A haka har suka gama zangon karatun da suka shiga ana hutu kuwa Abdallah ya tubure kan dole akaishi gidan Habibty yaga Beautynshi haka kuwa akayi to shine fa yake gidan yanzu haka.




Ƙara waving mata paper yayi yana ƙara faɗin "habibty ko motar batai kyau bane na kuma zana ma beauty wata?".



Da sauri ta futo daga tunanin da take na yadda Allah ya haɗe jinin Asmah dana Abdallah ta sake murmushi tana karɓar paper tace "kai Habibi tayi kyau sosai lallai kanaji da beautyn nan taka" zuba masa best food ɗinshi tayi ta tura mashi gabansa tare da faɗin "i maza kaci kaji Habibi kar yunwa ta kama mun kai".



Cokali yasa ya ciko fried rice ɗin zai kai baki kenan yaji baby Asmah dake can saman gado tana shaƙar baccinta ta tsala ihu alamun ta tashi dan ita komai da kuka ake yinsa dama shi ya lallaɓata tai baccin, da sauri ya aje spoon ɗin yana faɗin "kai subuhallahi beauty ta tashi" kan Haleemah ta takai tuni ya isa kusa da Asmah yana ta jijjigata haɗe da mata wasa da waƙoƙin kamar yadda ya saba, sai da Haleemah ta ɗauketa ta samata nono a baki kana tai shiru sai lokacin hankalin Abdallah ya kwanta ganin tayi shiru nan ya kama hannunta yana ta shafawa a hankali da ƙyar Haleemah tasa shi komawa ya cigaba da cin abincinsa sai da ya sumbaci hannun sannan ya saketa ya koma kan plate ɗinsa duk da rabin hankalinshi na kan beauty a haka sukaci gaba da rayuwa har hutu ya ƙare nan ma aka shiga daga da Abdallah sai da Muhammad (mijin haleema baban Asmah) ya kamosa yana ta turturjewa akan bazai tafi yabar beauty ba cikin lallashi ya dube shi yace "Kayi haƙuri kaji Abdallah kar ka damu inka girma zan aura maka beauty sai kai ta tafiya da ita duk inda kakeso kaji amman dai ka yarda ka koma kaga zaku koma skull ne kaji" da sauri Abdallah ya rungumeshi jin yace za'a ɗaura masa beauty duk da baisan ma meye aurenba a taƙaice cewa yayi "na gode Abban beauty kenan zaka bani beauty kyauta ko in tafi da ita har na sata a babbar motar dazan siyo mata mu tafi makkah ko?".


"Ay Abdallah" ya faɗa yana shafa masa kai, da sauri Abdallah ya ruga ya rungume halimatu haɗe da Asmah dake hannunta yace "kinji ko Habibty Abban beauty yace zai bani beauty kyauta ai kema kin yarda ko" gyaɗa masa kai tayi tana farin ciki, bakinsa ya kai kan kumatun beauty ya sumbanta a haka dai ya yarda aka maida shi gida kullum ko cikin labarin wai in ya girma za'a aura mashi beauty yake ahaka rayuwa ta cigaba da tafiya duk hutu kuwa Abdallah na gidansu beauty, a haka har beauty ta fara girma koda ta fara magana kuwa da sunansa ta fara buɗa baki zuwa yanzu ko da ta fara wayau ita ma ta saba dashi sosai dan ko kuka take yana ɗaukar ta to zata haɗiye kukan tas kuwa in kuma an koma makaranta yana gida amman kullum Abdallah na maƙale da beautynshi a waya lokacin ko ya abulla kawai ta iya cewa sai dai yai ta mata zuba ita dai tana maimaita sunanshi tana dariya cikin farin ciki, tun tana gwaranci har ta fara magana to ana haka ne tsautsayin da faru dasu ya afku lokacin da labarin ya isa kunnen Abdallah yace ina sam shi bai yadda ba maganar da ya sani kawai a fiddo masa beautynshi, haka yaita masu bori da su Ammie suka kasa dashi dole suka kawo shi nan gidan Naty da yaga dagaske dagaske baya ganin beautynshi haka ya shiga tashin hankali yatai ciwuwwuka haka in ya shiga ɗaki ya taras Haleemah na kuka haka zai shiga taya ta haka zasuyi tayin kukan tare har suyi bacci wata sa'in kuma Haleemah ke ƙarfin zuciya tana lallashinsa Naty ko tuni ta tattara lamatin ta miƙa wa Allah dan ta gaza gane kan daga uwar har ɗan ita dai addu'a kawai take masu, a haka har Abdallah ya koma gida sai dai duk ya sauya gaɓa ɗaya duk da bai cika kwaramniya ba amman shiru shirun nasa da shiga tunane tunane yaro dashi ba ƙaramin sosa ran mahaifan nasa yake ba, shine mafarin da yasa aka haɗa Abdallah da Khaleel aka kaisu can wajen ƙanwar Alhaji Muhammad Zayyan dake can london domin suyi makarantar secoundary ɗinsu a can, a lokacin Abdallah bazai wuce shekara sha ɗaya ba yasa a hankali hankali tun yana tunawa jefi jefi har ya rinƙa manta abubuwan duk da abun bai bar zuciyarshi ba har yana tunawa kuwa har faruwar hatsarinshi ne ma ya manta komai.

*Flash back over.....*





A hankali Asmah ta shiga kaɗa kai tana jinjina lamarin a ranta take faɗin "ba banza ba yasa nake mafarken al'ajabi da ya Abdallah kamar yadda shima yakeyi ashe mun shaƙu tun muna ƙanana Allahulazeem Allah mai yadda yaso a lokacin da yaso, yanzu gashi maganr Abbanta ya cika".



ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now