar ki sani nima nayi kukan".


Ammie ta jawo ta ta ƙara rungume ta tace "haƙiƙa ba kowa bane zai iya abunda kika aikata Asmah, ko a cikin ƴan uwanka sai ɗai ɗai, inaji a jiki na kamar akwai alaƙar jini a tsakanin mu, Allah ma sanin gaibu".

"Na gode da karamcinku Ammie, ba kowa bane zai iya abunda kuka aikata ma rayuwa ta, kune kuka haskaka rayuwata kuka bani ilimi boko da arabi, kai gaskiya bazan iya ɗirga mutunci da karamcinku a gare ni ba, inaga ni yakamata ace ni na gode maku, sannan in saka maku da duk abunda bai fi ƙarfi na ba, duk da nasan ban iya taɓa saka maku dukan karamcinku sai dai fatan ubangiji Allah ya saka maku da mafificin alkhairinsa".





ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now