Ai me neman kuka ne aka jefe shi da kashin shanu ai tuni kuwa ta fashe da kukan dan dama yana maƙoshinta da sauri Naty ta jawota jikinta tana faɗin "subuhanallahi Asma'u ya akai" tuni Asmah ta ƙara shigewa jikinta tana ƙara sakin sabon kukan da ya daɗe da tarar mata a ciki sai yau ta iya fidda shi dan duk sadda ma take son tayi shi baya futa sai yau, Abdallah kam da tunda Asmah ta fara kuka ya nemi natsuwarshi ya rasa dan ko da wasa Abdallah baya san kukan Asmah ko kaɗan sai yaji zuciyarshi na mashi ɗaci ɗaci ya rasa inda ke mashi ciwo a jikinsa dan gaba ɗaya jikinsa yake masa ciwo in yanajin sautin kukanta wannan kuma ba tun yau ba, ya samo asali ne tun tana ƴar jinjirarta, yanzu ma jiyai zuciyarshi sai mitsintsinarshi takeyi bai san sadda ya isa gabansu ba idanu rau rau shima kamar zaiyi kukan yace,


"Natynmu dan Allah ki faɗa mun me ya samu beautyna take kuka" yadda yai maganar ma saida ya ba Naty tausayi itako Asmah ɗan ɗago kai tayi ta kalleshi dan tasha duk cikin miskilancin nasa ne take ta ƙara fashewa da kuka tana maida kanta bisa cinyar Naty tare da faɗin "ya Abdallah wai yaushe ne zaka daina playing ɗina ne baka san ina cutuwa ba?" cikin ranta tana cigaba da kukan nata.


Naty kam da zuwa yanzu lamarin nasu ya gama ruɗa mata lissafi dan tama rasa wanda zata rarrasa dan duk sunƙi jin lallashin nata cewa tai "yau naga lafiyar Allah Mai gari gauro talaka da mata huɗu".






Dai dai nan Ummah ta shigo da jin ba'asin kukan Asmah da take jiyowa tun tana toilet, ita ma sororo tai ganin Asmah sharɓe bisa kan cinyar Naty tana ta kukanta bil haƙƙi shi kuma Abdallah na gefenta yana ta bata baki shima yana matsar ƙwalla, Ummah ta kai dubanta ga Naty da ta rasa abunyi inba jijjiga Asmah ba abunda take dan bakin ya toshe, Ummah tai mata kallon me ke faruwa?" sai da ta taɓe baki kana tace,




"Yoni me zance zanin aro ya toye, daga tambayarta dalilin rashin farin cikinta a yau ɗin ta sakar mun makoki".





Ummah ta kira sunanta
cikin rashin wasa ta ƙara faɗin "Asma'u tashi nace", a hankali Asmah ta ɗago jajayen idanuwanta da sukai luhu luhu suka ɗan kumbura kaɗan tsabagen kukan da ta risga, Ummah ta cigaba "me akai maki ne dan Allah kike tada mana hankali" ta faɗa a sanyaye domin ganin fuskar Asmah duk sai taji tausayinta ya baibayeta.




A hankali Asmah ta ɗaga ido ta kalli Umman nata da niyar magana sai kuma ta kasa dan ita kanta bata san dalilin kukan nata ba, Naty ce cikin ƙarfin gwiwa ta riƙo hanayenta cikin kwantar da murya tace "haba ƴar jikalleta me ya same ki ne ki faɗa mana ko ma meye dan baki da kamar mu kinji" ta faɗa tana shafa hannunta a hankali kan ta cigaba "ko baki son zuwa katsinarne a fasa sai wata rana?" da sauri Asmah ta kaɗa kai, "to ko kin gaji damu ne kano kike son komawa?" wannan karen ma da sauri ta kaɗe kai har tana cewa "ai bazan taɓa gajiya daku ba Naty ban ƙima mu dauwama anan ba" jin tayi magana da sauri Ummah tace "to meye damuwarki da har tasa ki kuka?".





Turo baki tayi tana kallon Abdallah tare da kawar da kanta gefe, tuni Naty tace "ai dama nasan akwai wata jiƙaƙƙiya a tsakaninku tuni na daɗe da lura ban dai yi magana bane kawai gudun kada zato na ya zamana ba haka bane".





Itama Ummah ta fuskanci komai tabbas akwai wata ƙullalliya a tsakanin nasu da daɗewa to a zatonta komai ya dawo dai dai ne shiyasa bata ƙara bi takan al'amarin ba, don ta fuskanci dukkansu suna ɓoye abunda ke tsakanin nasu wanda yai sanadin faɗan nasu domin sau barkatai tasha cikin hikima ta tare su da zancen amman kowa baya faɗin laifin ɗan uwan nasa sai ma kareshi da zai riƙa yi ta rasa gane kansu.



Abdallah ne ya katse
shirun da faɗin "tashi muje Beautyna ki faɗa mun me ya same ki" ya faɗa yana kama hannun Asmah bayan ya tashi ne ya jata zuwa ɗakin Naty wanda Asmah tai masauki, da kallo kawai suka bisu ita kuma Naty ta ɗauko goronta tana gogawa sai data sa niƙaƙƙen a bakinta kana tace "to i maza dai ku shirya kanku kan mu ganku a rana, abu da sirri ba wanda yaji balle ya gani" sai lokacin Ummah ta ƙaraso gaban Naty tana zama tare da amsan abun goga goron tana cigaba da goga ma Naty cike da son ƴaƴan nata tare da ƙara gode ma Allah son da sukewa junan nasu.





ZAN SOKA A HAKAWo Geschichten leben. Entdecke jetzt