"To".

Har bakin mota Aunty Nafy ta rako su tana ɗaga ma Asmah hannu sai da ta ga ɓillewar motarsu tai saurin shiga gida ganin yadda ƙasa ke shiga idanunta ga yadda iske ke kwaso yaye yaye.

Suna isowa gida part ɗin Ammie tayi direct sai dai yadda ta ga Ammie duk taji tsoro zuciyarta ta fara faɗin to meke faruwa? me ke faruwa dani? me yake shirin samuna? ta kauda tunanin da insha Allah ko ma meye alkhairi ne.

Ta ƙarasa ciki da sallama, Ammie ta amsa tana koƙarin kauda damuwar dake fuskarta, murmushi tayi tace "Asma'u kin dawo ko? sai ki kaga an ɗauko ki tun yanzu ko?".

Asmah ma tayi dariya cikin ƙoƙarin ɓoye tsoron da ke fuskarta cewa tayi "ba komai Ammie ai mun gaggaisa ga kuma hadari ya taso ai gwanda da na dawo ma".

"Yauwa ƴal albarka shigo ki zauna dama ina so na tattauna wani muhinmin abu dake", ta faɗa tana kamo hanun Asmah suka zauna suna facing juna.

Asmah ta yaye gyalenta da jakka ta aje gefe guda tana maida dubanta ga Ammie dan ji meye mahinmin abun.


Ammie tayi gyaran murya tace "dama tunani nayi naga ban sanki ba sosai ina nufin ban san rayuwarki ta da ba shiyasa naji ina kwaɗayin insa ya rayuwarki tada kike ina ne ƙauyenku ma? ina iyayenki suke kuma? in ke marainiya ce to taya akai suka mutu? ciwo sukai? ko ɓata sukai? ina dai san na san duk abunda kika sani game dake da fatan zaki faɗa mun komai?".

Asmah ko da taji tambayar bazata duk sai taji gabanta na faɗi tunaninta ɗaya to me ya faru, wata zuciyar tace mata to me ya faru kuwa dan kawai tana san ta san labarinki, to amma mai yasa abun ya zo kwatsam dole akwai wata a ƙasa, ita dama ta daɗe tana mamakin yadda akai su Ammie basu tambayeta ba, cikin ƙoƙarin kauda tunaninta tayi murmushi tace "Ammie ai bazan taɓa ɓoye maki komai ba insha Allah zan gaya maki duk abunda na sani game dani kamar yadda kika buƙata yanzu kuma".

"To ina ji ƴa ta".

Nan Asmah ta feɗe mata biri tun daga kai har wutsiya na game da labarinta tas ba abun da ta ɓoye mata, sai dai tun da ta fara bata labarin hatsarin da ya faru da ita da iyayenta taga hawayen Ammie sun ƙaru sai data gama tas sannan tayi shiru ita ma tana share hawayen tuna rayuwarta ta da.

Gani tayi Ammie ta faɗi a wajen tayi sujjada sannan ta ɗago ta koma inda take zaune hawaye na ƙara bin kuncinta ta kasa magana mamaki da dana sani take, tana mamakin yadda akai Asmah ta zama ɗiyar Nana da suke ta nema shekaru da yawa da suka wuce da kuma yadda akai duk tsawon zamanta a gidan nan basu gane ba sannan tana dana sanin rashin tambayar Asmah tarihinta da bata yi ba tun farko, nan ta cigaba da kuka itako Asmah ganin kukan na Ammie yayi yawa har ya wuce misali ya sata share mata hawaye tana faɗin,

"Ya haƙuri Ammie dan Allah ki daina kuka komai ai ya riga ya wuce ya zama labari da tarihi dan Allah ki bar kuka".

Ji tai Ammie ta jawo ta ta rungume ta tana faɗin "dama naji a jikina ke jini na ce, ashe na kusa ma ke ƴa ta ce Asmah, no wonder nake ganin halayenki ɗaya da jinin mu Asmah, ni yayar mahaifiyarki ce kuma kamar uwa a gareki". da sauri Asmah ta ɗago cikin mamaki da rashin fahimtar abunda Ammie ke faɗa mata tace,

"Ummata? kin santa ne? dan Allah taya kika san Ummata? ya kuke da ita? tana ina yanzu? tana raye? ko ta mutu kamar Abbah na? Ammie dan Allah kice kisan Ummata dagaske ne ba mafarki nake ba yau na haɗu da wanda yasan Ummata, amman Ammie ya akai kika san ummata?" a kiɗime take jero ma Ammie tambayoyin tana rirriƙe mata hannu tana sakin kuka.

Hannu Ammie tasa tana share mata hawaye tana faɗin "Ay tabbas ba mafarki kike ba na san Ummanki, farin sani ma kuwa".

"Ammie dan Allah a ina kika san Ummata, bayan ban taɓa gaya maki ita ba sai yau?".

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now